Auren sirri 07

257 14 0
                                    

🔐 Auren sirri🔐 7️⃣

Washe gari bayan sun gama lecture suka samu waje suka zauna, dukkanin su babu wanda ya iya fara magana sukai shiru kamar wa'anda ruwa ya cinye. Ayisha ce ta fara jan ajiyar zucia sana ta kalli king tace 'king munzo mu duka don muyi magana amma kayi shiru, tell me what's wrong? Shima ajiyar zuciyar yayi kafin ya fara da 'Aishh na rasa ta inda zan fara ne amma abu daya dana sani shine duk ma ta inda zan fara dole a karshe sai na fada maki gaskia dan haka kiyi hakuri da duk abinda zaki ji na fada maki, ina so kisan gaskia ne tun kafin abun yafi karfi na ko kuma kiji ta wani hanyar bata wuri na ba, ya danyi shiru kafin yaci gaba da cewa ' Aissh this is the second time da nake degree.
Cikin mamaki Ayisha ta kalli king kafin tace meyasa baka taba fada mani ba? Ba tare da king ya ansa mata tambayar taba yaci gaba da fadin 'shekarun baya na taba katarin haduwa dake da Mamy da Adnan kunje super market, anan Allah Ya fara hada ni dake, kuma cikin ikon Allah sai naji kuna maganar course din da kika zaba yana da wahala, Mamy na fada maki ko zaki canja dai? Kikace a'a kina son course din kuma kina son Oxford University. A lokacin naso in maki magana sai karaf kuma naji Mamy na kara tuna maki warning dinda ta maki akan bata yarda dan zaki shiga university kiyi abokai maza da mata barkatai ba kuma lallai kafin ki fara abota  saikin sanar da ita da kuma wanda zaki fara dasu saikin kawo mata su ta gansu, har Adnan yana maku daria, jin hakan sai na fasa maki magana sai kawai tunanin inje neman degree a karo na biyu ya fado man a rai kuma lallai irin course dinki zan nema dan ya zamana ina ganin ki har Allah Ya taimakeni in samu soyayyar ki da naji ta shige ni farad daya. Neman admission baiman wahala ba ta hanyar Daddy, na fara karatu kuma rana ta farko na fara ganin ki saidai ban yarda na nuna maki na taba ganin ki ba saina nuna maki nima sabon dalibi ne, a haka har kika kaini wajen Mamy cikin satin mu na farko da fara karatu.
Daganan King yayi shiru, Ayishan ma tsabar mamaki sai ta kasa cewa komai. Shiru kusan 3mns King yaci gaba da cewa 'akwai labarin Nadiya daban taba fada maki ba saboda ban taba daukar ta da muhinmanci ba, king yaja ajiyar zucia ya hura iska da hanci kafin yaci gaba da cewa 'Nadiya tare mukai karatu da ita a Canada kuma kusan tare muka tashi da ita domin mamar ta kawar mummyn mu ce, aminan juna ne, Tun fara hankalin mu Nadiya ke furta tana so na saidai in mata daria kawai in dauka shirmen magana ne amma tafia ta Canada data tashi ganin yanda Nadiya ta tayar da hankalin ta wa iyayen ta ita lallai Canada itama zata bini muyi karatun a tare a lokacin na tabbatar da gaske Nadiya take batun tana so na amma still ban bada muhinmanci wa maganar ba, munje Canada mukai karatun mu kuma course daya muka karanta dan haka kusan koda yaushe muna tare da Nadiya har muka gama muka dawo gida a lokacin ta matsa da maganar muyi aure nidai ban taba nuna alamun yarda da maganar taba kuma ban taba mata wulakanci ba koda yaushe saidai in mata murmushi ko kuma ince ke Nadiya ki daina wasa da maganar aure a haka muke, data lura banda ranar amince mata saita samu maman ta da maganar auren, ita kuma mamanta ta samu mummy da maganar azo a mana aure hakanan nida Nadiya tunda har Nadiyar take maganar da kanta, mummy bata ja da nisa ba taiwa Daddy maganar shima kuma ya amince har suka kirani wani yammaci suje fadamin batun auren, nan take na fada masu ban amince ba saboda ban taba cewa ina son Nadiya ba, mummy ta fara fada sai Daddy ne yaita lallashi na akan na amince sai nace to naji na amince amma nima duk sadda na samu wacce nake so ba zasu hana ni auran ta ba, Daddy yace babu matsala, daga nan aka shirya maganar aure akai engagement da niyyar shekara mai kamawa za'ai auren amma shekarar bata kama ba Allah Ya hadani da ke wanda haduwar mu komai ya canja ta bangare na kuma shine dalilin kin amincewa auren ta hanyar komawa neman degree na biyu, shine har yanzu ba'ai auren ba. King ya juyo yana kallon Ayisha dan ganin yanayin da take ciki tunda baiji ta katse shi koso daya ba.
