Auren Sirri 23

126 15 6
                                    

🔐Auren sirri 🔐 2️⃣3️⃣

Ganin Mamy ta kasa gane inane gidan su sai Ayisha tace Mamy me zai hana muyi tambaya ko za'a samu wanda ya sani? Bala yace wlh nima abinda ke rai na kenan, bai jira komai ba ya fice daga motar da niyyar ya tambayi wasu samari da suke gefen su suna hira, bai jima ba ya dawo yana susa kai yace Hajia aina manta ban tambaye ki inane zance muna nema ba, saida naje ina tambayar su na tuna banma san inda ake neman ba, Mamy cikin sanyin jiki tace ka tambayesu gidan Malam Isuhu idan basu gane ba kace musu mijin Inna Fulere da Inna Fatsima da Inna Rahane.
Wannan karon ma balan bai jima ba ya dawo yana washe baki da alamun nasara yace Hajia sunce ga gidan nan mai masallacin nan, cikin sauri mamy ta juya tana kallon gidan, mamaki cike a ranta saboda ganin gidan ya canja gaba dayan shi da alamun wadata ta ziyarci gidan nesa ba kusa ba, sai kuma mamyn ta kasa fitowa daga mota har saida Adnan da suka rigata fita daga motar ya bude side din da take ya jawo hannun ta dake rawa cikin taushin lafazi yace take it easy mamy, Allah Ya riga da Ya rubuta duk abunda zai faru dan haka ki samu nutsuwa mu shiga, daga haka ta daga kafa sukai ciki bala na biye dasu da traveling bags. Ayisha ce tayi sallama cikin hausar ta mai kama da wani yaren tunda sunfi ganewa turanci kusan kowa shi yake musu, mamy ce bata musu magana saida hausa shiyasa ma suka iya amma da sunyi magana mutum yake gane ba tashin cikin hausawa bane.
Wata dattijuwar mata dake kokarin shiga daki ta dan dakata tana ansa sallamar Ayishan cikin fara'a tana mata lale marhabin, Ayishan ma fara'ar takeyi kafin ta tambayi matar da cewa 'dan Allah ai nanne gidan Malam Isuhu ko? Bata jira amsawar matar ba taci gaba da cewa munyi tambaya a waje aka nuna mana nan ance nan ne, adnan da mamy suka shigo gaba daya cikin gidan, daga dattijuwar matar har mamy sai sukai cirko cirko, hausawa na cewa kowa ya bar gida gida ya barshi, wannan haka yake domin wata irin tsigar jikin mamy da matar ke tashi a lokaci daya alamun sun shaida juna kafin mamy kamar karamar yarinya ta kwace hannun ta dake cikin na adnan ta ruga izuwa ga matar tayi mata wata irin zazzafar runguma kafin kuka ya biyo baya, ita kuka matar ma kuka sai su Ayisha sukai cirko cirko suna kallan su yayinda bala ke shigowa da akwatunan su a ranshi yana ayyana ko kukan me sukeyi ko kuwa sun jima basu hadu bane? Koda yaje ga alama nan tunda jiya hajiya ta fada mani ta jima rabon ta da nan, sana da muka zo nan ma saida muka tambayi gidan, shi daya yake maganar shi a ran shi.
Malam Isuhu jin kuka saiya fito daga daki yana cewa 'Rahane daga fita daki na ki dauko sako sai kuma in jiyo kukan ki, anya Rahane ba zaki sassautawa kanki kukan nan... sai Malam Isuhu yayi shiru ganin wacce ke rungume da Rahanen da yakewa magana, lallai ko shekara nawa yayi baiga maryamun shi ba to idan ya ganta ba zai gaza gane ta ba, sai hawaye shima tsabar dadi, sai kuma yai gaggawar tsugunnawa a inda yake yakai goshi kasa yana sujjadar shukriya. Yana dagowa yaji maryam shima ta cakume shi har yanzu kukan dai takeyi, malam isuhu ya riketa gam yana murmushi ya kasa cewa komai, Inna Rahane ce tayi kokarin tsaida kukan ta tace cikin tsokana malam yanzu ka gama maganar yawan kukan da nakeyi gashi kaima yau idanu na sun nuna man kukan da kayi shekaru kana boyewa, bata jira cewar shi ba ta juya kan su Ayisha ta na musu iso zuwa dakin ta. Saida duk suka shiga aka hau gaisuwa kafin mamy ta durkushe kasa tana wani sabon kukan tana neman afuwar su, malam isuhu yayi saurin cewa tayi maza ta mike ta zauna su basu rike ta da komai ba tunda komai mukaddari ne daga Allah. Inna Rahane tace wannan gaskia ne dan nima da farko irin mugun fushin dana dauka nayi mamakin shi amma kafin aje ko ina na dena fushi na koma addu'ar Allah Ya bayyanar mana da ke ta karishe fadi tana goge wani guntun hawaye.
Bala daya shigo da jikkar karshe ya sosa kai yace hajia na gama, mamy tayi hanzarin bude jikka ta kwaso kudin da bata san yawan su ba tunda ba kirgawa tayi ba ta mikawa adnan tace maza ka mikawa bala, bala jiki na rawa ya hau godia, mamy tayi murmushi tace babu komai bala kayi man komai tunda ka kawo ni kaduna kuma zanyi saving number ka saboda gaba, balan yace babu damuwa hajia nizan juya, Inna Rahane tace kai kuwa bawan Allah baka bari ko karin kumallo kayi? Bala ya sosa kai yace a'a akwai inda zan biya idan naje zanyi acan, a haka ya musu sallama ya tafi cikin jin dadi.
Bayan tafiyar bala ne mamy ta gabatar da Ayisha da Adnan ga tsofaffin iyayen nata, Inna Rahane ta kamo hannun adnan cikin wasa tana cewa to malam gafa sabon miji nayi, malam daya ruko hannun Ayisha yace nima ga tawa sabuwar matar sai yaya kuma? Gaba daya sukai daria duk da su adnan din ba wai sun fahimcin wasan da kakannin nasu ke masu bane sosai. Mamy ta kalli Inna Rahane tace 'Inna ya naji gidan shiru babu kowa ina mutanen gidan suka tafi? Inna Rahane tace sunje zaria duba  Fatu (diyar rikon inna fulera) bata ji dadi ba, mamy tace ayyah Allah Ya bata lafia, gaba daya suka ce amin.
Inna Rahane sai shiga ake ana kawo abinci yau dai duk wanda zai ganta yasan cike take da tsananin farin ciki, Malam Isuhu kanshi ya kasa fita kasuwar da suke zuwa shida aminin shi malam Iro, dan koda ya biyo mashi su tafi saiya fita ya fada masa yau Allah Ya dawo musu da maryam dan haka babu inda zashi, Malam Iro har ciki ya shigo suka gaisa da mamy yana mai nuna jin dadin dawowar ta kafin ya mike yana cewa bari ya turo iyalan shi suyi mata sannu da zuwa, kafin kace me? Tuni labari ya baza anguwar maryam diyar malam isuhu Allah Ya mata dawowa ta dawo da wasu turawan yara, hatta wa'anda basu san maryam ba sai kaji labarin maryam ta dawo. Mutane da yawa suna ta shiga suna gaida ta saboda zaman mutunci da ake da iyayen ta, a haka tilon kanwar ta mace wato Hibba ta fado gidan cikin gigicewa tana fadin ina yaya maryam din take? Sora kadan ta bangaje inna rahane wajen cakumar mamy, suka rungume juna cikin tsananin kewar juna, kukan mamy dai ashe bai kare ba dan saiga wani sabon kukan, musamman da Muhd ma ya fado cikin irin nashi saurin, shima dai rungumar ne yayi mata idon shi yayi ja sosai babu kuka. Bayan sun natsa ne suka koma kan ayisha da adnan wa'anda suketa receiving sabon soyayya daga kakannin su da iyayen su hibba da muhd.
A gaskia duk wanda yaga iyalin nan yasan suna cike da jin dadi da farin ciki, banda sadaka babu abinda ake fitarwa daga gidan har dare ya raba kuma babu mutanen gidan wato basu samu dawowa ba to ko labarin dawowar maryam baije masu bane ba? Oho dai. Sai bayan Isha'i ne Inna Indo ta fado gidan kamar wacce aka jeho tana fadin yanzu ace maryam ta dawo gidannan tun tuni amma a rasa wanda zaije ya fado man sai a gari ne nake jin labarin dawowar ta ta? Inna Rahane tayi murmushi tace kiyi hakuri Indo banyi wannan azancin ba, kafin Inna Indon ta kuma magana mamy ta fito daga kuryar daki tana gaishe ta, ai sai inna indo ta hau murza idanu kafin ta fara shafa mamy tana fadin ikon mai sama yanzu maryam kece kika zama haka kamar a taba jini ya fito? Mamy tayi murmushi tace nice inna, nan dai aka hau sabuwar gaisuwa kafin inna indo ta fashe da kuka tana neman afuwar maryam din tana kuma cewa wallahi na jima dayin nadamar halaye na yar nan, dan Allah ki yafe mani kinji, mamy ta riko hannun inna indo cikin mamakin meya canja inna indo haka? Tace babu komai inna, ni ya kamata in roke ku gafara tunda na bar gida bada izinin ku ba, dan Allah ki tayani baiwa su malam hakuri duk da sunce sun yafe mani, inna indi ta anshe da cewa kedai bari maryam rayuwa sai a hankali kuma sai daga baya na fahimci lallai nayi rayuwa bisa doron karya, murya kamar zatai kuka Inna Indo tace Allah na tuba ka yafe mani bazan gaji da neman yafiyar ka ba gami da goge hawayen da suka fara zubo mata.
Inna Indo ta jima kafin ta bar gidan gami da cewa zata dawo gobe taji labarin maryam din, bayan tafiyar ta malam isuhu yake cewa hibba da muhd su tashi su koma wajen iyalan su amma kiri kiri daga hibban har muhd din suka make kafada kamar yara harda hada bakin wajen cewa su nan da sati daya ma basu ga mai raba su da yar uwar su da yaran su ba, mamy ta goyi bayan su gami da cewa gaskia nima ban gaji da ganin en kanni na ba da suka girma ba tare dana ga girman nasu ba gashi har sun aje iyali, inna rahane tayi gyaran murya tace aiko ni tsohuwa bazan bada goyon bayan su tafi ba sai munji labarin abinda ya faru dake duk da muna da wani daga cikin labarin, mamy ta kalli inna rahane cikin mamakin jin cewa wai suna da labarin wani abun game da ita amma dai bata nuna ba ta hau basu labarin abinda ya faru tun daga farko har zuwa yau da suka dawo gida.
Bayan ta gama ne ta kuma kara neman afuwar su danji take kamar har yanzu bata nemi afuwar tasu ba ma, malam isuhu ne ya tabbatar mata da sun yafe mata tun tuni shi dama bai rike ta da komai ba, inna rahane ce tayi mugun fushi shi kuma ya biye mata saboda ya samu ya lallashe ta kafin maryam a sallame ta daga asibiti sai ya dauko ta su dawo gida. Ayisha da adnan sai hamma suke alamun gajiya, hakan yasa malam yace to kowa yaje ya kwanta gobe in Allah Ya kaimu ma wata ranar ce sai a dasa daga inda suka tsaya, mamy tayi gaeran daria tace saboda nima kuwa gaf nake da tambayar canjin dana gani masu yawa, daga haka suka mike, muhd da adnan sukai dakin malam yayin da inna rahane da en matan ta da kuma sabuwar jikanyar ta suka kwana a nata dakin, wajen baccin ma mamy bata yarda ta raba gado da inna rahane ba, kamar yarinya haka ta nanuke mata yayin da innan tsabar farin ciki baisa taji wata kunya ba. Hibba da ayisha a gado daya suma har bacci yai gaba dasu.
Washe gari bayan sun yi wanka sun shirya sunyi kalaci sai suka sake haduwa anan falon inna rahane, mamy dai ta kasa hakuri ta sake tambaya abinda ya faru bayan barin ta gida.
**
Muhd ne yayi daria yake fada mata cewar ranar da suka barta asibiti shi ya fahimci komai amma saboda har lokacin ba wani shekaru ko girma gare shi ba yasa bai iya magana ba kuma ganin malam ya biyewa inna rahane sai shina ya kasa cewa komai amma lallai a ranshi yasan akwai yarda akai wanda bazai iya cewa ga yanda akayi din ba tunda kwakwalwar shi ba zata iya hasaso mashi wani abu ba amma abu daya daya sani shine lallai yayar shi ba zata taba kai kanta inda zata wulakanta kanta da iyayen ta dasu kansu kannan ta ba, dan haka daga nan sai kawai na rika bin duk wacce kukai school tare wacce nasan na taba ganin ku tare kuma nasan gidan su har Allah Ya kaini gidan su Asiya, asiyar tlbata boye mani ba cewar yau satin ku biyar kenan da barin kaduna kinsa an nema maki wajen aiki har Lagos kuma abin Allah agent din bata sake zuwa gidan su asiya ba tun rabar data bar gidan su tare dake.
Yayin da a gida kullum su inna Fulera da inna fatsima har da inna indo suke zubawa inna rahane habaici wai taje ta boye maryam dan kada ta auri adamu to duk inda ta kaita taje ta fiddo ta dan aure tabbas ba fashi, abun yaki ci yaki cinyewa saboda inna rahane bata taba kula su ba dan a lokacin ita fushin da takeyi dake ma isheta abin bakin ciki bare harta kara wa kanta da damuwar su inna fulera dan haka saita baiwa banza ajiyar su.
Har akai sati basu san me ake ciki ba tunda ba shirin arziki ake dasu ba bare har a fada musu abinda ke faruwa, amma a sati na biyu ne inna fulera tayi labe a dakin malam a inda ta tsinkayi malam na lallashin inna rahane akan ta hakura yaje ya dawo da maryam ai kaddara ce kuma tana kan kowa kuma ya kamata a tambayi ta yanda akai ta samu cikin jikin nata... sai ihun Inna Fulera sukaji suka fito a sukwane suka tarar da ita tana zuba ihu tana fadin an janyo masu abun kunya anyi cikin shege a gidan su, tuni ta tara yaran gidan da inna fatsima gami da adamu daya shigo a lokacin, kafin kace me tuni anguwa ta bazu akan maryam ta gudu saboda tayi cikin shege, kowa da abinda yake fadi amma dai magana daya ce maryam tayi cikin shege, wannan abu ya kara dugunzuma Inna Rahane ta kara yin wani irin fushi, kullum cikin fushi take, yayin da Malam ke kokarin saukar da fushin nata har ta gamu da ciwon hawan jini saboda yawan tunani...

Mrs sS❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now