Auren Sirri 30

160 13 5
                                    

🔐Auren sirri🔐 3️⃣0️⃣
Washe garin ranar Mamy ta saka Hibba gaba tana mata fadan meyasa bataiwa mijin ta abinda yake so? Tana ganin ta kamar mai wayau ashe wayon banza ne? Ta inda Mamy ke shiga bata nan take fita ba daga karshe ta koma bata shawarwari akan rayuwar aure, Hibba ta goge hawayen da suka zubo mata tace Mamy gani nayi a WhatsApp ana ta gargadin iyaye akan su dena saka kaya matsatstsu ko suyi kissing, hug da makamantan su a gaban yaran su wai ance tanan ma yaran suna ganin hakan zai iya sawa suje su fara yi, to bare ni dake da mata... Mamy taja wani dogon tsaki tace Hibba ashe dai wayon naki bana gaske bane, ke yanzu har biyewa zakiyi dan kinga ana warning? Eh gaskia ne akwai abinda bai kamata iyaye nayi gaban yaran su ba, amma dan hug da light kiss ko ma ince peck da shigewa mijin ki duk zaki iyayi gaban yaran ki, dake da su duk ku taru ku like mashi musamman ma irin Usman dake son hakan, gashi kinyi sa'a mijin ki na son ki har yana korafi ma, nan dai Mamy tayi ta baiwa Hibba shawara ta karashe da fadin bawai kiyi ta dibgawa cikin ki kayan mata ba alhalin kin baro tushen ginin, dan zai zama kamar kin dandana mashi zuma ne a baki, da yawan maza suna son kulawa, Hibba dai da alama ta dauki shawarar Mamy tace In Sha Allahu zan gyara Mamy, Mamyn tayi murmushin tace yawwa Hibba na, yawwa wai ni ina Muhammadun mu ya shige kwana biyu? Hibba tace nima na neme shi a waya ban samu ba kila ki ya lula neman kudi, sukayi daria su duka suna fatan Allah Ya bada sa'a.
A guest Chalet Abba yace akai king ya kwana, kafin su san ta yanda zasu bullowa wajen zaman su dan baima san ko Lagos din zai ja Ayishan ba, da kyar king ya iya rabuwa da Ayisha, duk inda tasa kafa yana biye da ita har Alima kafin ta wuce nata gidan bayan zuwan mijin ta tana ta tsokanar king.
Washe gari wajen breakfast bayan an gaisa ne Abba yake tambayar shi meye shirin shi akan Ayisha? Abba yace nasan baka da plan akan ta saboda yanda abun yazo ba'a shirya ba amma kaje kayi tunani duk yanda ka yanke shawara ka sanar mani, King ya sosa kai yace Abba aini tun jiya mun gama yanke shawara zamu zauna anan Abuja kuma su Daddy ma kaduna zasu dawo da zama kaga zaifi mana kusa, Abba yace to hakan ma yayi, akwai gidajen da muke ginawa na siyarwa inaga kawai kuje ku duba ku zabi daya sai ayi furnishing saiku bar mana gida dan na lura ba kawaici ne daku ba, Ayisha ta dukar da kai cikin kunya yayin da king ya sosa kai yayi godia sosai, Abba yace babu damuwa aishi da ne wajen shi ko ba Ayisha ya aura ba domin sunyi zaman mutunci da amana a US sadda suna karatu da Daddyn shi kuma har yanzu suna tare sosai, Hibba tace wai amma dai za'ayi biki kafin su tare ko? Mamy tace babu wani bikin da za'ayi amma idan zasu tare za'ayi walima acan gidan nasu shikenan suje suyi ta hakuri da juna, Abba yace tunanin ki yayi kyau Mamy dan bason wannan taron bikin nake ba ayi kaca kaca da gida, Abba ya mike gami da cewa ina da Appointment kada na saba alkawari bari na wuce, akwai driver yana nan sai kusa ya kai ku saiku duba gidan, Adnan ya mike ganin suma sun mike yace aida ni za'aje in zabi nawa dakin, king yace kamar gaske zaka iya barin Mamy, sukai daria.
