Auren Sirri 31

180 17 5
                                    

🔐Auren sirri🔐 3️⃣1️⃣

Washe gari 'yan uwa da abokan arziki aka taru aka mika Ayisha gidan mijin ta bayan tasha kuka na rabuwa da Mamy, rabuwa da Mamy baya cikin lissafin Ayisha, tun haihuwa bata saba da wani ba idan ba Mamy ba, ita ce kawar ta,Aminiyar ta, abokiyar hirar ta kai itace komai nata, yanzu lokaci daya ace aure ya raba su ai dole ta sha kuka, to ita kanta Mamyn dauriya tayi banda haka tsaf zata iya yin kukan. Wajen azahar aka kai Ayisha sana aka zarce da walima a gidan, 'yan uwa sai saka albarka suke da fatan Allah Ya tsare ya kare ya kuma zaunar dasu lafia. Zuwa biyar na yamma kusan kowa ya koma gidan Abba inda a washe gari kowa zai koma inda ya fito.
Ayisha tasha gifts, Daddyn king ya aiko musu da motoci biyu ita daya king daya, dama Abba ma ya siya ma Ayisha tuni, iyayen Abba ne suka tura wasu masu aiki suka tsaftace gidan aka bi ko ina aka zuba turaren wuta da aka siya a wajen Majestic-fabrics, dan danan gida ya hau kam shi, king dai babu aboki ko daya sai Adnan ne ya rako shi bayan gama sallar magrib da niyyar ya juya da Amal su koma tare tunda bata iya maida kanta duk da a cikin anguwa daya ne, Amal kanta da kyar ta samu Ayisha ta sake mata rigar ta data rike wai dan Allah ta tsaya ta kwana nan, Amal tace babu ruwa na wannan daren yayana ne dan haka ku raya shi da aminci, tayi musu sallama da nufin zuwa safe idan gajiyar walimar ta sake ta zata zo musu yini tunda domin su tazo.
Sadda suka isa gidan sun tarar da bakin morocco Muhd kanin Mamy, Amal ta zauna tana fadin wash Mamy na gaji sosai, gami da gaida bakon sai kuma kamar an tsikare ta tace Mamy bara na wuce daki na kwanta, Mamy dai tana lura da yanda Muhd ya tsare Amal da ido wata kila shiyasa ta kasa zama, Amal na barin wajen Mamy ta daga gira tace wannan kallon da kake ma yarinya ta na meye? Babu kunya ko nauyin baki Muhd yace naga ni ina so Mamy ko zaki bani? Mamyn tace bana son wasa Muhd, yace wallahi Mamy da gaske nake ina bukatar karin aure saboda wani dalili na kuma ina don matar da zan aje anan Abuja, ita waccan bata son barin kaduna. Mamy tace idan kuwa ka samu Amal ina tabbatar maka ba zakayi nadama ba, Muhd ya matso kusa da Mamy yana cewa Mamyn mu kiyi mata talla ta mana, Mamy saboda daria kamar zata fadi, Abba daya shigo yace wannan dariyar yaushe rabon da inga Mamy nayin irin ta, da kyar Mamyn ta iya daina dariyar take fada mashi Muhd ne ke nema ayi tallar shi ga Amal ko zata amince, Abba yayi murmushi yace aikuwa na lura tana da hankali, Mamy tace sosai ma, Muhd ya sosa kai yace toki shigar dani idan an dace shikenan, bayan sun gaisa da Abba yake fada mashi yaje morocco bayanan saida ya dawo yake jin labarin auren Ayisha shiyasa ya kasa zama kaduna saida yazo, zuwan shi kenan Abuja ma, gobe in Allah Ya kaimu zan zo sai a rakani gidan inyi musu Allah Yasa alkhairi, Abba yace to babu damuwa.
