Auren Sirri 22

127 16 3
                                    

🔐Auren sirri🔐 2️⃣2️⃣
Matsala ta farko da maryam ta fara samu a zaman ta itace zuwan yayar anty gidan wato anty adama, takanas tazo wajen kanwar ta halima saboda wani kasuwanci da antyn tayiwa yayar ta tayin shi. Anty adama Allah Yasa tana da masifar saka ido ga wulakanci da tsanar talaka kamar su sukai kansu a talakawan, zuwan ta ta kulla aminci da neighbor din anty halima wato laurat wacce yaran ke kira da mummy, kusan halin mummy da anty adama daya wajen kyamar talakawa da wulakanci. Mummy nada yara hudu ciki harda er karamar dako arba'in dinta basui ba amma a haka mummyn ke baro su tazo gidan mu ta hadu da anty adama suyi ta bala'in hira ana bata wuri ana kira na ina gyara wa, a haka wata rana mummy ta kyalla ido ta gano cikin jiki na wanda a lokacin ya kai wata biyar, kai ranar nan naga cin mutunci da wulakanci da kira na karuwa, babu irin wulakancin da basui man ba, ranar har anty halima saida suka kirawo ta dawo gida a sukwane ta hau buguna suna tambayata uban da ya mani ciki, kamar daga sama sukaji Abba yace 'nine uban cikin da kuke tuhumar ta akai' ai duk sai suka bishi da ido inda anan rigimar anty halima ta koma kanshi.
Tun daga ranar ban kara jin dadin gidan ba, kuma sai anty halima ta rage fita sai su hadu su uku suna gana mani azaba, a haka wata rana Abba ya rutsa su aikuwa sunga mugun bacin ranshi nan yayi rantsuwa akan duk wacce ta sake gana mani azaba sai kotu ce zata raba su sana ita halima idan ta kara to a bakin auran ta, wannan ne ya sama mani salama suka dena azabtar dani suka koma habaici da kira na karuwa.
Watan anty adama biyu kafin ta tattara ta koma gida Nigeria saboda ta baro diyar ta da mijin ta, a kuma watan ne su mummy laurat suka bar Italy da zama ban san inda suka koma ba bare rayuwar da tayi bayan nan saifa da muka hadu a school din ku tazo a matsayin maman king, ita da anty adama maman nadia.
**
Bayan wata biyar na haife diya ta sak mai kama da uban ta sai abinda ba'a rasa ba da ta dauko nawa, Abba yayi hidima damu kamar diyar shi ta cikin shi, tsakani da Allah yake son diya ta daya baiwa suna Aisha yasa mata Ayisha, dashi da alima sai in rasa waya fi son ayisha, kyakykyawan jego nayi cikin jin dadin kulawar mutum irin Abba, yayin da na baiwa anty halima baya ita da zafafan kalaman ta dan kullum ne da sabon cin mutuncin da zata mani har conference call take hadawa ta kuma saka speaker ita da su mummy laurat da anty adama amma sai idan taga abba baya nan.
Bayan wata biyu da haihuwar Ayisha ne abba ya samo mani school na koma.
Bayan shekara hudu tsakani Abba ya bijiro mani da batun aure na, girman sa da mutuncin sa da karamcin sa suka sa na amince, aka daura mana aure wanda sai bayan anyi ne anty halima ta sani, ai kuwa daga ni har shi saida mukaji dama bamuyi auren ba amma tunda an riga da anyi sai kawai muka barwa banza ajiyar ta, kullum da sabon cin mutuncin da suke bijiro mani dashi duk kuwa da anty adama da mummy laurat basu nan amma maganganun su har cikin kunne na da gangan anty halima ke zuwa da wayar ta waje na ta saka speaker suna zagi na saidai inyi kamar banji su ba.
