Auren sirri 16

138 12 1
                                    

🔐Auren sirri🔐 1️⃣6️⃣

Soyayya mai tsabta ke gudana tsakanin Ahmad da Maryam amma a boye sakama kon Usman daya cewa Ahmad ya nemi da Maryam karta fadawa kowa batun soyayyar su tunda daga bangaren Ahmad da Usman din sun kasa samun mafita akan hakan, saboda shi dai Ahmad Allah yayi sa da son siyasa yana kuma da kudurin siyasa to amma yana so ya koma yayi masters din sa kafin ya dawo ya fara neman aure ma, sana kuma gefe guda akwai er uwar shi diyar kanin Maman sa dake son shi dan saboda Ahmad ne ma ta baro kano da zama ta dawo Abuja tunda taji batun dawowar shi Nigeria. Bama wannan ba dan shi yarinyar bata gaban sa shidai niyyar sa da kudurin sa na siyasa shine a gaban sa dan ko Maryam tsakani da Allah tayi wa rayuwar shi shigar bazata ne haka kuma bazai iya juya baya gare ta ba saboda jin da yakeyi duk siyasar da yake so idan babu Maryam to lami ne, yayin da a gefe guda yake tunanin mezai je ya dawo idan har a yanzu bai amincewa auren Maryam ba? Wannan dalilin ne yasa ya cewa maryam karda ta fadawa kowa batun soyayyar su, a gefen maryam tana matukar son ta fadawa iyayen ta da en uwan ta amma saboda yarinta dake cikin lamari da kuma tuno rokon da Ahmad ya mata sai kawai ta share batun fada masu, tabi son ran Ahmad.
Yau garin da dan zafi zafi ba laifi ga karatu da Maryam keyi kasancewar sun fara exams na gama karamar secondary, kadan kadan saita aje littafi tayi tsoki ciki ciki hardar Muhd ya gaji yace Yaya Maryam wai meke damun ki kike ta tsaki haka? Cikin kasa da murya tace wlh Muhd zafi zafi nake ji.. kafin ta idasa fada sai jin muryar malam isuhu dake shigowa dakin sukaji yana fadin tashi tashi maza muje waje mu duka musha iska haka kawai kunbi kun takura kanku kuda gidan ku? Inna Rahane tayi murmushi cikin dabara tace Malam daka barsu anan musamman maryam zata fi maida hankali cikin dakin tayi karatun a wajen akwai hayaniya zata dauke mata hankali, Malam isuhu yace kuma fa hakane Rahane to kuyi zaman ku kuyi hakuri wata rana sai labari kunji? Hibba ta daga kai gami da cewa baba ina yalon daka ce zaka siyo mana? Malam isuhu ya rike baki kasancewar shi mai barkwanci yace ahafff hibba aini na manta shaff amma bari in hanzarta in siyo maki, yana fita tsakar gida yaci karo da Inna Indo ita da Adamu suna sawo kai.
Bayan ya dakata sun gaisa wai babu kunyar Allah da Manzon Sa Inna Indo ta karkace baki ta nuna Adamu take neman fashewa da kuka duk dan dan uwanta yaji tausayin ta ya mata abinda ya kawo ta take fada masa Adamu ne ya saka ta a gaba babu ci babu sha ko baccin kirki ya kasa yi kullum baida magana saita Maryam shidai a aura mashi Maryam, shine nazo da kaina in fada maka Malam, ta karishe maganar ta tana share hawayen karya.
Malam Isuhu yayi shiru kamar ruwa ya ci shi, banda bugun goma goma babu abinda zuciyar shi keyi, yanzu yarinya karama mai cike da nutsuwa da Ilimi ita ake nema a kashewa rayuwa ta hanyar aurar da ita ga yaro irin Adamu? Ina ma Adamu rayuwar shi ba gurbatacciya bace ba? Dan shi talaucin Adamu ba zai dame shi ba tunda itama Maryam din cikin talaucin take sai rufin asirin Allah data fi shi kasancewar uwar ta na en saide saide, gyaran muryar Inna Fulera ne ya katsewa Malam Isuhu tunanin shi, cikin wani irin farin ciki Inna Fulera ta fara guda tana cewa wannan aure ai kamar anyi shi an gama ne ke Indo dan haka ki kwantar da hankalin ki kaima Adama ka kwantar da hankalin ka, tuwo na mai na za'ayi mu ashe muna da babban biki, bikin gida da gida ai dadi gare shi, Malam kuma uban ka kamar yarda yake uban Maryam kaga kuwa uba baya hana dan shi abinda yake so bare ma raya sunnar Ma'aiki, saita juya tana kwala kiran Fatsima ina kike keda yaran nan ku fito kuji abun alkhairin dake samuwa a gidan mu, sai kuwa suka hau fitowa. Inna Fatsima zani a hannu tsabar kaduwa wai neman auren Maryam, Yarinyar da ita ce karama cikin en matan gidan, to ita ina zata kai nata yaran kuma duka mata? Kamar Inna Fulera tasan abinda ke zuciyar Inna Fatsima sai kuwa ta kyafta mata ido harso biyu alamun kartai wata magana, ila kuwa sai Inna Fatsima ta ce to madalla da Adamun za'a yi ko? Kai murna har baka. Saida sukai kidan su sukai rawar su sana sukai shiru babu wanda yace musu ci kanku, sai Adamu dake ta washe baki kamar gonad auduga, ga hakoran nan duk sun mutu ido jawur alamun abinda yasha bai ida sakin shi ba ma.