Gidajen anan cikin Maitaman ne suma saidai ta baya dasu Mamy ne, terrace ne gidajen, Suka yanke shawarar su zabi na farkon dake gefen dama, basu koma gida kai tsaye ba bayan sun gama sai suka shiga cikin gari cewar king baisan Abuja ba gara ya fara ganin gari dan gaskia nan din zaifi mashi zaman Lagos, Ayisha dai tana so ta tambayi king game da Nadia amma bata san me sakamakon tambayar zai haifar ba dan haka ta kama bakin ta tayi shiru, sai kusan la'asar suka koma gida suka tarar da Hibba da Usman na shirin wucewa kaduna, Hibba taja Ayisha daki ta nunnuna mata sauran kayan da tazo mata dasu yanda zata yi amfani dasu harsu kare, Ayisha tace to zatayi yanda tace, Hibba sukai sallama da nufin sai an saka ranar tarewar Ayisha sana su dawo.
Bayan Abba ya dawo gida ne ya samu kiran Daddyn king ya sanar mashi duk yanda sukayi har maganar gidan, Daddy yace ashe zaya raba hankalin shi ne biyu tunda ga Nadia anan Lagos ga kuma Ayisha anan Abuja, Abba yace nima dai nayi wannan tunanin kuma ina so in maka maganar aiki in hada da shi king din in nema masu ne idan lokaci yayi? Ita dai zata fara service ne, Daddyn yace hakan ma yayi Alhaji mun gode sosai Allah Ya saka da alkhairi, zan kira king din inji nawa ne yake ganin zasu ishe shi sai suyi furnishing gidan... Abba yayi hanzarin cewa haba haba Alh Ibrahim menene kuma wani kudi suyi furnishing gida, duk za'a hada ayi mudai fatan mu su zauna lafia, Daddy yace to naso ne inyi musu wani abun amma idan ka hana ba laifi sai in basu kudin sai suyi abinda duk suke so suyi, kuma babu wani biki da za'ayi tanan bangaren ku saboda dangin shi Mu'azzam din su samu halartar bikin? Abba yace gaskia babu amma idan aka gama gyaran gidan za'ayi walima ranar da zasu tare, Daddy yace to Allah Yasa alkhairi Allah Ya kaimu lokacin kuma muna kara godia na karramawar da akai mana Allah Ya fishshe mu kunyar ku, Abba yace amin.
**    **
Kwana daya biyu har sati babu king babu dalilin shi a Lagos, kullum banda kukan bakin ciki babu abinda Nadia keyi, wannan wane irin wulakanci ne a daura mata aure da mutum amma ya gudu ya tafi wani waje, wannan wane irin rashin so ne? Meyasa ba zata iya hakura da King ba? Wai mike gare shi data kasa hakura da shi? Duk ta fita hayyacin ta harta fara lalacewa, daman gata fara tass har wani ja ja fuskar ta keyi tsabar yawan kuka, ciwon kai kuwa harta fara sabawa da shi, tsakani da Allah Nadia tana son King ga wani azabar kishi da take ji idan ta tuna king din yana can wajen wata macen daba ita ba kuma Allah Kadai Yasan me suke aikata wa, da tayi wannan tunanin sai kuji wwuu ta kara fashewa da kuka, Maman ta kullum cikin bata hakuri take tana sanar mata Habiba tana nan zuwa Lagos kuma ta tabbatar mata da zata shiga zata fita sai ansa king yayi rabuwar wulakanci da su Ayisha, sai ya zama bawan ta, sai yanda tayi dashi danko iyayen shi saita bashi izini zaije ya duba su, ire iren wannan kalaman kullum suke fita bakin Maman Nadia, tun Nadiyar na yarda da hakan har dai dazu cikin tsananin fushi tace Mama kullum abinda kike fadi kenan amma babu daya da ya faru, banda azabar zafin zucia babu abinda nake ji, sai ta fashe da kuka, Maman ta kulu iya kuluwa tace toke uban wa yasa kika like mashi har uwar shi na cewa dan taga kene ke son king din shiyasa ma ta amince da auren ku, sai Maman Nadia ta quta alamun maganar har yanzu tana cin ranta, sai ma ta mike tace bari in kira Habiba inji yaushe ne ma tace zata zo.
