taura biyu 17&18

8.1K 663 19
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

              *17&18*

koda Nik Yakoma gida ya tsaya gaban mirror yakalli kansa saiyaji hawaye sun ciko idanuwansa..
Tubewa yayi ya jefo kayan qasa ta windown dakinsa ya fa'da toilet yayo wanka Banda zazza6in wuya Babu abinda yakeji.

A daddafe ya saka kayan bacci black yashige bargo ya kwanta jikinsa na rawar sanyin zazza6i..

Qarfe Tara mum tashigo dakinsa Finn na biyeda ita tana ganin yanda yake shaking cikin bargo ta qaraso da sauri tana Kiran sunan Jesus..

Tallafosa tayi taji jikinsa da mugun zafi ta kalli Finn cikin tashin hankali tace,

quickly call Dr Finn.

Fiddo wayarsa yayi daga aljihu ya latsa Kiran Dr cikin gaggawa.

Shigewa yayi jikin mum 'dinsa yana fiddo numfashi ahankali cikin azaba yace,

Mum I'm fine,, it's just a fever,,I will get better soon there's no need to call the Dr....

Cikin karyewar murya kamar zatayi kuka tace,

Quite.. you're not fine my love and it's not a normal fever,, you're hiding something from me,,I  can feel it.

Lumshe idanuwa yayi cikin sanyin murya qasa qasa yace,

Mum,,,,mum..i.i..I'm in love....I love someone.

Wat""""tafa'da da qarfi tareda kallon fuskarsa cikin rashin Jin dadi tareda rashin na'am da zancen cikin damuwa tace,

You can't be in love my boy,, you're too young for that and I ca....

Katseta yayi cikin sanyin murya da cewa,

I love her so very much mum,,,I can't even imagine my life now without her mum...mum..I really want her for myself,i love her mum..I madly love h....

Rungumesa tayi cikin tausayinsa sbd dukkanin alamu sun nuna Mata baqaramin so yakewa kowaceceba..

Share Masa hawaye tayi tana adduar Allah yasa ko wacece kada tayi amfani da wannan zazzafar soyayyar da Nik yake Mata ta cutatar Mata da yaro.

Kwanansa biyu Yana zazza6i Mai zafi ko qasa baya iya saukowa bare ya fita,,
Mum dinsa kuwa hutu ta dauka Dan bawa 'dan lelenta kulawa hakama 'yan uwansa wannan karon dukkaninsu sun matuqar tausaya Masa sbd yayi matuqar sanyi kamar ba Nik ba danko irin muguwar sakuwar dayake acikin gidan ta rage kullum Yana kwance.

Duk iya yanda take danne damuwarta saidata bayyana a jikinta sbd ramar datayi su husna sunyi faman tambayar harsun gaji Amma alamarin bamai kar6uwa bane ko a zuciyarta bare  fa'duwa.

Kwananta biyu kotaje makaranta Bata gane komai sbd dukkanin nutsuwarta ta tarwatse Wanda Sam takasa samun kuzari ko qarfin tattarota.
Ahaka take lalla6awa har tsawon kwana biyu.

Yau Bata samu bus da wuri ba shiyasa tayi yammacin dawowa gida,,

Ahankali take tafiya cikin nutsuwa duk da kwanakin nutsuwarta rawa take,,

Daf dazata shiga kwanar layin gidansu taga su ya Umar taredasu Yaya abbakar kusan su shida kowanne da abun duka jikinsu har rawa yake bama Kamar ya Umar 'din da idanuwansa yafi nakowa rufewa da 6acin Rai.

Mummunar fa'duwa gabanta yayi tai saurin sunkuyar da Kai cikin tsananin fargaba..

Kallonta ya abbakar yayi cikin 'daga murya yace,

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now