Bazai iya fahimtar yanayin da take ciki ba saboda fuskar ta bata nuna alamun bacin rai ba, yafi kama da fuskar mamaki dan haka bai mata magana ba sai yaci gaba da fadin 'duk gidan mu babu wanda yasan da batun ki sai guards da muke yawo tare amma day before yesterday na fadawa Mummyn mu maganar ki, king yayi shiru kafin ya hura hanci ya juyo yana fuskantar Ayisha kafin yaci gaba da cewa, Aishh basai na fada ba amma ke kanki a dan labarin nan daba baki da kuma sanin tarihi na dana iyaye na zaisa ki fahimci baza'ai maraba dake ba alhalin akwai maganar Nadiya, to hakan ne ya faru Mummy bata amince ba koda wasa amma hakan bai rage komai daga son da nake maki ba kuma a shirye nake da fuskan tar ko wani irin rayuwa a kanki, ba kuma zan iya auren wata ba ke ba wannan shine abunda na sani dan haka banji komai ba akan kin amincewar Mummy, kuma banyi magana da Daddy ba bare inji shi mai zaice.
Na yanke shawarar sanar dake duka abinda na fada maki saboda bansan mezai faru gaba ba kuma koba komai Aishh kinsan bana iya boye maki komai a rayuwa ta, a karshe Aishh ina son inji meye shawarar ki???
  Shiru na dan lokaci, zuwa can Ayisha taja ajiyar zucia ta maida kallon ta ga king daya kura mata ido kamar me neman sanin ainihin zuciyar ta, koda yake abunda yake bukata kenan sanin abinda ke zuciyar ta. Ayisha tayi gajeran murmushi kafin tace ' naji duka abinda ka fada king kuma abu biyu ne nake so na fada maka na farko banji dadi ba ta yanda ka kasa sanar dani duka wa'annan abun, a gefe daya kuma naji dadi daya kasance daga karshe dai ka sanar dani. Abu na biyu akan shawarar daka nema ne, King ina baka shawara dakayi wa iyayen ka biyayya da duk abinda suke so saboda nima idan nice a yanayin ka ina maka rantsuwa da Allah zanwa iyaye na biyayya in hakura da zabin zucia ta, King kai shaida ne yanda nike tsananin son Mamy a rayuwata, Wallahi idan yanzu Mamy zata fada mani ga Miji ta naso in aure shi zance mata to. Bazan taba mata rashin biyayya ba.
Idan baka manta ba ranar kaganni ina kuka a motar ka, shin king kasan saboda damuwar Mamy ne yasa nayi wannan kukan? Saboda naje shiga dakin ta naji ta tana ta kuka tana sunbatun maganar tayi nadama, a yafe mata, watannin nan bata da magana sai na in karashe school nan da 2 months mu koma kasar mu. King ya zaro idanu harda kwarewa yai saurin daukar ruwan dake gaban su ya tittila kafin yace 'dama ku ba 'yannan kasar bane Aishh? Ina ne kasar ku? Yaushe zaku tafi? Yanzu zaki iya tafia ki barni?
Ayisha tayi murmushi mai kama da yake tace muba 'yan kasar nan bane kuma bansan ina ne kasar mu ba amma Mamy tace kasar mu nada nisa, kuma bansan sadda zamu tafi ba abu daya dana sani shine muna kammala exams mamy tace zamu tafi ni da ita da Adnan, kuma king aibance zan bar ka ba, baga waya ba, ka kwantar da hankalin ka mana. A daidai lokacin kiran sallar Asr ya fara a wayar Ayisha dan haka bata jira jin komai daga bakin king ba ta mike gami da cewa kaga har lokacin salla yayi bamu lura ba, nasan kuma mamy nacan na jira na a Office kafin mu wuce gida. King ma ya mike jiki a sanyaye kamar wanda kwai ya fashewa suka jero zuwa wajen motar su king, yau ma shiya sauke ta Office din mamy kafin ya wuce nasu gidan a inda ya tarar da Nadiya baje tsakar falo suna hira ana daria da sisters dinshi da mummyn shi da maman su Nadiya, lokacin nan daya ga Nadiya sai yaji wani bakin ciki ya rufe shi ganin kamar basu lura ya shigo ba ya nemi juyawa saidai baisani ba akan idon Maman Nadiya, sai jin muryar ta yayi 'King daga shigowa sai juyawa yau kuma? Da alamun wasa tayi maganar shiyasa ya kakaro murmushi yace....

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now