Auren Sirri 28

124 13 5
                                    

🔐Auren sirri🔐 2️⃣8️⃣
Sai da King yayi sati uku sana aka fara samun kanshi, sai kuma rashin magana ya biyo baya, baya um baya uhum har gara Amal yana kulata amma itama idan babu kowa ne, Amal kullum cikin mamaki take dalilin da yasa King har yau bai taba yin maganar Ayisha ba, ita kuma ta kasa yi mashi maganar, to ko dai akwai abinda ke ran shi? Rashin mai amsa mata ne yasa ta zubar da tunanin hakan ma a ran ta, Nadia da Maman ta kullum cikin sintirin zuwa suke duba shi, hatta mahaifin Nadiya yazo duba jikin king kusan so hudu.
Saida ya cika wata daya sana akai discharging din shi, Mummy har cikin ran ta taji dadin da king baiyi maganar Ayisha ba dan ita har yau tana kan bakar ta, yau kwana uku kenan da sallamar king kuma jikin shi yayi kyau sosai wanda ba'ayi zaton hakan ba at first, yana zaune shi da Amal a dakin shi kamar daga sama ya jefo mata tambayar meyasa Ayisha bata zo duba shi a hospital ba? Bata san ya kwanta bane ba? Ko bata huce ba akan abinda ya faru a school? Amal cikin ran ta tace shikenan karya ta kare bori ya kashe boka, ta kalle shi sosai cikin ido da ido tace king kayi hakuri Ayisha bata da laifi, nima kuma bana da laifi domin nayi iya bakin kokari na akan in samu Ayisha amma na kasa samun ta, tun kana asibiti da kwana biyu naje gidan su domin in sanar mata saboda na kasa samun ta a waya, Amal tayi shiru ta gaza idasa fada mashi abinda tayi niyya, har saida king yace ina jin ki lil sis, hakanan ta daure ta mike ta dauko mashi sakon farar takardar da Ayisha ta bar mashi ta mika mashi sana tace mashi kamar yanda na fara baka hakuri to yanzu ma hakurin zan kara baka domin Ayisha ta jima da yin nisa, washe garin ranar da aka ci mutuncin ta a school suka bar kasar nan zuwa kasar su abinda na iya samun labari kenan daga Neighbour din su da sukayi masu sallama, na san idan ka karanta sakon Ayisha zaka iya samun karin bayani, daga haka Amal tayi hanzarin barin dakin king dan ma kada taga halin da zai shiga.
King yafi minti ishirin baiyi ko motsin kirki ba, baima san tunanin me yake ba, a haka daga karshe dai ya bude takardar Ayisha, hakuri ne ta bashi ta kuma kara jaddada irin son da take mashi, ta kuma roke alfarmar ya auri wacce iyayen shi ke so ya aura inyaso daga baya sai ya aure ta ita ta amince, sana kuma zatayi zaman jiran shi duk tsayin lokacin da zai dauka har yazo ya same ta, ta mashi fatan alkhairi ta kuma fada mashi idan ya tashi neman ta ya tura mata email musamman da number shi zatayi gaggawar kiran shi, daga karshe ta kara gode masa akan son ta da yake yi. King ya karanta takardar yafi so a kirga, tunowa da Ayisha da yayi wata rana yaje mata da complain akan Mummyn su ranshi a mugun bace, saita ce mashi yayi ta maimaita InnaLillahi wa'inna Ilaihiraji'un, tuno hakan da yayi yasa yanzu ma ya hau fadar InnaLillahi wa'inna Ilaihiraji'un, bai bar gurin ba har saida yaji ya samu nutsuwa sosai a ran shi.
