Auren Sirri 13

142 15 7
                                    

🔐Auren Sirri🔐1️⃣3️⃣
Jiki a sanyaye su Ayisha suka dawo gida, kowa ya nufi dakin shi ba dan dayan su yasan abinda zaiyi ba idan yaje. Kusan wata awa guda ta sake shudewa kafin Mamy tayi ajiyar zucia a ranta tace zama haka bai ganni ba dole in motsa kwanji na gami da mikewa ta nufi dakin Ayisha.
Kwance take bisa gado kanta na kallon saman dakin babu tabbacin tunanin me takeyi, komai juya mata yake sai kalamai biyu da suke mata uawo a ka karuwa, haihuwa ba aure. Babu kuka a idon ta amma karku tona zuciyar ta wacce ke cunkushe babu abinda take bukata da ya wuce answers but the question is from who? Wata zuciyar tace mata Mamy, wata zuciyar tayi saurin ce mata Mamy fa itace wacce Ayisha zata iya yiwa komi a rayuwa, to taya Ayisha zata tunkari Mamy da zancan tana bukatar answers??
Mamy data ke kallon Ayisha ba tare da Ayishar tasan da shigowar Mamyn bama, can dai Mamy tayi ajiyar zucia kafin ta durkusa ta dafa Ayisha tace 'take it easy Ayisha na, tana shafa gashin ta taci gaba da cewa idan kin dauki komai da sauki sai kiga rayuwar ta maki sauki dan haka ki saurarawa kan ki kinji? Kamar kadangare Ayishar ta gyada kai alamun to sai kuma wasu dumammun hawaye suka zubo mata, ganin hakan da sauri Mamyn tabar dakin kafin itama ta zubar da nata, dakin Adnan ta nufa, shi kuma yana zaune ya hada kai da gwiwa da alamun shima maganganun dazu ne ke mashi yawo a kai.
Mamy ta zauna kusa dashi gami da dago kanshi tana smiling tana cewa haba Adnan akan abinda baku da tabbacin sa zaku zo ku daga hankalin ku nima ku daga nawa hankalin? Abinda kuke so kenan? Tayi alamar tausayi, Adnan dama akwai shagwaba sai kawai ya fashe da kuka yace amma Mamy kina ganin yanda suka ci mutuncin Sis har suna fadin wani magana, shshshs Mamy tace gami da kamo shi ta rungume tace komai zai wuce i promise,Adnan yayi murmushi yace let me go and check on my sis gami da ficewa.
**
Tun kafin Amal ta isa asibiti King ya fita hayyacin sa, kasancewar shi mai heart problem, cikin sauri akai ciki dashi doctors suka hau binciken gaggawa, Amal banda share gumi ba abinda takeyi cike take da tsoron me zai faru? Saboda harga Allah tana da tabbacin yanda ita da kanta tama manta da King yana da heart problem haka sauran en gidan su sun mata, lura da irin dogon lokacin da aka dauka babu abinda ya faru. Sai kaiwa da kawowa takeyi cike da tsanar Nadiya da Maaman ta sai kuma haushin Mummyn su da sauran en uwanta Amatullahi da Amira, ba zata iya cewa ga lokacin da aka dauka ba taji wata nurse ta dafa ta gami da cewa 'take is easy dear, he will be fine and you can go and see him gami da nuna mata dakin da yake.
Cikin sassarfa Amal ta shiga dakin can ta hangi dan uwan ta kamar babu rai, wani irin tsoro da firgici ya shige ta, kuka ya taho mata tayi saurin toshe bakin ta, tayi kuka harya ishe ta kafin ta mike ta nufi office din doctor din. Bayan ya bata izinin shiga ta bude ta shiga ta nemi wari ta zauna dafe kai take tambayar shi halin da King yake ciki? Yaja ajiyar zucia yace meyasa za'a rika masa abinda zai taba zuciyar sa alhalin kunsan rashin lafiyar sa? Kafin tace wani abu ya kada kai kasancewar shi bature wanda bai damu da abinda bai shafe shi ba, ya kada kai yace 'anyway he will be fine kuma zamu rike shi zuwa nan da 3 days haka muga yanda jikin nasa zai kasance, da wannan Amal ta mike ta koma dakin da King yake, ta jima tana kallon shi cikin tausayi kafin ta nemi zuwa gida.
A parlor ta iske su duka sai ma Daddy daya karu, amma ba maganar abinda ya faru suke ba da alamu basa so Daddy yasan meya faru amma shigar ta sai duk suka zuri mata idanu, kai tsaye wajen Daddyn ta nufa ba bata lokaci ta sanar mashi halin da ake ciki, sai gaba daya parlorn ya dauki kara maimakon Addu'a. Cikin hanzari Daddy ya fice ba tare daya bi takan kowa ba, itama dakin ta ta wuce bata bi ta kan su Mummy dake tambayar ta meya faru ciwon King ya tashi ba. Saida takai kafa saman stair case sana ta juyo tana kallon su tace abinda kuka hadu kuka hada kai kuka masa ne ya faru, kuma Mummy banyi tunanin son da kikewa Nadia ya wuce wanda kike dan da kika haifa da cikin ki ba, ita uwar Nadia ta san tabi abinda diyar ta ke so amma ke fa? Sai asibiti kika dangana naki dan, tana kawo wa nan ta haye sama da sauri saurin ta tabar su baki bude kowa da abinda yake sakawa a zucia.
**
Washe gari tunda safe su Mamy suka hau shirin tafiya Airport kasancewar jirgin afternoon ne, duk abinda Ayisha keyi King yana ranta, tayi ta kiran wayar shi amma bata samu sai a dangana ta da voice mail, ta kuma kira Amal itama bata samu ba, damuwar ta bata samu damar fada mashi tafiyar da zasuyi ba, saidai kafin su wuce airport saida ta nemi alfarmar Mamy akan ta fada mata inane kasar su da garin su saboda tana so ta barwa King message tunda bata samu damar masa sallama ba, Mamyn batai gardama ba kuma bata nuna alamun bacin rai ba tace mata Nigeria, a garin Kaduna. Da wannan Ayisha ta barwa King voice mail ta kuma sake rubuta text message ta tura mashi.
Kujerun su daya sai suka saka Mamy a tsakiya sakamakon data nemi ta zauna tsakiyar su, wata irin ajiyar zucia ba kakkautawa Mamyn ke saki hakan yasa duk suka bita da ido ba tare da sanin meya sata ajiyar zucia a jere haka ba. Saida ta lafa ta kalle su tayi murmushi tace 'nasan kallon meya sani ajiyar zucia yarana ke mani, to hankali na ne naji ya fara kwanciya yau zan koma kasata ta haihuwa bayan shekaru ishirin da daya. Tsulum Adnan yace Mamy meyasa ba zaki fada mana labarin ki ba? Ayisha ta anshe da cewa Mamy we're very sorry to say but we want answers. Mamyn ta kuma murmushi tace yanzu kuwa zaku samu dukkan answers din da kuke nema.
ASALIN LABARIN....

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now