Mamy bata ko bari gari ya waye ba a daren ta samu Amal ta fito daga wanka tana shafa mai, Mamy ta zauna ta amshi man tana cewa bari in taya ki da shafawa kafar ki da bayan ki, Amal cikin jin dadi tace akwai kuwa gajia tare dani amma duk da haka sai kace wata yarinya Mamy? Mamyn tace yaro har kullum yaro ne wajen iyayen sa kuma ki dauke ni mahaifiyar ki sai alakar mu tafi dadi, hawaye suka taru a idon Amal tayi saurin maidawa tayi murmushi tace nagode Mamy, Mamyn tana shafa ma Amal mai a baya ta shigo mata da zancan Muhd inda tace Amal kina da wanda kike so ki aura? Amal tayi shiru tana tuna duk masu cewa suna son ta yara ne da suke karatu tare kuma ta tabbatar inba wani ikon Allah ba da wuya su auri juna, Amal ta kada kai tace a'a Mamy ban fitar da kowa ba, Mamyn tace to kenan zan iya shigar da kani na Muhd wanda kika tarar a falo dazu, Amal ta sunkuyar da kai kasa tana murmushi, Mamy tace ya ganki duk ya rude shi yaga matar aure dan Allah in bashi, shine nace to zan gwada sa'a idan yana da farin jini zaki amince in baida shi kuma to... Hibba dake shigowa tace haba Mamy Muhd akwai farin jini na san Amal ba zata ki shi ba ko Amal? Hibba ta karashe maganar da tsokana tana kalloj Amal, ita dai Amal har a ranta maganar ma dadi take mata dan haka sai tayi ta musu murmushi, Mamy tace kodai murmushin amincewa ne wai? Hibba kuma tace naji yana fadawa Mamy gobe zaizo a kaishi wajen su Ayisha dan haka sai kuje tare daga nan sai ku fara fahimtar juna.
A bangaren ango da amarya kuwa abun baya ma faduwa, suna son junan su, suna marmarin junan su, suna bukatar dare irin na yau da suka kira da night to remember, sun manta da duk wani abu daya dame su a baya, da wasu mutane da suka tare wa soyayyar su hanya, sun rungumi junan su sun zama abu daya a cikin daren yau, sun kuma kara daura damarar son juna da kasancewa tare da juna.
Washe gari tun 11am Muhd ya bayyana gidan su Mamy, dashi akayi breakfast yana ta kokarin hango inda Amal zata fito har dai ya kasa hakuri ya tambaye ta, Hibba tace wai ni matar ka tasan kana da niyyar kara aure? Muhd yace ban taba yi mata alkawarin da ita daya zan zauna ba bare tace na saba mata kuma nasha fada mata ni mijin mace biyu ne, takan ce Allah Ya bata kishiyar da zata zame mata 'yar uwa ba wacce zata fitine taba da yaran ta, kuma tunda kuka yabi Amal to na tabbata ta kirki ce, Mamy tace gaskia ne, nasan yarinyar tun muna London, da ita da king sun fita zakka a gidan su, idqn harka samu auren ta bana jin zakayi nadama, anan ne Amal ta fito da nufin breakfast, da kyar ta iya gaida Muhd duk ya tsare ta da ido har saida Hibba tace wai kallon na meye? Muhd ya harare ta yana cewa Mamy ki shiga tsakani da yarinyar nan kamar bani ne gaba da ita ba amma duk tana nema ta rai na ni, wai zaman me takeyi ne ma? Ta tashi ta kwashi iyalin ta su wuce kaduna mana, Mamy na daria tace to kai ke auren ta ne? Mijin ta yana garin nan da alamun yana son dawowa nan shima karfi da yaji, yace sai gobe zasu wuce kaduna.
Amal dai ta samu ta tsakuri abinda zata iya ta mike tana cewa Mamy ina zan samu drivern ya kai ni gidan su Ayisha tun sassafe suke kira na inzo inzo wai kada kwanaki na su kare bamuyi wata hirar kirki ba nida nayi tunanin ma ba zasu samu lokaci na ba, Muhd yayi tsulum yace muje in kaiki nima can zanje, Mamy tace ku dawo lafia. A mota Muhd yana tayiwa Amal tambayoyi tana bashi amsa har dai ya fito ya fada mata manufar shi, babu wani boye boye ta nuna ta amince amma yanzu tana final exams dinta dan haka maganar aure da yake tayi ya hakura harta gama nan da one month, Muhd yace Allah Ya kaimu, nan sukai exchanging contacts. Muhd ya jima gidan su Ayisha kuma tuni suka saba da king, sukai sallar zuhr har kusa da asr kafin ya tashi ya musu sallama.
