Auren sirri 09

181 12 0
                                    

🔐Auren Sirri🔐 0️⃣9️⃣
A cikin satin babu abinda mummy da maama keyi banda shawarwarin yanda auren King da Nadia zai kasance bayan gama karatun King din, yayin da a gefen Nadia banda rawar kai da sanarwa friends dinta zatai aure babu abinda takeyi, da alamun sun baiwa mgnr Ayisha baya kamar ba'ayi ta ba ma a wajen su. Yayin da bangaren King ya gaza katabus sai ido ya kawo ya zuba musu amma a ranshi ya kudurce sai dai su aurawa Nadia wani King din badai shi ba.
** **
Bangaren Ayisha kuma lafia lau dan bata saka damuwa ba akan abinda King ya fada mata duk da ta damu din musamman akan batun kin amincewar Mummyn King, to amma damuwar Mamy ta wuce duk wata damuwa data shafi batun ta da King, ko jiya haka ta kara samun Mamy tana kuka da hawaye shabe shabe tana sumbatun tayi nadama a yafe mata kuskure ne ta aikata wanda tage regretting iya tsayin lokacin nan, haka dai ta dakata bakin kofar Mamyn ta rika jiyo sambatun Mamyn cikin kuka wanda itama a karshe fashewa tayi da kukan ta ruga dakin ta tayi mai isar ta har Allah Ya gajishsheta. Ta kwana da wani irin ciwon kai da zuzzurfan tunanin wannan wani irin laifi ne Mamy tayi daya hanata jin dadin rayuwar ta? Suwaye take nema su yafe mata? Shekara nawa ta kwashe cikin wannan halin? Meyasa Mamyn ta kasa fitowa koda ita ce tayi mata bayanin abinda kenan? Meyasa Manyn ke boyewa sai ita kadai take cikin kunci??? Tambayoyi gasu nan da yawa dai, to a haka satin ya kare aka shiga wani satin wanda daga shi ne zasu fara final exams dinsu.
** **
Iya kokari King da Ayisha sunyi shi dan kada su samu problem da exams dinsu, sai suka aje duk wani batu tamkar babu abinda ke gudana ga dukkanin su, abu daya daya karu shine shigowar Amal kanwar King rayuwar Ayisha da karfi da yaji, a Dubai take nata karatun Medicine kuma suna cikin hutu ne shiyasa ta dawo gida. Kusan kullum tare da King suke zuwa school, tun Ayisha tana dari dari da ita har dan dolen ta ta saki da Amal suka zama friends amma saida ta tabbatar da takai Amal wajen Mamy kuma Mamyn ta amincewar friendship din sana suka kulle tamkar ba sabbin haduwa ba.
Amal ta lunka Ayisha surutu nesa ba kusa ba dan wani lokaci Ayisha har mamakin Amal take na surutun ta har ta taba ce mata gaskia Amal ina mamakin yanda kike karatun Medicine da wannan surutun naki, saidai Amal tayi daria tace haka mutane ke fada amma kinsan halitta ne kuma sanda muke zafin karatu ba zaki taba cewa nice mai surutun nan ba, sai suyo daria. Duk wannan kawancen kuma basu taba yin maganar data shafi Ayisha da King ba, yawancin lokuta ma King yana tare dasu to a haka suka ci gaba da exams cikin maida damuwa ba damuwa ba sai fuskantar ci gaban rayuwa.
** **
Gefen Mamy kuma taci gaba dayi musu shirin komawa kasar su ta haihuwa, a boye take komai badan yaran nata ba zasu bata hadin kai ba sai dan tana ganin kamar abun zai dame su kasancewar an haife su anan sun saba rayuwa anan da komai nasu dan haka rana tsaka ace za'a kaisu wani kasa na daban abun zai dan dame su a ganin ta. To Alhamdulillahi kusan ta gama da duk wani shirye shirye sai jiran lokaci kawai.
** **
A satin su na karshe na gama exams a cikin satin Mummyn King da Maaman Nadia suka fitar da ranar biki watanni biyu masu zuwa bayan gama exams kuma zuwa lokacin Baban Nadia ya koma Kasar shi Nigeria tare da iyalan sa gaba daya. Daddyn King shi aiki ya kaishi a kasar dama, shina kuma dan Nigeria ne saidai duk shekara yana zuwa yaga gida ya dawo, iyalan nashi ne ba wani zuwa suke ba har gara Mummy takanje inta mula tasha iska amma yaran sun manta rabon su da kasar su ta haihuwa.
Ganin King bai kuma tada musu zancan Ayisha ba yasa suke komi cikin kwanciyar hankali barin ma dai Nadia, Daddyn King baisan abinda ke faruwa ba sai zancan auran Nadia kadai da aka sanar dashi lokaci yayi ya kamata ayi auren hakanan dan haka sai kawai ya maida hankalin shi akan komawa gida Nigeria ayi bikin acan kamar yanda Baban Nadia ya shawarce shi kenan.
