taura biyu 22

8.3K 743 27
                                    

*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

              *22*


Qarfe Tara da kusan rabi baccin wahallalen zazza6in da yayi ya farka tareda bu'de idanuwansa ahankali ya saukesu akanta,
Take yaji wani sabon sonta da tsananin tausayinta na qara shigarsa sbd ganinta zaune gabansa bacci ya 'dauketa fuskarta jajir Kuma a kumbure sbd kukan datasha kafin baccin ya 'dauketa.

Ahankali ya saki wani lazy smile kafin ya miqe ya nufi qofar toilet yashige.

Wanka yayi cikin kwanciyar hankali farin ciki da nutsuwa na shigarsa...,
Alwala ya 'dauro kaman yanda shaikh ya koyar dashi kafin yafito 'daure da farin towel qal 'daure a qugunsa.

Har time 'din bacci take a zaune inda ya barta Kuma Sam bayason tayarda ita sbd ganinsa ahaka zai iya sa ta tsorata dashi besides that tana buqatan bacci da hutu sosai.

Telephone 'din dake cikin room 'din yayi amfani dashi yakira boutique 'din dake cikin hotel 'din yayi ordern kayan bacci nasa da nata tareda dogayen rigunan dazasu iya sakawa suyi sallah harmada designer perfumes masu sanyayan qamshi nasa da nata.

Bayan yakashe restaurant dinsu yakira yakuma ordern abinci kafin ya dawo gabanta ya zauna tareda qura Mata lazy eyes 'dinsa Yana murmushin farin cikin kasancewarta tasa.

Ahankali ta bu'de idanuwanta tana ganinsa tayi saurin miqewa tareda sunkuyar dakai gabanta na fa'duwa Dan kallo 'daya tayiwa lafiyayyan jikinsa dake bayyane ta 'duqar da Kai.

Murmushi yasaki harsaida sautinsa yafito ya matsota sosai hartanajin qamshin sabulun da yayi wanka dashi na papaya.

Hannunsa ya Kai ahankali ya 'dago da fuskarta ya qura Mata ido tayi saurin rintse idanuwanta hawaye na gangarowa daga cikinsu.

Fuskarsa ya matsa daf da Tata zaiyi magana akayi knocking qofar room 'din.

Rintse ido yayi tareda sakin ajiyar zuciya kafin ya juya ya nufi qofar...

Orders 'din dayayine aka kawo lokaci 'daya..
Kar6a yayi tareda 'dauko credit card 'dinsa ya miqa  musu suka wuce.

Bu'de kayan yayi tareda 'daukar farar jallabiya Mai santsi da kyau yasaka sannan ya fesa wani cool turaren signature na oriflame  kafin ya juyo ya kalleta tananan tsaye still kanta a qasa..

Matsowa yayi gabanta ya riqo hannuwanta duka biyi tareda 'dan duqawa ya leqa fuskarta yace,

My love am going to pray now,,, you should take a shower too then come and pray...

Ba musu ta zame hannayenta ta nufi toilet tashige ta rufo.
Wanka tayi tareda 'dauro alwala saikuma takasa fitowa sbd towel 'din yayi qarami sosai Sai kawai ta goge ruwan jikinta dashi ta maido kayanta ta fito..

Zaune yake kan sallaya Yana qoqarin karanto azkar da salatin da shaikh ya koyar dashi ta kallesa duk saitaji ya sake Kama zuciyarta ta qaraso ahankali ta tsaya kusadashi ta tayarda Tata sallar.

Tana idarwa tafara karanto azkar 'dinta a fili cikin sanyin murya Nan ya juyo ya fuskanceta Yana qara gyaggyara inda yayi kurakurai.

Sun 'dau tsawon mintuna ahaka kafin suka kammala Ya zauna kan sofa tareda jawota ba zata ya zaunar a cinyarsa Sai kuma yasaki 'yar qara ahankali da a rikice ta kallesa cikin tashin hankali saiya saki qayataccen murmushi Yana kallon fuskanta cikin tsokana yace,

Oh my God you broke my legs..

Ajiyar zuciya tasake tareda harararsa batareda tasaniba

Baisan sanda yasaki qaramar dariyaba Yana kallon bby face 'dinta  cikin wasa yakuma cewa,

Oh my God sweetheart you're eyeing me...