Bayan sun gaisa ne Habiba ta baiwa Mama hakuri akan rashin zuwan ta tace mata yaron tane baya da lafia amma yanzu ya samu sauki dan haka anytime zata iya ganin ta tunda itama tana nan cikin Lagos din, Mama tace dan Allah Habiba ki hanzarta kizo kafin Nadia ta fita hayyacin ta, na rasa gane kanta da irin wanna jarababban son da takewa wanda baya son ta, ni kuma wallahi indai aikin bokayen nayi to zan kashe ko nawa ne domin samawa Nadia abinda take so kuma uwar shi saidai ta haifi wani, amma sai Nadia ta mallake shi kaf din shi, aidai abinda ta tsana kenan ko? To zata ga mallaka iya ganin idon ta, saita rai na kanta, sai ta tausaya mashi irin bakar azabar da zaisha wajen mu, bari dai ya shigo hannu, Habiba tace duk abinda kike so zaki samu wajen arnan kan dutsen nan dan babu Allah a ran su, ke dai ki jira zuwa na daga gobe zuwa jibi.
Bangaren Mummyn king kuwa itama kullum cikin bakin ciki musamman da kullum saita nemi wayar king amma a kashe, ga Daddy da alama ya juya mata baya banda gaisuwa ba abinda ke hada su saima wani daure fuska da yake dayaga alamun tana so ta mashi magana, Amira da Amatullahi ma sunga canji wajen Daddyn nasu dako harara baya masu a baya amma yanzu sai share su yakeyi, abin mamaki sai kaji shi yana kwasar daria a waya shida Amal dake Dubai, basu taba jin yana maganar king ba da alama a waje kafin ya shigo yake wayoyin shi da king din ko kuwa ya abin yake oho dai.
Mummy ta kulu iya kuluwa, ita da yaron ta data haifa da cikin ta amma tun yanzu an raba su, tayi kokarin kiran Maman Nadia amma kusan kwana uku kenan ta lura bata daukar wayar ta, Mummy tayi mamaki meyasa bata daga wayar ta? To amma itama cikin damuwar take sai kawai ta share ta tana neman mafita ita da Amira da Amatullahi.
Saida Habiba ta kara wani satin kafin ta samu isowa gidan su Nadia, ko ruwa bata sha ba Maman Nadia tasa ta gaba harda Nadiyar suka wuce daji, tafiyar kusan awa hudu sukayi a mota kafin suka samu isowa dajin, banda kwazazzabai babu komai sai manyan duwatsu, har iya inda motar zata iya tsawa sana suka fita sukaci gaba da tafiya da kafa, Nadia tun tana tafiya harta fara fadin wash wash saboda rashin sabo da tafiyar kasa, Habiba tace sannu ai anma kusa, tafiya kadan ta kaisu wajen katon dutsen, Habiba ta hau kirari 'sai lalatacce marar imani uban shegu wayaja da kai muce dashi ba shi ba, wanda ya sanka ya huta da bakin ciki wanda bai sanka ba ya kwana da bakin ciki, uban aljannu masu aikata aikin sharri'  daga cikin dutsen sukaji wata mahaukaciyar daria kafin sukaji kakkaurar muryar shi yana fadin aljannu sunji dadi wannan kirarin suna maku barka da zuwa, Habiba ta kutsa kai suna biye bayan ta.
Wani mummunan katon gardi ne, ga wasu kwanonin karfe gaban sa baje, kayan kirki wannan babu a jikin shi, lallai da alama babu Allah a ran wannan mutumin cewar Maman Nadia data nemi wuri ta tsuguna tana jin kamar ace mata kyat ta zuba a guje saboda tsoron mutumin ma ita takeyi, a rayuwar ta bata taba zuwa wajen bokaye ba kodan Baban Nadia ba mazauni bane bare ta samu matsalar da zata sa taje wajen bokayen ne? Bokan ya katse mata tunani da cewa ba'a zuwa nan ayi mana shiru kuyi maza ku fadi abinda ke tafe da ku, sai duk suka hau rawar baki amma sun kasa furta komai, da kyar Nadia ta iya cewa king nake so da duk tunanin shi ya dawo kai na ta yanda baya da ikon komai nashi sai abinda nace, uwar ta samu kwarin gwiwar cewar bayan haka so muke ko uwar shi karya kara ganin ta sai da izinin mu, ya zama bawan da baya da abin cewa sai na uban gidan sa, a fitar mashi da kowa na shi sai mu, idan da hali yama manta da Allah Yayi zubin wani nashi, Habiba dai mamaki ya cika ta, iya sanin ta da Mummy da Mama aminan juna ne, meyayi tsanani da Maman ke nema ta kassara Mummy haka? Anya kuwa idan nayi shiru ban fadawa Laurat wannan lamarin ba nayi mata adalci, kasancewar ita tayi introducing dina ga Adama ma.
