taura biyu 24

8.2K 650 29
                                    

*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

              *24*

   

Da daddare dukkaninsu kasa bacci sukayi musamman mashi Sai juyi yake kewar matarsa na shigarsa,
itama anata 6angaren lafewa tayi Dan Kar juyin yayi yawa ayi zargin wani Abu.

Washe da asuba cikin 'dakinsa yayi sallarsa Yakoma ya kwanta gari na waye saiga mum da Bible 'dinta tafara jero Masa adduointa yanaji ya lafe kamar maiyin bacci sbd jiyake kaman tana watsa Masa ruwan zafi a kunnuwa.

Tana gamawa ta tadashi tareda kallonsa cikin kulawa tace yatashi ya shirya lokacin zuwa makaranta nayi.

Lumshe fararen lazy eyes 'dinsa yayi yanajin tsananin buqatar son ganin ayshah ya sauko daga gadon ahankali tareda miqewa ya fa'da toilet.

Duk iya zagayen dazaiyi yayi a makaranta da anguwar Amma baiga ko alamar ganinta ba haka ya lalla6a Yakoma gida a wahalce zuciyarsa ba da'di.

Itama dai Kam sukuku ta wuni ba wata walwala gashi ko maganar zuwa makaranta ba Wanda yayi Mata.

Abu kamar wasa saigasu har tsawon sati Basu ga junaba ita Sam anhata fita yanzu shikuma Yayi yawon yayi neman Amma Babu alamarta.

Sati na biyu kenan da yanxu Kuma zuwa lokacin daga shi har ita kowa danginsa sun gano Yana cikin damuwa ita tayi wata irin Rama shikuma rigis ya kwanta ciwo.

Zaune take tana kallon yanda su husna ke Shirin fita zuwa gidan anty Amina a sanyaye ta bu'de baki tace,

Wai sauri da 'dokin me kukeyi na zuwa gida musamman make husna.

Asma'u dake saka hijab tace,

Fa'da Mata zamuyi tazo taga kayan lefen da ya Umar ya ha'da miki.

Duk da batada wani kuzari a jikinta batasan sanda ta tashi zaune ba ta kalli asma'un da kyar tana ha'diye yawu tace,

Lefen me?

Kallon rainin wayo asma'un ta jefeta dashi kafin tace,

Na aurenku Wanda za'ayi Nanda sati biyu.

Hawayen datake dannewa ne suka 6alle Mata tayi saurin juya musu baya kuka na qwace Mata.

Binta da kallo sukayi basuce Kuma cemata komaiba suka fice.

Bayan gadonsu tashige tafara rero kuka cikin tashin hankali tareda rashin sanin abinyi.

Kamar daga sama saiga nuratu tashigo 'dakin tana ganin halinda take ciki ta qaraso gurinta da sauri tana kallon yanda idanuwanta sukai mugun kumburi.

Kasa tambayarta dalilin kukan tayi cikin sanyin murya tace,

Anty ayshah ummi ce tace nazo nace Miki ki shirya mutafi gidan anty Amina muma sbd duk yau zasuso ganin kayan aurenki gwara ki 'dan fita.

Kallon nuratu tayi da jajayen idanuwanta kamar zatace Bata son fita Koda tsakar gidan ne saita tuna tana tsananin buqatar ganinsa Dan sanin abinyi.

Wanke fuskarta tayi tareda canxa hijab tafito..

Gidan nasu Ashe tuni yafara cika da 'yan uwansu dake garin Sai murna da farin ciki suke.

Kanta a sunkuye tayita gaidasu harsuka fito gidan.

Tunda suka fito take tunanin hanyarda zatabi tagansa suyi magana.

Daf dazasu Isa unguwarsu anty amina kamar daga sama saita hango Davina sun fito wani qaton mall itada mum da Finn..

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now