taura biyu 37 last chapter.

15.3K 1.1K 126
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
_Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

*37*

Zaune take tana cika tana batsewa Dan yau jitake Sai anyita ta qare Dan wlh tagaji da wulaqancin Deen saidai ko ita ko ayshah wani yabar gidan sbd bazata yarda karuwa tafita matsayi acikin gidantaba.

Da sallama yashigo fuskarsa ba yabo ba fallasa.

Ko sallamarsa Bata amsaba ta taso tazo gabansa ta tsaya cikin zafin Rai tace,

Yau inason sanin matsayina a gidan Nan.

Kallonta yayi cikin baqin cikin Yama ya iya zaman aure da wannan for almost two years Kai wlh na cutu nida ayshana da yawa.

Cikin masifa tace,

Fadamin meye matsayina acikin gidan Nan Dan kuwa yau inason sanin nida tsintacciyar matarka waye Mai....

'daga Mata hannu yayi da sauri sbd ransa daya fara 6aci yaciro envelope daga aljihunsa ya miqa Mata.

A wulaqance ta kar6a kafin ta bu'de yabar gurin.

Cheque na kudi tagani kafin taga muguwar takarda daga baya ma'ana takardar sallama.

Hannu ta 'dora akai zata zunduma ihu saita fasa tana cewa,

Wlh ma bazanyi ihunba saidai Kuma wlh bazan yardaba.

A zuciye ta banko qofar palon mum tashigo ba zato tasakarwa ayshah wani mummunan mari kafin ta sauke hannunta mum tasakar Mata tana juyowa Deen ya 'daga hannu ayshan ta riqe hannunsa tasakar Mata Wanda yafi na mum qara ranta a6ace.

Riqo ayshan yayi da sauri Yana shafo fuskarta kaman zaiyi kuka ya juyo Rai a6ace yace,

Get out.

Kururuwa ta saki tana cewa,

Wlh bazan tafi koina ban kar6i wannan sakinba indai akan wannan tsintacciyar karuw...

Marin dai dabata samu a farkoba saidata shasa a gigice ta 'dago Dan Marin ba qaramin shigarta yayiba ya kalleta Rai amatuqar 6ace yace,

Foolish woman,idan baki yarda da sakin akan ayshah ba kije ki yarda da sakin akan abinda kikayi yazama sanadin rushewar lafiyar khadija.

Wat""""mum tafada da qarfi tana kallon Deen 'din ya 'dauke Kai Dan baiso fidda maganarba Amma ita taja.

Azuciye mum takalleta zuciyarta na 'daukar zafi ayshah tayi saurin dafa mum 'din tana cewa,

Don't weste your energy mum let hand her to police let them deal with this crazy mentality.

Kai tsaye yace,
She's not going to any police let her go zata ga daidai abinda tayi Nan gaba.

Kuka tafashe dashi tareda zubewa qasa cikin nadama tana basa hakuri ya fice riqeda hannun ayshah Yana kallon face 'dinta inda siyamar ta mareta.

Part dinsa suka shiga ya zaunar da ita kan kujera tareda durqusawa gabanta yakai hannu ya shafo fuskarta kaman zaiyi kuka.

Riqe hannunsa tayi tana kallon face 'dinsa hawaye naciko idanuwanta tace,

Deen idan har saboda ni ka saki siyama then please ka maida ita nizan koma gombe ita ta zauna anan...

Shihhhhhh''''yace Mata Yana 'dora yatsansa kan lips 'dinta ahankali yace,

Ayshah kece rayuwata farin cikina,,
Ayshah matuqar kina taredani bazan ta6a yiwa ko wace mace adalciba bare siyama da Bata ganin girmana Dan mum 'dina,
Banason ranar lahira natashi da shanyayen Rabin jiki sbd rashin kwatanta adalcina.

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now