Bayan tafiyar shi ne king da Ayisha suke fadawa Amal sun yanke shawarar bin Amal Dubai suyi hutu acan har sun fadawa Daddy yasa a nema musu visa da ticket, Amal dan dadi kamar zatayi kuka, nan take fada musu yanda sukayi da Muhd, Ayisha cikin jin dadi tace Uncle Muhd yana da kirki kuma zaki ji dadin zama da shi amma ina fatan kinsan yana da wata matar? Amal tace duk ya fada mani kuma na amince musamman daya tabbatar mani bata son tashin hankali kuam ba gida daya zamu zauna ba.
Rayuwa tayiwa Ayisha da king dadi, basu da sauran damuwa sun ma manta da yanda damuwar take cikin kwanakin nan har zuwa sati daya sukai shirin barin kasar tare da Amal. Ana gobe zasu bar kasar Daddy ya isko su har Abuja ya samu Abba suka zo ziyara gidan Ayisha da King, Daddy yaji dadin ganin su lafia harya manta da batun Nadia dayayi niyyar yiwa king sai ma ya buge da cewa daga Dubai babu inda zasu je? King yace babu Daddy kawai dai muna so mu jira Amal ta gama exams dinta tunda ba zai wuce one month ba sai mu dawo gida tare, Daddy yayi gyaran murya yace kama tuna mani ina so inyi maganar Amal da Muhd da Alh Ahmad ya fada mani, Muhd din ya kira ni kuma shekaran jiya har Lagos yaje takanas dan ya gaishe ni kuma na tabbatar mashi dana bashi auren ta, tana dawowa za'ayi bikin amma nace zanyi shawara dakai inji, king yayi hanzarin cewa wannan yayi kyau ai Daddy ina bada goyon bayan hakan, Daddyn ya kalli Abba yace to kadaiji dan haka saika sanar mashi an bashi auren Amal, Abba yace to Alhamdulillah mungode Allah Ya saka da alkhairi, bayan sun masu sallama sun tafi ne kuma Mamy ta samu zuwa ganin gida dayi musu sallama, ta taho cike da abin alkhairin ta ga Amal wai tayi tsaraba, Amal kasancewar nan zata kwana gidan su Ayisha tayi ta godia, Mamy sai dare sana Abba ya dawo ya dauke ta ita da Adnan dake ta lissafi abinda za'a siyo mashi tsaraba.
Washe gari da king da Ayisha da Amal suka bi jirgin Emirate na yamma suka wuce Dubai yayin da suka manta da Nadia.
** **
Bangaren su Nadia kuwa tunda suka dawo daga wajen boka suke tunanin hanyar da zasu bi domin aiwatar da mugun nufin su. A ranar da suka rabu da Habiba a ranar saida ta kasa hakuri ta wuce gidan Mummy bayan sun gaisa ta fara tsumulmula tana so ta fadi abinda ya kawo sai kuma tana fasawa, Mummyn tace wai ni Habiba ba magana kike so kiyi bane ba? Habiban tace kwarai magana ce babba ta kawo ni gidan ki amma har kunyar idon ki make ta yanda zan fada maki, ta juya ta kalli Amira da Amatullahi dake zaune tace ko zasu bamu waje ne? Mummy tace Amira kuje dakin ku zamuyi magana da Habiba, bayan sun tafi ne Habiba ta zayyanewa Mummyn kaf abinda ya faru, ta karishe da cewa nauyi, kunya da sanin idan kece ba zaki aikata masu haka ba shiya kawo ni gidan ki dan kisan abinda ke faruwa kuma zaki tabbatar da magana ta idan kinga suna neman ki a waya, dan naji suna fadin ita Maman Nadiyar ta fara neman ki a waya ta nuna maki komai ya wuce daga nan Nadiyar zata zo nan da nufin ta kwana biyu, Mummy zufa sai yanko mata takeyi kamar wacce tayi workout, ta rasa kalma daya da zata furta sai ruwa take durawa cikin ta kafin taji cikin ya katsa ta nufi restroom a tsiyace ta zazzago abinda ke cikin ta, Mummy ta dawo gwiwa a sage tana ta share zufa, banda tafasa babu abinda zuciyar ta keyi, bata bar yanayin ba saiga kiran Maman Nadia ya shigo wayar ta, sai Habiba da Mummy suka hau kallon juna, Maman Nadia ta kira wayar Mummy yafi so shida amma Mummyn ta kasa dagawa, lallai biri yayi kama da mutum, wato duk yadda kake da mutum tsaf zai iya cin amanar ka, yanzu ita ai tayi tunanin tsakanin ta dasu Nadia sai godia da shi albarka irin fafutukar da tayi musu, ganin Mummy ta kasa magana yasa Habiba ta tattara handbag dinta tana cewa bi zan wuce Laurat amma kafin nan ina baki