Auren sirri 35

280 9 0
                                    

🔐Auren sirri🔐 3️⃣5️⃣
MARUFIN LABARIN
Bayan shekara biyar da suka biyo baya babu komai a tare da rayuwa su sai ci gaba da zaman lafia cikin aminci da yardar juna, bayan haihuwar Mu'azzam Junior da Adnan Junior da shekara uku ne Ayisha ta sake haihuwar diya mace suka saka mata sunan Mummy, yayin da suke kiran ta da Maama. Amaal ma da suke Turkey ta haifi yaran ta biyu duka maza, suma sunfi sunan daddy da Abba.
Amira da Amatullahi ma Allah Ya kawo musu nasu mijin tun shekarar data gaba ta, Amira na Lagos yayin da Amatullahi ke Kaduna, ko waccen su da nata yaran, rayuwa fa Alhamdulillah tayi kyau ga kowannen su, sai sam barka.
Gefe daya kuma zumuncin Abba da Daddy sai kara karfi yakeyi saboda haduwar iyalan su, Mummy kuwa har islamiyya ta manya ta samu suka koma ita da Mamy, kullum suna tafia tare su dawo tare.
Mu'azzam King idan ka ganshi a yanzu zaka rantse bashi bane, ya kara wani cikar zati da haiba, shi da kan shi yakan tsokani Ayisha  da cewa yasan kiwon ta ya amshe shi dan gashi nan ya zama babba sosai, saidai tayi mashi daria kawai.
Ayisha ma ta shiga islamiyar su mummy tana binsu kullum suje su dawo, Adnan an samu shiga Nile University dake nan Abujar yana karantar computer saboda yace dunia ta fara komawa akan computer kuma nan gaba kadan komai zai zama dole sai computer din dan haka gara ya karanta tun yanzu, Abba ya goyi bayan Adnan yayin da mamy taso ya karanci medicine, amma hakanan ta hakura da Abba ya kara mata bayanin abinda ya hango sai tace to Allah Yasa hakan shi yafi alkhairi, Allah Ya bashi sa'a.
An saka twins din Ayisha school, Ayishan da kanta take kai su ta dauko su, da yamma kuma malamin islamiya na zuwa har gida ya koyar da yaran, sai ta nemo wata er uwar su Karima da mijin ta ya rasu take zaune da su tana kara kula mata da yaran musamman idan ita Ayishar ta fita islamia, dama batun aiki ma dai Ayisha jingine shi tayi gefe ta rungumi business din ta kuma Alhamdulillah komai na tafia yanda ya kamata.

Ya labarin su Nadia??
Sun sha bakar azaba kafin baban nadia ya hakura ya mayar da su gidan shi, saida kuma yayi warning din su sosai akai bin bokaye da malaman tsubbu har saida ya gitta auren su yace duk ranar da maman nadia ta kuma kara taka kafarta ko ta yi aike wajen bokayen da malaman tsubbu to a bakin duka igiyoyin ta na aure, kuma idan tayi ta boye ba tare da ta bari ya gane ba to ta sani Allah Yanaji Yana gani kuma yasan cewa shi kam Allah Ba zai kama shi da laifi ba sai dai Allah Ya kama ta da laifi, da wannan suka samu suke lallaba rayuwar su.
Nadia kam kullum bata da aikinyi sai kuka, dare da rana da safe kuka take saboda tsakani da Allah tana son king so mai yawa, sanda kuwa ta samu labarin haihuwar Ayisha ai zauci ne kadai Nadia ba tai ba, tabi ta rame ta lalace, duk wani gayu da aka san Nadia da shi sai ta zubar da komai, gashi tun tana samun layin shi yanzu ta dena wanda hakan ya tabbatar mata da ya canja layin waya ne, saboda ta kira da wasu layikan amma bata samu.
Maman Nadia kan ta tana tausayin halin da Nadia ta samu kanta, wanda ita ce babbar silar hakan shiyasa ita ma wani lokaci takan boye kanta daki tayi kuka ta godewa Allah, wai a irin wannan lokacin ne kuma baban Nadia yake fada musu ya samu mata zai aura, budurwa ce amma babbar budurwa dan kuwa shekarun ta 37 amma bata taba yin aure ba sai wannan lokacin Allah Ya kawo baban Nadia kuma ta amshe sa da kyau, baban Nadia yaci gaba da fada musu ma'aikaciyar CBN ce kuma ta na can headquarter Abuja koda anyi auren acan zata zau na dan haka basu da damuwa da ita, ita dai Nadia bata ji wani abu mai muhimmanci ba cikin maganar baban ta face Abuja! Yayin da maman Nadia ta fashe da kuka ta kama kafar baban nadia tana rokon ya mata rai kada yayi auren nan bayan shekarun da suka kwashe tare yanzu lokaci daya sai ya mata kishiya kuma ma'aikaciyar cbn ai bai mata adalci ba.