Bokan ya katsewa Habiba tunanin ta da cewa kun samu abinda kuke so saidai sharuddan da zan gindaya masu tsauri ne, idan baku cika daya daga cikin su ba lallai asarar da zata biyo baya kuyi kuka da kan ku, na farko ku tabbata kunyi amfani da abinda zan baku yanzu kuma yanda nace, na biyu ku tabbata wani baigan ku ba sadda kuke aikatawa, abu na uku na karshe shine magani ne aljani zai bada kuje ku samu kayan shi mutumin ku bada masu wannan maganin sannan ku hure maganin ta yanda ba zai gani yace datti ya hau kayan ba bare yaki sakawa, sana ku tabbata ya saka kayan a jikin shi kafin awa ishirin da hudu su shude dasa maganin, idan kukayi haka toku tabbata sa'a taku ce, bokan ya tillo musu maganin yana mai cewa na gama da ku dan haka ku zube abinda ke jikkar ku sana ku bace man da gani, ina kuma kara gargadin ku da kada ku bari wani ya gan ku, sana lallai kuyi amfani da maganin kafin sati hudu, kuma lallai ya saka kayan, sabawa sharuddan nan yana nufin lalacewar lamurran ku, tuni Maman Nadia ta zazzage jikkar ta gami da sungumar maganin suka fito.
Bayan sun dawo wajen motar su ko maganar basu kara tadawa ba har suka isa gida kowa da tunanin da yakeyi, ita dai Habiba harga Allah jikin ta yayi sanyi tana kara tabbatarwa a ranta idan ta bari aka cuci Laurat to itama hakki zaibi ta, tana tuna Mummyn ce da kanta ta hada kawancen ta da Maman Nadia wani zuwa da tayi London, ita abinda yafi damun ta ma irin wannan bakin buri da Maman Nadiyar da ita kanta Nadiyar suka ci na raba king da iyayen shi ko ince kowa na shi, Habiba ta rika tunanin anya da sun koma kuwa ba zata wuce gidan Laurat ta fada mata abinda ke faruwa ba? Yayin da Nadia take tunanin wane shiri zatayi dan ta samu ta aiwatar da abinda boka yace ayi? Ta dai san shiga dakin king ba zai mata wahala ba tunda ko ada tana shiga amma yanzu idan taje gidan su king tace musu me? Bayan gabanta Mummy ke kiran Maman ta amma Maman nakin dauka? Yayin da bangaren Maman Nadia take tunanin gayacan anci nasara king ya zama bawan Nadia, a ranta tana dariyar mugunta yanda zasu wulakanta Mummy, aisai ta gane kuren ta badai tana ikirarin king baya son Nadia ba, ita Nadiyar ke son shi, zata gane kuren ta ne.
**
Cikin sati daya an gama shirya gidan su king, gidan yayi kyau sosai, ga kayan kirki an saka, kamar yanda Daddy yayi alkawari haka ya turawa king kudi masu yawa yace suyi wani abun dasu tunda Abba ya dauke musu dawainiyar komai, king din yayi godia kafin yace Daddy kana ganin su Mummy zasu samu halartar walimar da za'ayi jibi? Daddy yace king ka fita harkar Mummyn ku da en uwan ka, idan sun dawo daga rakiyar shaidan saiku daidai ta, daga can bangaren Daddy ya goge hawaye yace king kayi hakuri nima harda laifi na domin na sake ku sakaka kunayin abinda kuka ga dama, nafi maida hankali ga neman kudi a lokacin, ina ganin kamar idan mutum nada kudi to bashi da sauran damuwa yayin da na mance da batun mu musulmai ne kuma hausawa wata rana dole zamu dawo kasar mu cikin en uwan mu, yanzu ka duba ka gani Mummyn ku yaushe rabon ta da dangin ta? Bata ko yarda su rabe ta saboda basu da karfi, ka duba rayuwar Amatullahi da Amira basu da ko mashin shini na gaske sai en karya mayaudara, kai kanka ka duba rayuwar daka farayi kafin ka hadu da Ayisha data rika maidoka kan hanya, ni ai tsakani na da iyalan Alh Ahmad sai godia da addu'a da fatan gamawa lafia, ina nadamar sakacin da nayi na kuma rasa ta yanda zanbi in gyara.
