taura biyu 26

8.1K 664 41
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._
 

_Viawattpad@mamuhgee_

                 *26*

Babban alamarin tashin hankalin ba qaramin Dakar zuciyarsu malam babba yayi ba Dan iya ,'daukar zafi sun 'dauka da ayshah shiyasa malam ya 'dau babban mataki cikin 6acin Rai na hanata fitowa Koda tsakar gidan bare harta fita.

Tayi kuka har qarfin jikinta ya qare saidai na zuci,
Fuskarta kuwa ta ko'de tayi wani haske kamar Mara jini.

Nuratu ce kawai mai tausayinta tana qoqarin tausauta Dan ganin ta rage damuwa Amma Sam kullum alamari qara gaba yake Dan ba abinda ke 'daga Mata hankali kamar yanayinda aka fitardashi batada tabbacin Yana Raye....

Hakan take tunanowa taji kamar zata haukace wani sa'in Sai nuratu ta ririqeta...

Kamar lokuta da dama yauma kwance take ta takure qarshen qatuwar katifarsu zazza6i takeji sosai Amma batajin ko motsawa zata iya yi sbd raunin dake zuciyarta yayi nasarar karya dukkanin garkuwar jikinta.

Qarasowa nuratu tayi ta zauna gabanta tareda kallon yanda hawaye suka bushe Mata a fuska ta dafa qafafuwanta cikin sanyin murya tace,

Anty ki misalta min inda yake zance nadubo mikishi Dan hankalinki ya 'dan kwanta..

Da sauri ta 'dago idanuwanta dasuka koma qanana sbd kuka ta kalli nuratu batasan sanda ta rungumetaba cikin farin ciki.

Gidan anty zainab tayi qaryar zuwa aka barta tana fita daga gidan saita fara zuwa gidan anty zainab 'din Sai yamma sosai ta fito ta nufi asibitin da ayshah ta misalta Mata
Bata Sha wata wahalar gano room 'din dayakeba tana shiga Nan ta tarar da wani tashin hankali.

Zaune yake kan daddumar sallah kansa a qasa kuka yake kashir6an kamar ransa zai fita..

A darare ta qaraso gabansa takira sunansa cikin hawaye Dan baqaramin karyewa zuciyarta tayiba da ganin shima halinda yake ciki.

'dagowa yayi Yana ganinta yasan nuratu ce qanwar ayshansa datake fa'da Masa ya kalleta cikin dashashiyar murya yace,

Ayeeshahna tana...

Katsesa tayi cikin hawaye da fa'din,

Ita tasani nazo Naga halinda kake ciki...

Rintse idanu yayi cikin Jin sabuwar soyayyar ayshansa ya bu'dese ya sauke akan nuratu tareda zubewa gabanta tayi saurin ja da baya jikinta rawa cikin kuka tace,

Me kakeyi haka??

Murya a shaqe yace,

Please take me to her,,,,I want to see her before I die coz I can feel my life is about to end...
I want to see and tell her how much she means to my miserable life because I'm the couse of all her pains...
Please please ple.....kuka yaso kwace Masa batasan sanda tayi saurin durqusawaba itama tace zata kaisa.

Ana Kiran magriba suka Isa anguwar..
Dayake duhu ya'dan fara Babu Wanda ya lura dasu suna,
Saidata leqa taga gabaki 'daya mazan gidansu sun shige masallaci matan kuwa duk sunshiga 'dakuna sallah tayi saurin kiransa yashigo takaisa 'dakin da aka maida ayshan aka hanata fitowa.
Yana shiga tasaki ajiyar zuciya tareda barin gurin.

Duhu ne a 'dakin Amma Yana iya ganinta zaune kan sallaya ta cusa kanta cikin qafafuwanta tayi Nisa acikin tunani.

Jikinsa ne yayi matuqar saki ya qaraso ahankali ya zauna gabanta tareda Kiran sunanta can qasan maqoshi.

Kamar a mafarki taji muryarsa tana 'dagowa sukai Ido biyu da qarfi ta fa'da jikinsa tareda fashewa da kuka tana qanqamesa.

Shima hawayen yake Yana qara shigarda ita jikinsa.

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now