taura biyu 27

8.8K 681 47
                                    

*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._
 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *27*

*_godiya Mai tarin yawa ga masoyan TAURA BIYU aduk inda suke.._*💋

Babbar Riga baba alhaji ya gyara Yana qara gyara Zama sbd shi Sam bai fahimci zancenba ya kalli Dr yace,

Aa wannan dakake magana ba itace Wadda muka kawoba,,
Wadda muka kawo itama tanan cikin 'dakin sunanta ayshah Kuma budurwace Bata ta6a aure ba...yauma ne dai za'a 'daura auren nata kaga mijin Nan a tsaye.

Takaici ne ya 'dan Kama Dr Amma fahimtar dayayi da Rashin sanin komai dasukayi akan 'yarsu saiya gyara Zama Dan sake musu bayani dalla dalla..

Alhaji maganar danake fa'da muku anan bayanine akan 'yarku da kuka kawo..'yarku ayshah tana 'dauke da ciki na haihuwa 'dan wata 'daya da satittika...

Sharce zufa baba alhaji yayi ya juyo ya kalli baba qarami dashima tuni babbar rigarsa ta Shirin 'daurin aure ta jiqe sbd zufa...

Atare suka juyo suna aikawa Umar da zuciya tagama kashesa Banda mazari ba abinda jikinsa keyi idanuwansa kuwa ko gani sosai bayayi dasu sbd baqin ciki da tafasar zuciya...

Juyawa yayi a fusace zai fita baba qarami yayi saurin Shan gabansa tareda sharara Masa lafiyayyan Mari...

Ji yayi kansa na neman bugawa ya 'dago da jajayen idanuwansa yakalli su baban yaga irin kallon dasuke Masa ya daki bango da qarfi kamar zautacce yace,

Karma kufara wannan tunanin,, tunda nake a rayuwata ko hannun ayshah banta6a riqewa bare har ni nayi Mata.....

To idan bakai bane wane?""""" Baba alhaji yafada da qarfi cikin zafin zuciya da 6acin Rai.

Jiki sanyaye baba qarami ya kalli baba alhaji yace,

Muje gida mayi komai acan gaban malam babba.

Fitowa sukayi kowanne daqyar babbar rigarsa ke 'daukarsa sbd kunya da baqin ciki..

Kallonsu mama sakina tayi cikeda damuwa tace,

Lpia kuwa?
Meke damunta likitan yace?

Fuskarsa na kallon wani gurin yace,

Ayshah cikine da ita Dan haka kitashi maza yanzu muje gida ayi komai can gaban kowa.

Yawu ta ha'diye daqyar jikinta itama Yana 'daukar rawa sbd gabaki 'daya ta nemi nutsuwarta ta rasa dajin wannan mummunan zance daga bakin baba alhaji.

'dakin tashiga ta tararda ayshan ta tashi saurin 'dauke Kai tayi cikin tashin hankalinta daya kasa 6oyuwa tace,

Taso maza gida zamu yanxu..

Ba musu ta sauko gadon ahankali jikinta na tsananta sanyi hakama fa'duwar gabanta na tsananta..

Koda suka fito su baba harsun samu mota sun shiga suna fitowa Umar yabar gurin yaje yahau mashin Dan bayajin zai iya shaqar numfashinda jinin Deen dake cikin ayshah yake shaqa.

Tunda suka shiga motar Babu Mai ko qwaqwaran motsi sbd kowada tunanin dayake ransa.

Umar ya rigasu isowa shiyasa koda suka iso ya Tara kowa a palon ana jiran isowarsu Dan ko magana baya iyayi bare yafa'di abinda yake faruwa..

Suna shigowa palon kowa yabisu da idanuwa sbd fargabar Jin koma menene Dan tun a yanayin Umar 'din suka tabbatarda koma meyene bamai da'di bane.

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now