King ma ya goge hawayen da suka zubo mashi, yace gaskia ne Daddy kuskure an aikata shi sai neman gafarar Allah kuma har yanzu lokaci bai kure ba, kuma Alhamdulillah daka gane kuskuren ka kake kuma tuba, Allah Mai karbar tuban bayinsa ne, itama Mummy zata gane hanyar data dauka ba mai bullewa bace, zasu gyara su duka ka dena damuwa Daddy kada wani ciwon ya same ka, kuma babu damuwa idan basu samu halarta ba, amma Daddy ina neman alfarma, Daddyn yace nasan me kake so dan ita er uwar taka ta riga ka neman wannan alfarmar kuma na amince kuma tuni na siya ma Amal din ticket zata iso gobe in Allah Ya kaimu, zatayi sati daya saita koma dan tace zasu fara final exams ne, ni ma daga baya zanzo inga gidan naku in kuma gaisa da maman ita Ayishan, King yayi godia mai yawa kafin suka aje wayar.
Washe gari wajen 12noon jirgin Emirate ya sauke su Amal kasancewar na asuba ne jirgin, Ayisha da King sai driver dake jansu suka isa Nmandi Azikwe International Airport domin tarar Amal, basu jima suna jira ba ta fito janye da traveling bag din ta, Ayisha da Amal suka rungume juna Amal din fadin Congratulations Ayisha ina murna sosai, Allah Ya baku zaman lafia, King da ya bi traveling bag din Amal kasa yana dauka ya dago yana cewa amin amin lil sis, Amal tayi shaking hannun King gami da sakar mashi hand bag din ta tana cewa wash nafa gaji dan haka komai ku zaku daukar mani, Ayisha tayi saurin ansar handbag din tana cewa king ai saidai ya rike akwatin kayan ki, ni kuma in rike dan karamin handbag din, sukai daria gami da karasawa wajen mota.
Kusan awa daya ya kaisu maitama gidan su Mamy da ya fara cika da en uwa da suka zo daga kaduna, Mamy ta tari Amal da hug tana mata sannu da zuwa, har dakin su Inna Fatsima da Inna Fulera da Inna Indo da yaran su Mamy ta kai Amal tana gabatar da ita matsayin kanwar King, sun tare ta da fara'a suna mata sannu da zuwa kafin Hibba ta janye ta zuwa dakin Ayisha, Amal dai taga kara da sanin mutuncin mutum har tayi sha'awar inama wannan ne familyn su, sai yamma Abba ya shigo shima har dakin Ayisha yaje da kanshi suka gaisa da Amal yana tambayar ta karatu, tace Alhamdulillah sun kusa fara final exams ma, Abban yace Masha Allah! Allah Ya taimaka Allah Ya bada sa'a, dukan su suka ce Ameen Ameen.
Da dare har gidan su Abba saida Ayisha ta kai Amal suka gaisa da kakannin Ayishan, suma sunji dadin zuwan Amal din suka tare ta da farin ciki ga karramawa kamar mutanen katsina, sai wajen goman dare suka koma gida domin ida shirye shiryen walimar saboda washe gari ne in Allah Ya kaimu. Amal ta samu kebewa da king a dakin Ayisha kasancewar babu kowa sai su yasa tace mashi brother yanzu daga family din mu ni kadai ce kenan? Babu wanda zai kuma zuwa? King ya furzar da huci yace hakan ne Amal, sukayi shiru su duka kafin Amal tace yanzu wai ya zakayi da Nadia dake Lagos? Cikin faduwar gaba king ya kalli Amal ba tare da yace komai ba, har ga Allah ya mance da Nadia da auren da aka daura musu, ya kalli Amal yace kinfi kowa sanin Nadia bata gabana dan haka me kike ganin ya dace ayi? Amal tace ka bari zamuyi maganar daga baya tunda any minute wani zai iya shigowa kuma ma abu ne dake bukatar nazari ba wai a yanke hukunci lokaci daya ba, tana kuwa rufe baki Hibba na kwankwasa kofar gami da shigowa tana cewa Amal kije side din Abba kuyi trying kayan da aka kawo maku idan da gyara sai tailor din ya koma ya gyara ya kawo da safe idan babu kuma shikenan, Amal ta mike tana cewa to Aunty Hibba.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now