Sunkuyar dakai tayi da sauri tareda miqewa yayi saurin dawo da ita amma saita zille tazauna gefensa maimakon jikinsa.

Abincin da aka kawo ya bu'de tareda kallonta yace taci...

Daqyar yasami ya takurata taci ka'dan ta miqe tashige toilet kafin shikuma yasamu yaci slice 'din pizza 'daya da milkshake.

Wanko bakinta tayi ta fito ta tsaya tareda kallonsa a 'dan daburce tace Masa,

Deen let's go home please it's already late.

Tasowa yayi ya tsaya gabanta yace,

Baby it's already late and I don't drive at nights I'm scared of dark.

'daure fuska tayi tana qoqarin danne hawayenta tace,

Ok I will go myself.

Hanya takama ta nufi qofar fita tajita a rufe Gam tasake mur'dawa tajita Gam tajuyo a tsorace zata kallesa taji mutum a kusada ita tayi saurin matsawa ya kalleta yaga yanda duk takasa nutsuwa ya matsa nesa da ita yace,

Ayeeshah please don't get me wrong but....

Kuka tasakar Masa tun bai qarasaba yayi saurin matsowa a ru'de yace,

Please don't cry I will take you home now...

Keys 'din motarsa ya 'dauka tareda kamo hannunta ya bu'de qofar suka fito.

Har lokacin ruwa ake sosai Amma haka ya 'daure ya tada motar suka baro hotel 'din.

Tafiyar minti shida sukayi yafara sakin hanya Yana qure kallonsa a hanya sbd komai baya gani sbd qarfin ruwan ga qarin darene Kuma Daman shi baya tuqin dare sbd tsoron fitama yake da daddare.

Ba zato sukaji sun daki wani Abu sun fa'da qatuwar gota...

A tsorace ya kashe motan ya juyo ya kalleta yaga idanuwanta a waje cikin fargaba da tsoro qarara yawu ya ha'diye tareda tattaro qarfi da jarumta sbd Kar tagane tsoronsa da yawa ya bu'de motar ya fita.

Qatuwar gotace suka fa'da Kuma ya tabbatarda bazasu iya fitaba Saida taimako gashi ba mutane.

Komawa cikin motan yayi ya fa'da Mata dole ta fito tana matsar hawaye suka fara takawa cikin ruwan suka koma hotel 'din..
Saidai kafin su Isa kowannensu ya daku da ruwan musamman mashi da ko Yaya ruwa ya ta6asa ba 6ata lokaci zai fara zazza6i..

Itadai Kam zazza6in ne Mai qarfi ya kamata tun kafin su Isa room 'dinsu tafara Jin kamar zata zube.

Suna shiga yayi saurin kashe ac tareda zaunar da ita a kujera ya zare Mata hijab 'dinta dake jiqe tareda saurin 'dauko kayan baccin dayayi order 'dazu yafara qoqarin cire Mata doguwar rigar atampar dake jikin tayi saurin riqe hannunsa ya kalleta kaman zaiyi kuka yace,

Ayeeshah please don't do this to yourself you're completely wet and...

Kar6ar kayan baccin tayi tareda miqewa da qyar ta fa'da toilet Dan itama kayan a matse take dason ciresu Dan har 'digar ruwa suke.

Doguwar rigar bacci ce cotton fara qal mai 'dan kauri Amma batada wani tsawo Dan duka fararen  cinyoyinta a waje suke hakama hannuwanta Dan hannun shimi ne da ita gashi har bra 'dinta tacire Dan itama a jiqe take.

Kasa fitowa tayi ta zauna  gaban mirron ciki tareda qanqame jikinta dake tsananta rawar sanyi.

Tu6ewa yayi shima tareda saka kayan bacci shima masu kauri ka'dan ya zauna jiran fitiwarta Amma shiru.

Matsawa yayi bakin qofa yakira sunanta Amma shiru..
Da sauri ya bu'de qofar cikin fargabar ko wani Abu yasameta aciki.

Qarasawa yayi da sauri a ru'de tareda tallafota jikinsa Yana cewa,

Oh my God baby you're burning.,

'daukanta yayi da sauri ya fito ya kwantarda ita a gado tareda rufeta da blanket Mai laushi ya hau shima tareda jawota jikinsa ya rungume ahankali.













Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now