Da dare King ya shigo cikin gidan ya gaishe da iyayen nashi dake zaune a falo, Daddy yace yawwa king dama ina jiran a sallame ka inga ka samu nutsuwar zuciya data jiki sana in baka damar auren duk macan da kake so, tunda dai Allah Bai hana ba nima bazan hana ba dan haka kaje ka zo man da duk yarinyar da kake so ni mahaifin ka zan shige maka gaba domin ganin ka aure ta, Mummy harda shakewa wajen tayi magana saboda bala'i, Daddy ya daga mata hannu yace lallai kika ja da wannan al'amarin ran ki bazai so ba dan haka kiyi man shiru, ya maida duban shi ga king yana mai sauraron abinda zai fada, king din yace nagode daddy Allah Ya saka da  alkhairi kuma batun auren Nadia a gaskia bana son ta Daddy amma idan kace in aure ta zan aure ta, Daddyn yace naji dadin jin hakan daga gare ka kuma ina neman alfarmar indai auren nata bazai zame maka wata irin takura babba ba to kayi hakuri ka cika alkawari ka aure ta, daga baya sai ka auri duk wacce kake so kamar yanda na taba yi maka alkawari nima zan cika maka naka alkawarin, Mummy banda harare harare babu abinda takeyi sauki daya da aka samu jin king yace ya amince da auren shi da Nadia, a ran Mummy tace ayi dai auren tukuna daga baya duk ma ta halin yayane za'ayi domin ganin auren Ayisha bai tabbata ba. Bayan King ya koma dakin sa ya jawo laptop dinsa ya turawa Ayisha sako ta email din ta ya kuma tura mata number shi kamar yarda ta bukata cikin takardar ta, yayi ta zaman jiran ganin reply ko kiran waya amma har garin Allah Ya waye shiru kakeji.
Albishir din aure da Mummy tayiwa Mama da Nadia ya tsananin faranta ran su kamar wa'anda aka bawa Aljanna, suka fadawa Baban Nadia aure fa ya taso yaushe ne zasu koma gida tunda an tsaida shawarar komawar gida. Cikin kankanin aka shirya komawa gida Nageria daga ko wane bangaren, Amal dai ba'a koma da ita ba domin hutun ta ya kare ta wuce Dubai cike da jimamin sabon halin da king ya tsirawa kansa na shiru da rike waya da laptop duk inda zaka ganshi to zaka ganshi ne da laptop da wayar sa yana sauraren ji daga Ayisha wacce kullum a rana sai ya tura mata sako yafi goma amma ko so daya baiji daga gare ta ba hakan kuma baisa gobe ya ki tura wani sakon ba.
** **
A Lagos suka sauka gaba dayan ahalin biyu, tun daga London suka fara sanarwa mutanen su da en uwa batun auren King da Nadia dan haka wasu en uwan na kusa kusa ma tuni suka sauka a Lagos din suna tsumayin bakin, sati biyu da dawowar su aka fara shagalin biki, koda wasa king bai taba halartar partyn da aka shirya ba, har ranar daurin aure. Usman mijin Hibba kanwar Mamy kuma abokin Ahmd da shi kanshi Baban Ayisha wato Abba (Ahmad) suna daga cikin mutanen mahaifin King kasancewar su abokan karatu kuma basu yarda juna ba akan gaisa musamman ma yanzu da kasuwanci yake dan hadasu, Abba yaja Adnan suka hadu su uku suka nufi Lagos halartar daurin aure.
Babu yanda ba'ayi ba da king ya shirya yaje daurin auren amma yaki har saida Daddy ya shigo yana fadan meyasa zai gayyato mutane saboda daurin auren shi kuma ya wulakanta shi haka? Wato abokan shi basa da darajar da zai nuna musu yaron nashi da yake aurar wa? Meyasa ya amince da auren idan yasan hakan zata faru? King ya bashi hakuri gami da masa alkawarin ya bashi minti ishirin zai fito a shirye. Kamar yanda ya fada kuwa cikin mintina kalilan ya shirya ya tarar da mahaifin nasa anan suka hadu suka wuce a can anguwar su Nadia tunda a gidan su za'a daura auren, kusan a tare su king suka isa wajen da motar su Abba, Adnan da Usman. Adnan ya murtsike idanu ya kara gogewa wai ko idanun shine basu nuna mashi gaskia ba, amma king din daya sani ne dai cikin manyan kayan da suka sauya halittar sa ya koma wani kyakykyawan matashi mai cike da kamala.
Adnan ya fisge hannun shi daga cikin na Abba ya ruga a guje cikin taron mutanen ya cakume king ta baya, jin rikon da akama king ne ya juyo da shi shima idanun shi cikin na Adnan sai shima ya kasa gasgata abinda yake gani kafin shima yayiwa Adnan wata tsatstsauran runguma, tambayar shi yake ina Ayisha? Tana ina Adnan? Komi Adnan ya tuna sai kuma yayi hanzarin kwace jikin shi ya kwasa a guje wajen Abba yayin da King yake tsoron kada Adnan ya bace ma ganin shi sai shima ya rufa ma Adnan baya da gudu sai kuma kallo ya koma kan su. Adnan yana isa wajen su Abba ya hau jan rigar shi yana cewa Abbba Abba mu tafi mu koma gida sune suka ci mutuncin Sister a school din su, Abba mu tafi kawai. Abba cewa yake Adnan calm down and talk to me, what are u saying? Sai karaf king ya cafke hannun Adnan cewa yakeyi wallahi ba zaka guje mani ba Adnan sai ka kaini ga Ayisha, nasha wuya har bansan yanda zan fada ba kuma har yau zucia ta bata taba hutawa da tunanin inda zanga Ayisha ba, Daddyn king daya karaso cikin hanzari yake kama hannun king yana cewa kai Mu'azzam mike damun ka? Meke tsakanin ka da yaron Alhaji Ahmad? Maza sake mashi hannu muje muyi abinda ya kawo mu, da alamun king baima san abinda mahaifin nashi ke fadaba, Ayishan kadai ke fita daga bakin shi.