Inna Indo ce ta dan motsa tace Malam banji kace wani abu ba har yanzu? Malam Isuhu ya nisa ya saki ajiyar zucia kafin ya iya cewa Indo kuje gida sai nayi shawara tukuna saboda bani kadai keda hakkin aurar da yarinyar nan ba, uwar ta na raye itama tana da abun fadi akan harkar yaran data haifa haka yarinyar kanta zanyi magana da ita inji ta bakin... sai kukan Inna Indi yaji yayin da Inna Fulera da Inna Fatsima suka hau sallallami da kururuwa suna cewa dama mun dade muna fadin Rahane tuni ta shanye Malam ta gama dashi sai abun da tace yakeyi yanzu gaya nan gaskiya tayi halin ta, Inna Indi cikin kukan munafurci take fadin yanzu Malam dan kaga babu ran iyayen mu shiyasa zaka nuna mani wariya? Yara na da naka ba duk daya bane dama a wajen ka? Ina laifin yaro kamar Adamu yace yana son Maryam? Minene abun shawara a ciki? Ba kai ne ka haifi Maryam ba? Zata sake magana kenan Malam Isuhu ya katse da dan Allah Indo ki tashi ki tafi gida ki dena wannan kukan, Maryam ce ai kena diyar ki ce dan haka a bari ta gama wannan karatun da takeyi sai asan abunyi dan yanzu suna tsaka da zana jarabawa ne, daga haka Malam Isuhu baiji ta bakin kowa ba yasa kai ya fice wajen Aminin sa kuma makwabcin sa Malam Iro, bai rage komai ba ya sanar wa Malam Iro abun da ake ciki.
Malam Iro ya nisa yace Malam Isuhu nida kai amana ce tsakanin mu babu zancan yaudara dan haka kai tsaye ina fada maka auran Adamu da yarinya kamar Maryam bai dace ba bashi cikin tsarin Addini, kuma diya taka ce duk da anan wajen ba iko ake so ka nuna ba to amma ana so ka nuna ikon wajen zabawa Maryam miji nagari da zai rike ta da amana cikin so da tausayi, daga haka suka shige masallaci.
A can gida kuma Adamu ya kasa hakuri sai washe baki yake gani yake kamar ma anyi auren su da Maryam angama tunda Malam Isuhu ba cewa yayi ba zai bashi ba, cewa yayi a bari ta karishe jarabawar ta dan haka Adamu ji yake kamar yau take salla har lumshe ido yake yana hango nesa kusa, baiyi sanya ba yasa kai dakin su Maryam inda ya iske su jigum jigum kowa hannu a fuska sunyi tagumi dan kaf abinda ya gudana suna ji. Adamu ya dage labule yana washe baki yana fadin ina amaryar tawa take ne, zo mana in dan ganki, idan bango dakin yayi magana to wani daga cikin dakin ya tanka mashi, ko miya zo ran shi? Oho sai ya juya yana cewa koda yaje nasan kunyata kike ji amma zan dawo da daddare zance, daga haka suka fice shi da Inna Indo wacce sauran matan Malam suka kara hura mata kai akan auran.
Bayan fitar su Inna Indo sai Inna Fulera tayi hanzarin yaficin Inna Fatsima da sauran yaran sukai dakin ta, tsabar farin ciki sai ta fashe da daria, duk suka bita da ido suna neman karin bayani, saida ta dara sosai sana ta fada masu manufar ta ai ba auran jin dadi Maryam zatayi da Adamu ba, shin sun manta ko wanene Adamu da shaye sheyen sa sun manta Adamu baida aikin yi sai zaman kashe wando? Ai su godewa Allah kawai dan dama burin su kada Maryam ta samu wani fitaccen miji to indai zata kare ga Adamu aisu gaba ta kaisu.
Inna Fatsima aka saki ajiyar zucia gami da cewa haba sai yanzu hankali na ya kwanta dan gaba daya zucia da ido na sun rufe na manta da aibun Adamu sai auren Maryam kawai nake hangowa, da wannan zancan nasu ya tsaya.
Karatun da Maryam bata karisa ba kenan, Allah Yaso ta ba soyayya kadai sukeyi da Ahmad ba a'a yana koya mata subjects da dama kawai dai karin haske ne tunda exams sukeyi. Inna Rahane taga shirun ba zai ba sai ta kaida shirun da cewa ku tashi muje muyi salla naji har an shiga masallaci ma, suma da wannan suka mike ba tare da dayan su ya tofa bakin shi cikin abunda ya wakana ba.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now