taura biyu 21

10.7K 662 45
                                    

*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *21*

Tsayawa Finn yayi akansu Yana kallonsu cikin wulaqanci ganin har lokacin da sauransu ya juyo ya kalli tiger yayi Masa alama da ido...

Kallon yaransa tiger yayi Sai aka Kuma 'debo ruwan qanqanra a qaton bucket aka Kuma jiqasu tareda cigaba da dukansu..

Iya dakuwa Kam sun daku bama kamarsu Yaya abbakar dasuke samari anfi dukansu duk da dai Suma su baban ba a raga musu ba...

Sake kallonsu Finn yayi yaga sun bugu yasaki murmushin qeta tareda fiddo wayarsa ya 'daukesu yaturawa mum kafin yakirata yace ta duba..

Dariyar Jin da'di tayi lokacinda taga hoton takira tace a kaisu inda aka 'daukosu a watsar..


Zamewa tayi daga rumfar dayayi Mata takoma bakin gado ta zauna kanta a qasa tana kallon dogayen fingers dinta..

Dawowa yayi kusada ita ya zauna shima ya qurawa hannun nata ido..

Ayshah please lets get married before informing our families about us...

'dagowa tayi ahankali takallesa ta kawar da idonta kafin ahankali tace,

No Nik...I can't marry you without my family's approval.. besides that I'm Muslim you're Chris.....

Katseta yayi da cewa,

I'm ready to convert my love....I want to become Muslim too...

Kallonsa tayi idonta na cikowa da hawaye sabuwar soyayyarsa na qara shigarta sbd ganin yanda idonsa ya rufe bayako tuna masifar dake gabansu ta dukkanin 6angaren biyu...Dan tasan gidansu sun gwammace ta mutu dasu barta dashi..

I love you ayeeshah...

Juyarda Kai tayi tareda sakin 6oyayyen murmushi..

Fira yafara yi mata ahankali Yana Bata lbarinsa saidai tayi murmushi kawai batareda tayi maganaba.

Mantawa suka da komai da kowa Saida sukaji knocking tayi saurin miqewa tsaye gabanta na fa'duwa jikinta na rawa..

Kallonta yayi tareda sakin qaramin murmushin daya bayyana white teeths 'dinsa qasa qasa yace,

Wait hia...

Qofar ya 6ude ahankali saiyaga nurse ce yasaki ajiyar zuciya ahankali tareda juyowa ya kalli yanda ayshan tayi zuru duk saiyaji tabasa tausayi ya matso kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta zaiyi magana tayi saurin zillewa ta Fice 'dakin da sauri tana Jin farin ciki na shigarta tako ina.

Shafa kansa yayi tareda kwantawa a gado Yana Jin farin ciki Mara misaltuwa.

Tundaga nesa ta hango qofar gidansu da kamar mutane gabanta yayi fa'duwa ta qarasa a darare..

Su Yaya sani dasu babanta ne ke qoqarin shigardasu baba alhaji cikin gida dukkaninsu ba kyan gani kawunansu da fuskokinsu a kumbure da jini a kayansu..

Yawu ta ha'diye daqyar tashigo gidan Nan ta tararda kowa hankalinsa a tashe su husna ma harda kuka ganin mummunar aika aikar da akayiwa su baban.

Sosai itama hankalinta ya tashi Dan koba'a fa'daba tasan wannan aikin mum ne..

Har dare gidan ba da'di Dan kowa na cikin jimami da baqin ciki..itadai Bata kosanyin wani qwaqwaran motsi sbd tsoron Mai zai biyo baya.

Har akai kwana biyu ba'ai zancen komaiba kan al'amarin Kuma tun ranar Bata fitaba sbd tsoro da fargabar abinda zai biyo baya duk da ba qaramin tausar zuciyarta takeyiba akan son sanin ya jikinsa yakeba..

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now