shawara daki rabu da mutanen nan domin babu imani a ran su, ni kai na na tuba bazan kara ba zanje gida inta Istigfari ina neman yafiyar Allah akan shirkar dana jima inayi kuma Alhamdulillah ni nama ji dadi da su Nadiyar suka zama silar gane abinda nake aikatawa haramun ne kuma zalunci ne, Habiba ta goge hawaye tace zanje in hakura da duk abinda Allah Ya dora mani, miji na kuma dana hana kara aure yanzu zan bashi damar karo wasu matan harya cike mu hudu idan yana da iko, Allah Ya yafe man abinda na aikata shima miji na zan nemi afuwar shi, ke ma ina baki shawara daki hankal ta ki gane cewa wacce yaron ki yake so mace ne ta gari ba wacce zata cutar da shi ba, ki bar shi ya mori rayuwar shi cikin aminci da soyayya, kada ki sashi yayi maki abinda kike so saboda karfin ke kika haife shi domin Allah Zaya tambaye ki akan hakan, abu na karshe koda wasa karmi bari su Nadia da uwar ta suzo maki gida domin zuwan su yana nufin aikata sharri ba alkhairi ba, daga haka Habiba tace na barki lafia sai naji daga gare ki.
Mummy ta zagaya toilet yakai so uku, bakin ta kuwa kamar ansa allura da zare an dinke, ta kasa magana gaba daya, hangowa kawai takeyi an maida mata yaro bawa kamar yanda uwar Nadia tayi ikirari, sai kuma ta hango Nadia na mulka king ta kuma hana shi tarayya da kowa, haka dai Mummy take ta wannan tunanin har Amira ta taba ta, Mummy tayi wata ajiyar zucia, Amatullahu tace lafia dai Mummy? Da kyar Mummyn ta iya sanar musu abinda Habiba ta sanar mata, suma dun sai sunai tsuru tsuru da su, can sai Mummy ta ja yo waya ta hau kiran layin king ba kakkautawa amma a kashe kuma taki hakura ta dena kiran nashi, a haka suka jiyo sallamar Daddy aiduk sai sukayi waje da gudu kamar wa'anda aka koro, Daddy ya tsaya yana kallon su yana hangen bayan su domin ganin abinda ya koro su.
Mummy ta zube kasa ta fasa mashi kuka tana cewa nabi Allah na bika Daddyn yara amma dan Allah ka taimake ni ka hada ni da Mu'azzam a waya inyi magana da shi.. Daddy ya katse ta da cewa baki da number shi ne? Mummy tace kullum na kira layin a kashe nake samu, Daddy yace hakan na nufin baya bukatar ji daga gare ki sai Daddy ya hankade ta zai wuce, sai Amira da Amatullahi suka zube suma suna kukan dan Allah Daddy ka saurari Mummy kaji abinda zata gaya maka, kamar zai wuce sai kuma ya kalli Mummy yace okay menene zaki gaya mani? Mummy bata iya boyewa Daddy komai ba daga karshe ta fashe da kuka tana cewa no ban sani bane ba ina gudun kada a mallake mani yaro ashe wa'anda nake tare dasu suke shirin mallake mani yaro, dan Allah Daddy kayiwa Allah da Annabi ka hada ni da shi inyi magana da shi, Daddy cikin tsananin fushi yace kice mashi mi? Ki gaya mashi batun abinda kika janyo mashi da kan ki ko kuwa umarni zaki bashi ya saki Nadiyar? To wallahi gara ma ki shiga hankalin ki dan na rantse da Allah idan kika furtawa Mu'azzam ya saki Nadia toki sani a bakin naki duka igiyoyin auren, dan ba zaki saka ni kunyar uban yarinyar nan ba Alh Abubakar, yana gani na da mutunci, kuma abinda kika nema ne yanzu saboda kin samu shiyasa kike turewa da hannun ki kuma? Mummy ta fashe da kuka tana cewa dan Allah Daddy kayi mani rai King ya rabu dasu tun kafin su sabauta mana shi, Daddy yace kindai ji abinda na gaya maki muddin kika sa king ya saki Nadia to a bakin naki igiyoyin auren kuma ko kinyi bayan ido na Allah Yana kallon ki, daga haka Daddy yana tsaki ga hankada Amira zai wuce sai kuma ya tsaya yace ku kuma kattin banza da wofi da ake hada baki daku ana aikata sharri na baku nan da wata daya ko waccen ku ta fiddo mijin aure idan baku fitar ba ni zan zaba maku kuma duk wacce tace bata amince ba to saidai tabar mani gida na dan na gaji da aje kattin mata a gida na suna haddasa mani fiti na, Daddy yaja tsaki ya wuce dakin shi.