Baban nadia yayi tsaki ya janye kafar shi yace duk ke kika jawo wa kan ki, aure kuma anyi an gama, ya sa kai zai fice sai nadia tayi saurin cewa baba dan Allah ka taimakeni ka kaini Abuja in zauna, baban ya juyo ya harare ta gami da cewa saboda ki samu hanyar zuwa ki watsawa Mu'azzam gida? Ashe kenan har yanzu baki tuba ba? To babu gidan da zaki kina nan Lagos, ya kuma jan tsaki ya wuce. Amma harga Allah a ranshi yana tausayin Nadia duk da yasan ita ta jawa kan ta, to amma ai diyar shi ce kuma yana da laifi akan tarbiyar ta, shine ya sakarwa uwar ta komai na yarinyar to me yasa yanzu yake jin zafin su? Sai kuma ya tuna da maganar daddyn king dan haka sai jikin shi yayi sanyi ya koma cikin falon ya same su yanda ya bar su, kai ya isa wajen nadia ya kamo ta ya zaunar da ita, ya rika buga bayan ta a hankali yana bata hakuri akan tayi shiru da kukan da takeyi hakanan, a kalla minti goma kafin nadia ta nutsu.
Baban nadia yace kiyi hakuri nadia da halin da kika samu kanki ki mikawa Allah al'amurran ki zaki ga sakamako domin babu abinda yake tabbata har abada sai ikon Allah. Ya rika bata baki har taji ta samu nutsuwa kuma zata mika al'amarin ta ga Allah kamar yanda yace dan hak cikin nutsuwa ta rungume shi tana murmushin yake tace ta gode kuma In Sha Allah zatayi kokarin bin shawarar shi to amma bata da ilimin addini, bata san ya zatayi ibada sosai ba, baban nadia kamar zaiyi kuka yace kiyi hakuri ki yafe manu wannan kam laifi na ne ba naki ba domin na mikawa mahaifiyar ki ragamar rayuwar ki da tunanin zatayi abinda ya dace ashe ba haka bane, zan bincika in sama maki malamin da zai rika zuwa yana koyar da ke karatu.
Bayan tafiyar baban nadia ne, mamanta ta kalle ta tana hararar ta tace nadia kamar baki ji ba sosai akn auren da mahaifin ki zai yi ba ko? Nadia tace naji maama amma nasan babu abinda zan iyayi ne akai shiyasa na zabi inyi shiru, ai sai maman ta hau masifa, ita dai nadia ta lallaba ta wuce dakin ta.
Bayan sati daya malamin ya fara zuwa yana koyar da ita kuma ta bada muhimmanci sosai ga karatu dan da alama tana jin dadin karatun tana kuma so, harta shigar ta saida ta canja ta, ko fita ta kamata yanzu sai dai ta janyo cikin hijaban data din ka ta saka ko ta janyo daya daga cikin Abayoyin da tayi order daga Dubai wajen Farasha ta saka, malam yusuf yana girmamata saboda nutsuwar daya fahimci tana da shi da yanda yanzu gaba daya ta canja.
Cikin shekara biyu zaka rantse da Allah nadia ba ita ce tayi rayuwar da tayi ba a baya, har wani annuri take fitarwa, ta samu nutsuwa sosai ga wani aminci da kusanci dake tsakanin ta da baban ta, harkokin sa na kasuwanci duk ya dora ta akai sunayi tare, Malam yusuf ma ashe yayi karatu rashin mai tallafa masa ne yasa bai samu aiki ba kasancewar kasar tamu sai addu'a, in bakasan kowa ba ko dangin ku babu wani mai dan karfi da zai iya taimaka maka to sai ka shafe sama da shekara goma da gana karatu amma baka samu aiki ba, ga dai malam yusuf nan shekara shida kenan da gama karatun shi amma ba batun aiki harya fitar da ran aikin shiyasa ya kama batun koyarwar a islamia da muhimmanci, wata rana ne suna hira da nadia yake mata wannan jawabin, ta tausaya mashi sosai dan haka ta samu baban ta tayi masa bayanin malam yusuf, baban ma ya tausaya masa dan haka kai tsaye shima ya saka shi cikin kasuwan cin da sukeyi, sai ya zama sai bayan ko wacce sallar isha ne suka samun damar karatun tunda da safe an tafi wajen neman na abinci.
Ba'a shekara daya ba saiga malam yusuf na canja kamanni ashe rashi ne ya boye zatin shi da kyawun fuskar shi, cikin kankanin lokaci saboda yawan haduwar da yake da nadia sai ya fara son ta amma yasan tuni bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane dan haka yaja bakin shi yayi shiru har wata shekarar ta sake gabata, a nanne kuma kwatsam baban nadia da kan shi yake tambayar malam yusuf ko zai amshi tayin auren nadia? Me zaiyi idan ba sujudar godia ga Allah ba? Ya dago ya rika zubawa baban nadia addu'a yana gode mashi, baban nadia daba hakan ya zata ba sai shima farin cikin ya kama shi yaji kuma ya kara nutsuwa da malam yusuf din.