Ganin idanun tsiraran mutanen da suka gayyata yasa Baban Nadia da shima yake wajen ya nemi dasu shiga daga cikin gida sai ayi magana saboda ga idanun mutane anan, Adnan yana jan hannun Abba yana fadar Abba mu tafi gida bazan zauna nan ba, yayin da King ma yake jan dayan hannun Adnan yana fadar wallahi babu inda zaka saika kai ni ga Ayisha, Mahaifin King kuma sai zufa yake sharewa yana fadar mu'azzam ka saki hannun yaron mutane mana, amma king da alamun baima san mahaifin nasa na magana ba.
Bangaren Alh Abubakar Manga wato mahaifin Nadia suka nufa, a babban falon shi suka zauna anan ya nemi jin ba'a sin abinda ke faruwa, karaf king yace Daddy kace duk ranar dana tashi in maka maganar wacce nake so zaka nema mani, ya nuna Adnan yace wannan kanin wacce nake so ne Ayisha kuma bansan inda take ba ina ta wahalar neman ta sai gashi Allah Ya hadani da Adnan kuma wallahi babu inda zayaje saiya nuna mani inda take saiji kake kikiki yana jan Adnan, adnan daya fara jin zafin jan da king ke mashi sai ya nemi ya fara kuka, in takaice maku da kyar aka samu king ya sassautawa adnan tsaurin rikon daya masa amma duk da haka yaki sakin shi, Usman yace nifa bawai na fahimci abinda ke faruwa bane ba sosai ya maida duban shi ga Adnan yace kai Adnan maza fada mana abinda ke faruwa. Adnan bai boye musu komai ba na dan abinda ya sani tarayyar Ayisha da King har cin mutuncin da aka mata a school saida ya fada, King yayi hanzarin cewa Wallahi Wallahi tun ranar ban kara lafia ba kuma ni baza'a hada baki dani aci mutuncin Ayisha ba balle mahaifiyar ta, ran Baban Nadia ya baci jin abinda matar shi da Nadiyar suka aikata sai ma wata kunya ta nemi rufe shi duk da son da yake wa Nadia baiyi zaton zata iya wulakanta mutum haka ba domin basa yi gaban shi ko alama basa nunawa. Shima Daddyn ran shi ya baci sosai jin abinda matar tashi tayi har baisan sanda yacewa Abba yayi mashi alfarma ya baiwa king auren Ayisha sai yaga tsiyar abinda zata iya tsinanawa idan zata iya hana ikon Allah. Abba dai ya fahimci wannan shine king din da mamy ta bashi labari kwanakin baya game da Ayisha dan haka yaja Usman gefe yayi mashi bayani a takaice sai suka yanke shawarar su kira mamy da iyayen mamyn da iyayen abban su sanar dasu. Malam mahaifin Mamyn suka fara kira kuma nan take yace ni lamarin aure yana bani tsoro kuma tunda akwai waliyyai da shedu kuma yarinyar nan kai keda iko da ita amma duk da haka ka kira ni domin ka nemi shawarar mu dan haka ina baka shawara daka daura auren anan inda kuke, bidi'a dama ba tamu bace daga haka sukai sallama da Malam. Mahaifan Abban ma sun goyi bayan abinda Malam ya shawarce shi yayin da Mamy ce last person daya kira ya mata bayani cikin dan lokaci ya kuma karashe da fada mata shawarar Malam da kuma goyon bayan iyayen shi sai Mamyn ma tace Alhamdulillah! Lallai Allah Ne ya amsa mana addu'ar mu Abba dan haka nima bazan ja da ikon Allah ba, ka daura mata auren Allah Yasa albarka a ciki.