Mummy, Amira da Amatullahi sai duk suka saka kuka aka rasa wanda zai lallashi wani har sukayi suka gaji suka mike. Tun daga ranar kullum sai Maman Nadia ta kira Mummy amma Mummyn bata dauka saima ta kashe wayar ta gaba daya, abinda ke damun ta ya ishe ta, nema take ido rufe ta samu tayi magana da king tasan shi kadai ne zai iya sakko da fushin Daddy, dan ya juya masu baya, ko gaisuwa da kyar yake amsawa kuma yana hararar su yake amsawa kamar wanda akaiwa dole.
Mummy da yaran ta cikin kwana uku suka fice hayyacin su ba cin kirki bare shan abin kirki yanda suka saba, ashe komai suna gare shi, har Daddyn da kanshi ya fara tausaya musu amma daya tuno irin abinda suka aikata sai yaji tsoron ka suga yayi saurin sauka ya zamana ba nadamar gaske sukayi ba, kuma koda wasa bai taba fadawa king ba bare Amal, kullum kuma sai sunyi waya musamman da king, ada Daddy yana niyyar yayiwa king maganar Nadia amma dayaji wannan batun sai ya fasa, amma har office ya samu baban Nadiyar kuma bai wani boye mashi komai ba ya sanar mashi king yayi tafiya kada aji shiru baizo wajen Nadiya ba, yayin da baban Nadiya ya sunkuyar da kai cikin kunya yace ina so inzo wajen ka amma nauyi da kunya sun hanani saboda abinda iyaki suke niyyar aikatawa, Baban Nadia ya sanarwa Daddy cewa shekaran jiya ya koma gida ya iske Nadia na kuka maman ta na bata hakuri tana rarrashin ta akan idan suka cika sharuddan boka to zasu samu abinda suke so dan haka ita tana yanke shawarar zuwa gidan su king tunda Mummy bata daukar wayar ta, Nadia tace Mama boka yace cikin sati biyu gashi yanzu mun kusa cinye sati daya shiyasa nake kuka kuma king baya Lagos ma, Maman tace duk inda yake binshi zakiyi daganan ki aikata abinda boka yace, aisai Laurat tayi nadama tayi kuka da idon ta. Nan dai Baban Nadia ya fadawa Daddy abinda zai iya fa da mashi dan wani baya faduwa ya karashe da fadin yanzu haka Adama na sake ta tun ranar kuma nace tabar man gida na, ita kuma Nadia na mata shegen duka kuma nasa ta dauko mani maganin da bokan ya basu na zubar dashi na kuma fada mata zan samu king din da kai na in bashi umarnin ya sake ta domin basu dace da juna ba.
Daddy yayi shiru kamar ruwa yaci shi daya rasa me zaice sai yace Allah Ya zaba abinda yafi alkhairi amma ni bazan cewa king ya saki Nadia ba, gara a bari harya tuba ta dena batun bokaye, Baban Nadia yace indai uwar ta na raye to ba zata bari ta dai na ba ni nasan wacece Adama dan haka ni zan nemi king da kai na in bashi umarnin sakin Nadia, Baban Nadia ya amshi number Ayisha dan Daddy yace king tunda yaje Abuja ya rufe layin shi idan za'ai magana da shi saidai a kira layin Ayisha.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now