Na shiga university da karamin ciki na wato cikin adnan, abba kamar ba'a taba masa haihuwa ba saboda yanda ya hana kanshi sakat saboda cikin adnan, tun bayan haihuwar ayisha ya bude mani account dani da ayishan duk wata yake saka mana kudade masu yawa har zuwa sadda na haife adnan, ya saka mashi sunan shi wato Ahmad, in yaso ya tsokane shi yakan ce Ahmad dan Ahmad, nida alima saidai muyi daria wacce a lokacin ta zama matashiyar budurwa, gaba daya halin ta ba irin na uwarta bane, sunsha banban, kaf halayen alima na mahaifinta ne.
Ayisha nada shekara shida Adnan nada shekara biyu, rayuwar mu saidai muce Alhamdulillah dan gaskia bana da wata damuwa tunda tuni na aje damuwar anty halima gefe, abu daya dake ciman tuwo a kwarya bai wuce abinda nayi wa iyaye na ba shikam babu rana ta Allah da zata fito ta koma banyi kukan hakan ba, gashi harna kuma yin aure na biyu na sake haihuwa amma shima basu sani ba, banda Allah babu wanda ya sani sai Abba kadai yasan wannan damuwar tawa, kullum cikin bani hakuri yakeyi yana fada man wata rana komai zai wuce da ikon Allah ko baya raye zance dama ya fada mani.
Mutum mai karamci da sanin hakkin dan adam sai Abba, da ni da Ayisha da Adnan haka yake dankara mana kudi a account din mu mu duka ba tare daya damu ba, idan nayi magana sai yace ai bansan me gobe zata haifar ba, saidai kawai in masa godia. Adnan nada 3 years yayin da Ayisha keda 7, Abba ya kwanta ciwon ciki na yini daya washe gari ranar juma'a ya rasu. Nayi kuka nayi kukan da bansan yawan shi ba, nayi rashi babba, yarana sunyi rashin uba managarci, haka alima tayi rashin uba na hakika. Ko arba'in Abba baiyi da rasuwa ba Anty halima ta tattara kaf abinda yake dashi ta gudu Nigeria ita da Alima, ranar ma muna zaune da alima tana shiryawa adnan, anty ta fado daki ta hau jan alima, alimar na kira na ina kiran ta a haka anty ta janye alima suka bar gidan, wanda har yau ban kara jin duriyar su ba. A zaton Anty halima zani tagayyara ne bayan ta kwashe komai harta gidan da muke ashe ta siyar, washe gari sai ga masu gida sunzo sun bani notice na one week in bar gidan.
Duk da ina da kudade hakan bai hanani kuka sosai ba saboda tuno Abba da nayi, cikin satin daya na nema mana visa muka bar Italy muka koma London da zama, nayi hidimar komai da kudaden da Abba yake tura mana duk wata, na nemi karamin flat na kama haya muke zaune, banyi shekara daya ba na samu aiki a wani company, na nemi school na saka ku. A lokacin sai rayuwa ta ta canja gaba daya na maida kai na babu kawa ko daya sai yara na, haka kuma na saka ido sosai akan yara na kamar yanda mahaifiyar mu tayi akan mu, duk ilimin dana iya na addini babu wanda ban koya ma yara na ba sai ma wata makarantar addinin dana kuma saka su a haka mukai ta rayuwar mu har zuwa yau da muke cikin jirgi zamu koma kasar mu ta haihuwa wato Nigeria.
**
Mamy na kawo wa nan a karshen labarin ta saita goge wasu hawaye da suka zubo mata saboda tuno iyayen ta da kuma Abba da tayi, Ayisha ta rungume Mamy tana kuka a hankali ita da Adnan, Mamyn ta janye jikin ta ta dauko wata jikka ta bude ta zari hotuna tana baiwa kowannan su, ta baiwa Ayisha pictures din da suka dauka ita da Ahmad ranar da ta gama jss exam dinta, yayin da ta baiwa Adnan hoton da suka dauka ranar da akai sunan shi da mamy da abba da alima da ayisha duk suna daria.
Kusan mintuna goma kafin Ayisha tace Mamy ashe sunan baba daya ke gare mu nida Adnan shiyasa muke bearing da second name iri daya, Mamyn tace eh, shiyasa wannan yazo man cikin sauki. Adnan yace yanzu Mamy zama ki iya gane gidan ku? Mamyn tayi shiru, can dai ta nisa tace Adnan ban sani ba tuku na sai idan munje, nidai fatana in tarar da iyaye na da ransu dan in samu in nemi gafarar su.