Abba da Usman suka dawo tsakiyar falon suka fadawa Daddyn king sun amince da auren king da Ayishan a hada tare da na Nadiyar, haka kuwa akayi aka fara daura auren Nadia da King sana aka daura da Ayisha da king, cewa yake mi zanyi in godewa Allah da wannan rana? Adnan ya tsinano baki yace kayiwa Allah godia, king yace wace iri Adnan? Adnan yace kayi sujjada shukriya, tun kafin ya karasa fada tuni king yakai goshi kasa, yana dagowa ya rarumi waya ya bugawa er uwar shi mai son farin cikin shi, Amal ta dauka daga can bangaren tana tsumayin king cikin kunan rai ya fada mata an gama daura auren shi da Nadia sai taji sabanin tunanin ta, cewa yake er uwa ki tayani murna ashe alheri ne ya kawo mu Nigeria an daura aure na da Ayisha, Amal dai da kyar ta samu king ya natsu yayi mata dan bayanin da zai iya saura kuma yace sai daga baya yanzu yana so yabi iyayen Ayisha zuwa Abuja ne saima ya kashe wayar gaba daya.
Tuni labarin daurin auren Ayisha da King ya isa cikin gidan su Nadia da suka tara en gayun mutanen su suma ba dika ba domin acewar su bikin en gayu ba'a tara barkatan mutane bare ma basu jima da dawowa kasar ba, Alima da mahaifiyar ta da suka samu ziyartar bikin Nadia kasancewar su first cousins, suka jiyo ihun Nadia daga dakin ta aida gudu suka kwasa a tunanin su ma wani mugun abun ne ya faru, Nadia cewa take na shiga uku na lalace ni Nadia yau wacce irin bakar rana ce maimakon ta zame mani ta farin ciki saita juye ta bakin ciki? Maman ta data kariso ta kama jan Nadiya tana fadin tashi maza mu shiga cikin daki sai mu nemi abinyi amma a yanzu kuka baya yi, da kyar Aunty Halima maman Alima da Maman Nadiya suka tura Nadiyar a daki, anan ne Maman Nadia ke fadawa maman alima abinda ya faru da kuma wacce abin ya faru, ita dai Alima sai godia ga Allah ta saki cewa take ai kuwa Mu'azzam yayi mata ga kyawun hali ga kyawun sura, saiji kake kaf kaf Aunty Halima ta kwashe ta da mari ta kuma hauta da bala'i yanzu dan uban ki Alima ace maki anyi wa er uwar ki kishiya right after an daura mata aure amma kizo kina murna? Kuma ma har wacce aka daura auren da ita kinji amma dan kinfi son su a kan mu shine kike murna? To tashi dan uban ki bama son zuwan naki maza jeki bi iyayen Ayishan ki tafi wajen su ai dama kinzo har gida kin fada mani kin gano su, sadaf sadaf Alima taja hannun yaron ta daya hau kuka jin hayaniya suka bar dakin, wayar Abban ta kira yana dauka ta sanar mashi idan basu tafi ba su jira ta gatanan fitowa su wuce tare, bai wani tsaya tambayar ta ko nuna mamaki ba jin yanayin muryar ta ya amsa mata da cewa to ta fito yanzu bada jimawa zasu tafi airport ba.
Alima dai ko sallama bata yi musu ba ta dauki akwatin kayan ta dana yaron ta ta fito waje inda ta hadu da adnan yayi saurin karbar akwatin ta ya saka a boot, sana ta bude mota ta shiga ta zauna tana zaman jiran su, king ne ya dage akan zai bi su Abuja ana rokon sa ya zauna yana rantsuwar kafar su kafar shi amma yau babu mai raba shi da Ayisha, Daddy yace Alh Ahmad ku wuce da shi kawai daga baya zamuyi magana yanda za'ayi na tarewar Ayishan saboda tuni ita Nadiya an shirya wajen zaman ta anan Lagos, Abba yace to shikenan babu damuwa sai munyi magana, daga haka suka shiga mota suka wuce airport, a cikin motar ne Alima ke fada masu abinda ya faru a gida da korar da sukai mata sai kuma ta gangaro kan cewa da fa har zan kira mamy ince ta tura man Ayisha muje biki tare amma dana tuna lokacin baya a Italy sai na fasa to ashe ma rabon angon ma ya zama namu ne, haka dai sukai ta fira har suka isa airport, gashi koda wasa Alima bata bar king ya huta ba sai tsokanar shi take har saida tasa ya fara daria.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIDove le storie prendono vita. Scoprilo ora