taura biyu 3&4

9.1K 704 14
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
       _Mi amor-mi vida_....

_viawattpad@mamuhgee_

           *3&4*

Toilet tashige da hanzari tareda rufowa tasaki wani sabon kuka ahankali,

Gabaki 'daya rayuwarta a makarantar ta zamar mata masifa Wanda take danganta hakan da qaddararta.

Rarrashin kanta tayi daqyar kafin ta zare niqaf dinta ahankali takalli fuskarta jikin mudubi taga baiwa ta kyau da tsarin halitta da Allah yayi mata rashin sani yasa ana mata 'daukar mummunar halitta.

Share hawayenta tayi tareda maida niqaf dinta tafito tawucewarta gida gabaki 'daya batareda ta tsaya attending sauran lectures 'dinta ba.

Da daddare bayan sunci abinci itada su husna tareda sauran yaran gidan suka nufi babban palon baba malam gurin 'daukar karatun dare Wanda qaidar gidance kullum da dare saisun 'dau karatu.

Awa 'daya da rabi sukayi sunayi kafin aka gama.

Gyara Zama baba malam  yayi tareda gyaran murya 
Nan kowa ya nutsu sbd sauraron Mai zai fa'da.

Kallon sauran dattijawan qannensa yayi kafin yace,

Mustapha 'dana ne Kuma  ya 'dauko zance Mai girma Don kuwa ya take akidar gidan Nan daya tarar tun kakanni tunma kafin ni mahaifinsa a haifeni..
Ma'ana dai bayan mun tsayarda maganar ha'dashi aure da yar uwarsa jininsa ya tsallake waje yana neman auren wani yaren ma'ana bahaushiya.

Wani yawu iya lami ta ha'diye Dan kuwa tasan mummunan hukunci 'danta zai fuskanta Dan anta6a irin haka can baya abun baiyi kyau ba sbd Saida aka rasa rayuka.

Tsit palon yayi babu Wanda ya motsa sbd jinjina girman laifin da mustaphan yayi.

Cigaba baba Mal yayi da fa'din,
Mustapha kaje kashirya gobe bayan sallar juma'a  za'a 'daura aurenka saudat a goben zaka koma gida nijar tareda matarka Kuma bamu yafe katako qafarka Nigeria ba kokuma Kiran 'daya daga cikinmu Sai bayan shekaru biyar.

Sunkuyar da kansa  yayi hawayen baqin ciki da damuwa suka ciko idanuwansa sbd hukuncin da iyayensa suka yanke Masa bazai iya jadasuba Wanda wannan tarbiyace da'aka ba zuriar gidan kaf tun suna yara.

Saudat kuwa wani irin kukane ya kufce mata ahankali batajiba Bata ganiba laifinsa ya shafeta bayan auren bazata an datse mata karatu gakuma nesa dazatai da gida bako waya har tsawon shekara biyar.

Jikin kowane yasaki Banda iyayensu maxa dake da'da nanata yi musu fadan kowa ya kiyaye aikata irin hakan,

Baba Mal ma fa'da Mai tsanani ya 'dora dashi sbd ran iyayensu ya 6aci matuqa.

Umma sakina kuwa Jan 'yarta tayi cikeda tausayawa suka fice kowama ya fice jiki a sanyaye.

Ayshah kuwa 'dakin ummi tashige ta kwanta jiki asanyaye tana tsiyayar hawayen tausayin saudat da yaya mustapha.

Kallo 'daya umminta tayi Mata ta 'dauke Kai sbd Bata cika kulata kasancewarta 'yar farin..

Cikin sanyi da karyewar murya tace,

Duk lokacinda Abu yasamu 'dan uwanka Mara kyau to kayi qoqarin nesanta kanka da abun Nan sbd gujewa mummunan sakamako irin wannan.

Zuciyata takasa nutsuwa da zuwa makarantar ki Dan haka ki guje afkawa cikin irin wannan mummunan halin.

Tsit tayi tana sauraron nasihar umminta duk datasan Sam ita bazata iya fadawa soyayya da wani yarenba bayan nata Dan itama gwargwado tana qyamatar wani yaren.

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now