Ayisha ta jehowa Mamy tambaya da cewa Mamy kenan anty Adama, mummy laurat da anty halima duk basu san cewa Abba bashi ne baba na ba ko? Mamy tace basu sani ba da farko amma daga baya sun sani daga bakin Alima saboda ta sani, sai adnan kuma yace in hakane meyasa a school dinsu Yaya Ayisha suka kira ta da karuwa harda ke? Mamyn ta furzar da huci tace me yiyuwa har yanzu basu manta da abinda ya faru ba, koma dai menene damuwar su ce nidai fatana kada Ayisha ta maimaita kuskuren da na aikata wanda har yau na kasa samun farin cikin zucia saboda hakan, Ayishan tayi murmushi tace Mamy koda ada ina da wannan niyyar to a yanzu da kika bani labarin ki niyyar ta fasu dan haka ki kwantar da hankalin ki bazan taba aikatawa ba da izinin Allah.
Haka sukai ta hira har suka sauka saman filin jirgin Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja. Mamy koda ta shaki iskar kasar ta datai missing sama da shekara ishirin saiga wasu hawaye masu zafi, a ranta tayi fatan samun iyayen ta da ransu. Ayisha da Adnan babu alamun wani canja tare dasu tunda wannan ne zuwan su na farko Nigeria saidai suna ta kalle kallen sabbin fuskoki, Mamy ta sama musu cab ta fada mashi ya kaisu hotel din da ya sani saboda ita bata san ko ina ba a Abuja, wannan ne zuwan ta na farko. Bala Driver ya washe baki yace to ranki ya dade, The Wells Carlton dake Asokoro ya kaisu. Mamy ta sallame shi da dollars din dake hannun ta sana ta roke shi alfarma idan zai iya taimaka mata ya kaita inda ake canjin kudi, Bala da tunda aka bashi wannan kudin yaji wata zufa zufa na neman safkar mashi ya kuma washe baki yace Hajjaju duk abinda kike so zanyi maki, yaushe kike son zuwa wajen en canjin? Mamy ta jinjina kai gami da cewa idan ba zai damu ba ta shiga ta sama wa yaranta masauki sai ta fito su tafi, Bala yace to ranki ya dade bari in nemi waje inyi parking.
Baifi awa daya ba cikakka Mamy ta dawo wajen bala ta shiga suka tafi, suna tafiya tana kalle kalle, shi kuma Baka a ranshi yana jinjina wannan wace irin mata ce? Anya ta kuwa san yawan kudin data bashi ne? Basu jima ba acan ma Mamy ta dawo dauke da matsakaiciyar jikka, a hanyar komawar su the wells carlton ne Mamy ke tambayar shi ina zata samu drivern da zai iya kaisu kaduna gobe da sassafe? Bala da yake tunani a ranshi yake magana baisan a fili bane yace habawa ni wawan inane zan hada ki da wani driver hajia alhalin gani? Mamy tayi murmushi tace to babu matsala, karfe nawa zaka zo goben? Bala ya shafa kanshi alamun kunya baisan maganar a fili yake yi ba, yace Hajia ke zaki fada sanda kike so inzo, Mamy tace zaka iya zuwa idan ka gama sallar asuba? Bala yace eh In Sha Allah, da haka sukai sallama.
Washe gari ba'a jima da gama sallar subh ba Bala yazo as promised, tunda ya loda traveling bags dinsu suka gaisa sai suka dauki hanyar kaduna, awa biyu ya kaisa kaduna. Mamy ta fadawa Bala sunan anguwar su, Balan yace ya sani, dan haka suka shiga cikin gari, komai ganin shi Mamy takeyi wani iri saboda jimawar ta da garin, anguwar tasu tana nan yanda take sai dai gyaruwa da tayi sosai, amma abun mamaki gidan su data sani ada yanzu ta kasa gane shi sai raba ido takeyi cikin faduwar gaba.

Mrs sS❤️✨

AUREN SIRRIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt