taura biyu 28

9.8K 673 76
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._
 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *28*

_*A zahirin gskia banajin da'din yanda wasu da dama suka dameni da zancen wani bai kamataba ace ayshah tayi karuwanci da aurenta  ba,,*_
*_kusani nimafa musulmace Kuma gwargwado inada ilimi da sani akan addina nakumasan me nakeyi Kuma ni nasan abinda nake rubutawa amma ku masu karantawa Sai ku kasa hakuri kuga yanda labarin zai kasance wasuma harda zagi da munanan kalamai to Wanda hakan ba tunani bane Dan haka please and please for god sake idan Kunga abinda bakwa iya karantawa to ku barshi ba dole bare zagi da cin fuska yashigo._*😠
 

Tsakar dare suka shiga garin Abuja Kuma zuwa Time 'din ayshah gaf take da ficewa hayyacinta sbd mugun zazza6i da ciwon marar datakeji.

Sannu fannah ke Mata cikin tausayawa da damuwa tareda tsoron Kar 'yar mutane ta mutu a hannunta.

Wata 'yar babbar private hospital dake kusada anguwarsu ta nufa Kai tsaye batareda sun Isa gidaba Nan aka kar6eta tareda qoqarin fara Bata treatment 'din gaggawa sbd tashin farko suka gano cikin dake jikinta ne ke qoqarin qarasa zubewa Nan suka fara qoqarin tsayar da jinin.

Tun fannah na 'daukar abin da sauqi saigasu da kwana asibitin.,,

Koda ayshah ta farka abun farko da fannah tace Mata shine azubar da cikin.

Kallon mamaki ta aiketa dashi fuskarta na qoqarin bayyana farin cikinta tace,

Cikina yananan bai zubeba?

Cikeda mamakinta fannah tace,

Yana Nan amma banga amfanin barinsa ba gwara ki zubar tunda shege n....

Cikin tsawa ta dakatarda ita hawaye suka gangaro Mata tace,

Cikina ba shege bane 'dan halak ne,
'dan sunna Kuma Koda shegen ne ta bazan ta6a zubarwaba sbd shika'dai ne abinda Zan riqa gani naji sanyi arayuwata zuwa Nan gaba,,,,
Bansakaki Zama Dani doleba idan kinajin bazaki iya Zama Dani Dan inada cikiba to ko anan Zaki iya tafiya kibarni ahakanma nagode..

Ajiyar zuciya fannah tasaki tareda miqewa tsaye cikin kulawa tace,

Ayshah bance lallai saikin zubarba shawarace nabayar a tunanina ba cikin aure bane Kuma kince bazaki zubarba ba shikenanma ki daina kukan ya Isa haka...Bari naje na kar6o Mana sallama muje gida Dan gskia nagaji da zaman asibitin.

Tana fita ayshah tabi bayanta da kallo cikin mamakin sanyin halinta sbd yanda ta gasa Mata maganganu Amma bataji haushiba..

Fannah ta girmeta zaikai kamar da shekaru biyar,,
Fannah kyakkyawar chocolate mace Mai kyan jiki,,Sam batada zafi  tanada hakuri da tausayi Amma a gurin maza labarin bambam ne don kuwa Bata raga musu Bata 'daga musu qafa hakama batajin wuyar ci musu mutunci sbd namiji ne sanadin qorar da iyayenta sukayi Mata,,

Ahankali tariqota suka fito tashigarda ita mota suka bar asibitin.

A wata anguwar masu Hali gaban wani qaton flat Mai kyau da tsari taga sunyi horn Mai gadi yazo da saurinsa ya bu'de musu gate suka shiga harabar gidan sukayi parking..

Kallonta gidan tayi zuciyarta na karyewa idanuwanta na qoqarin kawo hawaye sbd tunanin iyayenta daya fa'do Mata Dan tabbas tafi sha'awar Zama taredasu Koda acikin ruga suke akan irin wannan daular da aka Tara ta hanyar 6arna.

Qofar shiga babban palon sukayi fannah ta fiddo keys ta bu'de suka shiga.

Zaunar da ita fannah tayi  tareda Zama kusada ita cikin sanyin murya tace,

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now