taura biyu 7&8

8K 684 8
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
       _Mi amor-mi vida_....

_viawattpad@mamuhgee_

           *7&8*

Harta Isa iga ruwa ake sosai shiya Hana aga 6arkewar hijabinta da jajayen idanuwanta.

Shigewa 'daki tayi ta dunqule da jiqaqun kayan tasaki wani sabon kukan.

Wasa wasa saigata da zazza6i ciwo kwance rigis sbd kukan datake yawan yi batareda anluraba.
Jinya tayi tsawon kwanaki kotaji alamar sauqi saita lafe sbd Sam batako qaunar taji ankira sunan makaranta bare hartayi sha'awar zuwa
Babu abinda tafi buqata yanxu kamar ace antsaida ranar aurenta da ya Umar anyi ta huta.



*********
Kwance yake cikin lallausan bargon gadonsa idanuwansa a lumshe Yana sauraron Murphy dake Masa fa'da akan abinda ya yarda su Josh suyiwa ninja lady.

Sautin kukan tane yadawo Masa ya cikin kunnuwa ya lumshe idanu tareda qara shigewa cikin bargo.

Kwana biyu mum 'dinsa tarasa gane kansa sbd son jikinsa ya da'du dan kullum daga makaranta Sai gida yazo ya kwanta ya lumshe idanu.

Kwana 'daya kwana biyu har sati batazo makaranta son ganinta yake sbd kullum Murphy bayada zance Sai nata shiyasa yanxu yakeson yaganta yayi Mata kallon mintuna sbd kawai ya cire tsoronsa akanta.

Yau kwana goma rabonta  da makaranta dole tashirya zuwa sbd yawan tambayarta da ya Umar keyi akan rashin son zuwanta makaranta yanxu.

Tsaf tashirya cikin dogon hijab 'dinta maroon da niqaf dinta harma da safarta ta hannu da qafa kamar kullum.

Tunda tafito gida take addua harta Isa makarantar.

Sosai takuma Kama kanta sbd fahimta datayi komai zai iya faruwa matuqar batayiwa kanta babbar katanga da duk wata hanyarda Nik yabi ba.

Cikin ikon Allah hankalinta ya 'dan kwanta sbd kusan sati biyu kenan Basu ha'duba acikin makarantar Nan tasawa ranta Allah ne ya kar6i adduarta yayi Mata tsari dashi.

Sun fara exam shiyasa Bata cika Zama cikin mutane ba saidai taje can baya inda Babu mutane ta zauna tayi karatu kokuma ta zauna tana nazarin rayuwarta a makarantar.

Yau zaune take baya gurin wasu ciyayi dasuka kwanta luf iskar ni'ima na  ka'dowa ahankali tana ratsata.

Ba karatu takeba kawai zaune take tareda lumshe idanu tayi zurfi cikin tunanin rigimar dasukayi jiya da ya Umar akan shima nijar yakeson komawa bayan aurensu itakuma Sam bazata iya rabuwa da iyaye da sauran 'yan uwantab dukda Sam Bata iya ko 'dagowa tayi Masa dogon kallo bare harta iya musa masa saidai tashige 'daki tayita hawayenta.

Zaune yake shima agurin ammashi Saida aka kafa Masa 'yar rumfa sbd iskar tayi Masa  yawa sbd Sam ko ka'dan  jikinsa bayason sanyi sosai Dan Nan take ne zai fara mura ko zazza6i.

Tare sukeda Murphy Amma yaje ya dubo Davina data kirasu yanxu wai gatanan tareda police cikin school 'din sbd glass 'din motarta da'aka fasa aka 'dauke Mata purse da laptop aciki.

Shika'dai ya rage zaune agurin fuskarsa sanye da black goggles daya qara  fiddo haske,kyau,hutu tareda wayewarsa a fili.

Wayarsa yake ta6abawa kamar daga sama yaji Abu na tafiya a kafa'darsa ya zabura da sauri ya Duba...

Zaro idanuwa yayi cikin wani masifaffen tsoro da tashin hankali yayi wurgi da wayoyinsa duka tareda qwalla qara Yana cewa,

Mu..mu..mummmm scorpion,, scorpion,,help help help me,,mummmm

Dummm gabanta yabuga ta bu'de idanuwanta da sauri tareda miqewa sbd itama ba laifi akwaita da shegen tsoro...

