taura biyu 25

8.1K 683 39
                                    

*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._
 

_Viawattpad@mamuhgee_

                 *25*

Tun ranar Ba'a Kuma barinsu fitaba har tsawon kwana hudu duk inda hankalinta yake yayi mugun tashi musamman yanda taga shirye shiryen biki Sai da'da kankama suke Dan yanxu sati 'daya ne yarage kullum tana quryar 'daki a takure batada aiki Sai kuka ga wani mugun zazza6i da kullum dashi take kwana..

Duk hanyarda tabi danta samu ta fita batayi aikiba  ga Yaya Umar da yanxu wata soyayya yakeji saima hakan yakuma sakata cikin babban tashin hankali..

A 6angaren Deen ma kusan haukacewa su mum yayi ya 'daga musu hankali yaqi ci yaqi Sha ga ciwon damuwa da yunwa daya bayyana qarara a tattare dashi Nan hankalin mum yayi mummunan tashi takasa zaune takasa tsaye Amma yaqi fa'da Mata damuwarsa.

Yau Kam daqyar yaga safiya yanayin sallar asuba ko wanka baiyiba ya zari mukullin mota ya fice.

Direct anguwarsu ayshah ya nufa yanayin parking ya fito ya doshi gidansu Kai tsaye ba tsoro ba fargaba.

Kasancewar da safe ne Babu kowa a qofar gidan dai Sai qarfe goma ake fara karatu.

Qofar gidan a bu'de take Kuma Yana jiyo sautin karatun alqur'ani da wani yakeyi a 'dakin dake kusa daga ciki.

Sallama yayi ahankali ba'ajiba ya 'dan 'daga murya yakumayi Yana cusa Kai cikin babban soron gidan.

Ya Ahmad dake 'dakinsa Yana karatun Qur'an ya aje ahankali tareda tasowa yafito Dan ganin wake sallama da sassafe haka.

Murza idonsa yayi yakuma kallon Wanda ke tsaye cikin doguwar farar jallabiya ya matso a zafafe zai cakumosa Deen ya riqe hannunsa tareda 'dago lazy eyes 'dinsa dasukai ja Kai tsaye yace,

I'm not here for this...I came to see my ayeeshah.

Uwarka zaka gani ba ayshah ba'''''sukaji anfa'da daga bayan Ahmad...

Umar ne tareda sani da baba alhaji..

Fixge hannun Ahmad baba alhaji yayi daga hannun Deen bai tsaya komaiba ya wankeshi da lafiyayyan Mari.

Rintse ido yayi da qarfi sbd Marin yashigesa Amma bayajin yau zai ja baya.

Nunasa da yatsa baba alhaji yayi cikin 6acin Rai yace,

Wannan Marin qoqarin 6ata Mana suna dakayine ta hanyar sace  Mana 'ya dan sunanmu ya 6aci.,,Kuma inason maza tun kafin mutane su taru kabar Mana gida.

'dagowa yayi da fuskarsa datayi ja sbd Marin ya kalli baban yace,

Ayshah is my wife and....

Naushi Umar yakai Masa a baki kafin ya cakumo wuyansa cikin zafin Rai Yana huci yace,

Idan kakuma fa'dar ko sunanta a wannan qazantaccen bakin naka saina fasa makashi da kwalba.

Sakinsa yayi tareda turasa baya da qarfi yana nuna Masa qofa da Ido yace,

Maza bar Nan tun kafin hakurina ya qare.

Gyara tsayuwa sukaga yayi yakuma kallon baba alhaji danko kallon Umar bayasonyi danji yake zuciyarsa zata iya bugawa idan Yana kallonsa...yace,

Baba please let me see her we have something to tell you all....

Ta baya Umar ya fixgosa jiyayi zuciyarsa ta 'dau zafi a hasale ya juyo ba zato ya saukewa Umar gigitaccen marinda Saida hancinsa bakinsa ya fashe..

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now