** **
Yau exams din da alamun tayi dadi sosai kila shiyasa basu jima ba suka fito suka cimma Amal zaune kasan bishiya rike da katin bikin King da Nadia, bata san zuwan su ba sai katin kawai taji Ayisha ta zare a hannun ta tana dubawa take cewa su Amal wannan katin kuma na meye aka kura mashi ido hak... bata ida kai aya ba idon ta yakai ga ainahin sunan king wato Mu'azzam Ibrahim Fari da Nadia Abubakar Manga sai lokacin bikin su. Wani irin jiri ya nemi kayar da Ayisha da sauri Amal ta ruko ta ta zaunar da ita kusa da ita gami da fadin take it easy Ayisha. King baibi ta kansu ba sai katin daya tsunto kasa wanda ya subuce daga hannun Ayisha, shi kanshi ya razana da ganin katin dan baisan har takai ga buga kati ba.
Cikin bacin rai ya fara hararar Amal yana cewa akan wani dalili zaki biyo mu da wannan banzan katin har school? Saboda Aishh ta gani ne ko? To ta gani sai ki tashi ki bamu guri, kasancewar Amal mara saurin bacin rai yasa ta dago kanta cikin tsananin tausayin King da Ayisha ta fara magana da 'nayi tunanin zuwa yanzu mu ukun nan mun zama daya babu wani abu da zamu iya boye wa junan mu, wannan dalilin ne yasa na taho da katin anan saboda mu samu mafita cikin lamarin nan King badan in batawa Ayisha ba, banbancin yanda kakejin Ayisha cikin ranka kadan ne da yanda nima nake jinta cikin rai na, fisabilillahi nake son Ayisha da kuma son da nike maka a matsayin ka na shakiki na ya shafeta, kuma ina tausaya muku dan haka fushi ba namu bane sai neman mafita...
Kamar an bude bakin Ayisha ta katse Amal da cewa 'kada ku wahalar da kanku Amal, meyiyuwa ni da King are not destined to be together, ni mai daukar kaddara ce akoda yaushe a kuma ko wani hali dan haka wannan kaddarar ma na dauke ta dama ko Mamy bata san da tarayyata ta soyayya da King ba kuma ina fargabar ranar da zata sani ba tare da na sanar da ita ba da kai na..
Cikin zafi king ya katse Ayisha shima bangane kin dau kaddara ba? Da bakina kinji nace na amincewa auren Nadia ne? Dama zaki iya rabuwa dani saboda wani dalili mara tushe? Son da kike mani daman ba gaskia bane? In subdued Ayisha tace 'ni yau kake tuhuma da bana son ka Mu'azzam? Hakika iya sanin dana maka baka taba man wani abu dayai hurting dina ba irin yau'. Ta mike tana mai rike kukan ta da sauri tai gaba.
King ya mike da hanzari zai bita sai Amal tai saurin kamo hannun shi tana girgiza mai kai gami da cewa she's already hurt and she wont listen to whatever u have to say, let's give her some time before ur next exam. Kamar mara laka ya dawo jabar ya zauna gami da dafe kai idanun shi sunyi jawur, Amal ta mika mashi ruwan dake kusa da ita, daya kafa kai seda ruwan suka kare yai cilli da robar, da wannan yanayin Amal ta shigar dashi mota taja suka wuce gida, kasancewar tunda suka fara zuwa school din tare Amal ta dakatar da masu zuwa tare da King a cewarta zata na kula dashi.

Shiru shiru Mamy tana jiran Ayisha tazo office dinsu sana su wuce gida har dai taga ta kara one hour sai tayi deciding ta tafi gida kawai kuma dabarar kiran waya baizo a ranta ba. Adnan ta fara gani a falo yayi tagumi, da sauri ta karasa wajen sa tana tambayar sa wani abu ne ya samu Ayishan? Girgiza mata kai yayi yace bazan iya ganewa ba Mamy amma ta shigo tun dazu bata kula ni ba ta shige daki ta rufe kanta bansan abinda ke faruwa ba kuma taki bude dakin... kafin ya karashe Mamy tayi gaba sai shima ya rufa mata baya, knocking kofan Ayisha tayi gami da kwala mata kira Ayisha! Ayisha!! Ayisha!!! Maza ki bude dakin nan, kafin ta kara magana Ayisha ta bude dakin sai kuma ta tafi ragwaf zata fadi da sauri Mamy da Adnan sukai kanta suna Subhanallahi! Ayisha! Ayishaa!!!!

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRITahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon