Auren sirri 04

376 19 0
                                    

🔐 Auren sirri 🔐 4️⃣

Washe gari kamar yanda king yai alkawari haka ya cika shi, da yamma yazo ya dauki Ayisha da Adnan zuwa park da shopping, yawancin shopping din duk Adnan ne ke tsintar abinda yake so.
King ya lura kamar Ayisha na cikin tunani sakamakon yawan shirun ta, sai yayi kamar ya tambaye ta saiya fasa har dai ya kasa hakuri yace 'babe what is the matter'? Murmushin da baikai zuci ba Ayisha tayi kafin tace 'nothing'. Badan king ya yarda ba sai dan bai son ya matsa mata shiyasa ya kyale ta.
Sunyi yawo kam ba laifi cikin birnin na London, Adnan kuma ya jidi kaya sosai, kusan magrib king ya mayar dasu gida.
Bayan fitar Adnan, king ya dubi Ayisha yace 'sorry babe, amma ni nasan akwai abinda ke damun ki wanda baki so ki sanar min kuma ni ina ganin kamar mun zama daya babu wani boyo tsakanin mu amma sai ina ganin ba haka ba wajen ki, bazan boye maki ba Aishh banji dadi ba kuma a haka zan tafi gida cikin rashin dadin, ya dan numfasa yaga ko zatai magana amma shiru kamar bada ita yake ba sai binshi da kallo da takeyi, ganin haka cikin rashin kuzari king ya nisa kafin yace shikenan Aishh kina ina tafiya gida nima zan wuce.
Hawayen da Ayisha ke kokarin boyewa sukai fitar ba zata sai kawai ta ida rushewa da kuka, idan hankalin king yakai duba to duka ya tashi, baiyi aune ba shima yaji idanun shi sun cika da hawaye saidai jarumta irin ta maza yasa bai zubar da hawayen ba sai kunar zucia gashi ya rasa mema zaiyi.
Kusan minti uku Ayisha na kuka yayin da zuciyar king ke nata kukan zuccin wanda ya daskarar dashi saboda tunda yake rayuwar shi daya san Ayisha kullum da smiling yake ganin ta, idan baiyi karya ba to zaice bai taba katarin ganin koda bacin fuska ne gun Ayisha ba sai idan ya taba mata hannu nanne kadai zaiga canjin fuska amma daga bashi ba tsayin shekarun da yai da ita bai taba ganin wani yanayi na damuwa ko bacin rai ba gun Ayisha to amma yau dinnan meyai zafi? Me aka mata? Kuka dungurugum?
Da kyar king yayi ta maza ya fara neman kalamin lallashi, cikin sanyin jiki yake magana 'Aishh idan na maki complain akan halin 'yan gidan mu kece mai yawan gaya mani inyi hakuri wata rana sai labari, kullum kece mai sanyayar da zucia ta, ban kuma taba ganin ki cikin wani yanayi marar dadi ba idan ba yanzu ba, Aishh idan ba nima kuka kike so na fara ba tona roke ki da girman Allah kiyi shiru ki daina zubar min da hawayen ki dan Allah Aishh.
Duniya kaf Ayisha bata ga abinda wani zai hada ta da Allah ta kasa yin abinda aka hada ta da Allah domin shi ba, dan haka yanzu ma cak kukan ya tsaya kamar anyi ruwa an dauke, sai ajiyar zucia da takeyi. King ya mika hannun shi ya zari tissue dake cikin motar gami da mika mata, sanin me yake nufi yasa ta ansa ta goge fuskar ta tsaf kamar batai kuka ba sai dai idanun da suke farare tass yanzu sunyi jaa sakamakon kukan da tayi. King ya kuma dauko ruwan roba da ya taho dasu da suka je shopping, ya mika mata ruwan bayan ya balle hancin robar, bata ki ba tasha ruwan amma ba sosai ba, muryar ta bata fita sosai tace thank u king, murmushi yai mata gami da cewa ki shiga gida lokacin salla zai wuce , gobe kuma muna da lecture so zamu hadu school.
Fuskar Ayisha ta nuna jin dadin rashin tambayar ta dalilin kukan ta saboda itama murmushi tayi wanda yake na ainahi bana yake ba gami da cewa thank u once again for your understanding. Sana ta bude motar tana mashi bye bye ta wuce gida.
King ya kusa minti biyar cikin rashin sanin abinyi kafin ya samu ya tada motar ya wuce gida, kasancewar bai fito da masu tsaron shi da mahaifinsa yasa suke tafia dashi ba duk da shi baya so amma baida yanda zaiyi inji mahaifin nashi. Wannan kenan

Mrs sS ❤️ ✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now