Juyowa tayi da sauri zata bar gurin Ashe inda yake ta nufa saigata gabansa turus.

Tsayawa tayi tareda juyawa da sauri cikin tsoro sbd ganin kyakkyawar farar halittar qirjinsa a bayyane Dan tuni ya cire rigarsa yayi wurgi Sai ihu yake Yana qoqarin zare wan.....

Cikinta yayi tareda cukuikuyeta Yana ihu bakin Rai Yana Kiran scorpion..

Tsoro da tashin hankali yasa tafara qoqarin qwacewa Amma ba qaramar cukuikuyewa yayi mataba ba zato Sai gasu a qasa gaba 'daya Kuma har lokacin ihu yake sosai Dan duk ya yage kyakkyawar farar fatarsa sbd tsoro gashi yaqi sakinta.

Turesa tahauyi tana kuka ahankali Dan ita tsoron biyu ya kasar Mata gana scorpion 'din dayake Kira ga nasa.

Idonta ne ya sauka kan wuyansa taga gizo gizo irin Mai kaurin Nan Yana tafiya saman fatarsa...

Hannunta ta 'daga ahankali takai kan wuyansa ta 'dauko gizogizon tareda kai hannunta saitin fuskarsa ahankali cikin sanyin murya  tace,

Look it is not a scorpion,,it's a spider...

Cikin wani irin yanayi ya 'dago sbd mummunan dukan da muryarta tayiwa zuciyarsa da gangar jikinsa taredayin rugu rugu da tsoron dayakeji Nan take.

Fuskarta ya kalla har lokacin a rufe take ya maida kallonsa kan tafin  hannunta data ware tana nuna Masa spidern dake cikin hannun nata.,,

Kyakkyawar farar fatar hannunta fara tas ya qurawa ido gabansa nacigaba da fa'duwa sbd wannan shine karo na farko data cire Safar hannunta acikin makarantar,, Zara zaran fararen yatsun hannun nata dasukaji Jan lalle Mai matuqar tsari ya qurawa ido zuciyoyinsu na bugawa kusan atare....

Ahankali yafara 'daga hannunsa yakai fuskarta zai yaye niqaf dinta batareda ta hanasaba ta rintse ido hawaye suka gangaro tana jiran taji ya yaye niqaf 'din......

Wat da heck Nik''''''sukaji Davina tafa'da da qarfi sbd yanayin dasuka samesu Shiba Riga ajikinsa hakama kwance a qasa Yana maqale da ita.

A zabure ta turesa tareda miqewa tsaye shima miqewa yayi jiki a sake Yana kallon wainda ke tsaye akansu.,,

Davina, Murphy tareda police 'din case 'din motar Davina da wasu friends 'dinsu kusan su shida.

Dukkaninsu kallon Nik 'din suke cikeda mamaki da tuhuma musamman ma Murphy da tuni yaji zuciyarsa tafara quna.

Juyawa tayi jiki a mace kamar munafuka zatabar gurin cikin takaici Davina Tasha gabanta tareda kallonta a wulaqance tace,

Arrest her officers for trying to take advantage of my brother's inno.....

Stop Davina'''''' murphy yafada cikin Jin zafin abinda take fa'da.

Ayshah kuwa cikin tashin hankali takalli Davina da police din Jin tozarci da qazafin daza'ai Mata Dan kawai a lalata Mata suna.

Ido cike taf da hawaye ta juyo gefen Nik takallesa
Ya juyar da Kai tareda juyawa yabasu baya Dan har lokacin bai gama dawowa nutsuwarsaba ta yanayin dasuka kasance tareda ita.

Lumshe idanu tayi wasu zafafan hawaye suka gangaro Mata ganin yanda yajuya baya maimakon ya fa'di gskiar abinda yafaru.

Cikin tsawa Davina takalli officers 'din tace,

I said take her away.

Hannu police 'daya yakai zai kamo hijabinta yaja yaji anriqe hannunsa.

Dukkaninsu kallon mamaki sukabi Nik dashi ganin shine yariqe hannun police din ransa amatuqar 6ace.




Mamuh💋



_dont forget to follow, vote and comments_

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now