Nadia dake bakin kofa tun daga farkon lamarin itama murmushi tayi cikin amincewa da batun baban nata na auren malam yusuf saboda shekara hudu kenan suna tare bata taba ganin halin banza tare da shi ba, ga sanyin rai da daukar abu da sauki, koda ya samu aiki tare da baban ta a yanzu bai canja halayen shi ba sai ma abinda ya karu kuma har gida ya kawo iyayen shi sukaiwa baban nadia godia tun sadda ya dauke sa aiki, wasu hawaye masu dumi suka zubo ma nadia sakamakon tunawa da king da tayi, duk tsayin lokacin ba wai ta dena son shi bane dan ita tana ganin ma tun farko Allah Ya dasa soyayyar king a zuciyar ta ne wanda har yanzu babu abinda ya ragu na son da take mashi to amma ya zatayi da abinda Allah Ya tsara? King ba mijin ta bane ba, malam yusuf shine mijin ta daya dace da ita da rayuwar ta dan haka ta saka hannu biyu ta share hawayen ta tanawa Allah godia a ran ta.
Ashe da baban ta da yusuf din sun gan ta, baban ya kira ta ta zauna kusa da shi yake tambayar ta taji duka abinda suke magana shi da yusuf? Ta ce eh baba, baban ya kuma cewa baki amince bane ba shiyasa kike kuka? Wasu hawayen suka kara zubo mata wannan karon bata damu ta goge ba cikin kukan take girgiza kai tace ba haka bane ba baba, ina hawaye ne saboda naji dadin hakan, ina hawaye ne saboda in nuna godia ta ga Allah, ina hawaye ne saboda in godewa Allah Da Ya bani kai a matsayin mahaifi mai nemawa 'yarsa gatan aure tare da mutum mai ilimin addini da na zamani mai tsoron Allah irin yusuf, a karshe kuma ina kuka ne saboda ban dena son king ba amma na hakura da shi tunda ba shine miji na ba, tana kaiwa nan ta mike ta fice da sauri tana ci gaba da kuka.
Jikin yusuf a sanyaye da jin karashin bayanin nadia ya kalli baban ta, baban ya masa murmushi yace karka damu da gaske ta amsa batun auren ku da zucia daya kuma tana so, amma ka bata lokaci. Tun daga ranar yusuf ya kara dagewa da addu'a yana neman zabin Allah, bayan sati daya kuwa nadia da kanta ta neme shi tana zolayar wani irin ango ne haka baya neman amaryar shi? Dan daria harda shaqewa daga nan suka hau hira.
Sati biyu da suka zagayo aka daura auren su babu wani shagali amma anyi walima, iyayen yusuf ma sunzo, amaryar baban nadia ma wato Safiya ta samu halartar bikin tare da dan yaron ta data haifa, komai anyi shi lafia an gama lafia, sai addu'ar Allah Ya basu zaman lafia, ameen.
To haka rayuwar taci gaba da tafia cikin mutunta juna da sanin darajar juna, ga soyayyar da yusuf ke mata tasa itama ta fara son shi tsakani da Allah, shekara daya daidai nadia ta dire diyarta kyakykyawa fara tas, ranar suna yusuf ya mayar da sunan nadiyar suna kiran ta da baby. Maman nadia ma dole yasa ta sauke makaman yakin da take da kishiyar ta ganin ita kishiyar babu abinda ma ya dame ta, musamman daba ko gari daya suke ba.
Business trip ya kama yusuf sai ya tisa nadia gaba da diyar su suka wuce Abuja, kwanaki biyar suka gama abinda ya kai su, nadia kai tsaye ta roke shi alfarmar zuwa gidan king, yusuf baiji komai ba yace shi zai kaita da kan shi, suka kira ube ya dauke su zuwa maitama kasancewar a Asokoro sukayi masauki.
King da Ayisha na zaune suna taya yaran su homework door bell yayi kara, Ayisha ta mike tana cewa let me get the door, tana budewa taci karo da nadia dauke da diyar ta, cikin sakin fuska sukaiwa juna murmushi kafin Ayisha ta bata hanya ta shigo ciki, king yayi mata marhabin da zuwa gami da ansar babyn ta, yana cewa Masha Allah! Wannan beautiful baby haka Nadia duk ke kika haife ta? Nadia na murmushi tace to indai amshe man diya zakayi ai gara in boye ta tun yanzu, sukai daria su duka, nadia tace idan ba matsala miji na zai iya shigowa? Cikin sauri king yace of course yes, bari in shigo da shi. Cikin kankanin lokaci aka sauke musu abinci dana sha suna ta hira kamar babu abinda ya faru marar dadi ada can, cikin hirar ne nadia ke neman yafiyar Ayisha akan abubuwan da suka mata, Ayisha tace babu komai ta yafe mata tuni, nadia ta tambayi mummy, king yace tare muke zaune muje ku gaisa.
Gaba dayan su suka isa wajen mummy, ita kanta taji dadin ganin nadiyar musamman data ganta tare da mijin ta da diyar ta, aka ci sa'a daddy ma yana nan, dan haka sun jima anan har sukai sallar magrib kafin sukai shirin wucewa hotel din su, Ayisha ta roki su kwana mana, Yusuf yace ya musu alkawarin zasu zo musu hutu amma yanzu gobe ne zasu koma Lagos gara su tafi su tattara kayan su dan sukai exchanging contacts kafin su tafi.
Rayuwa mai dadi da kwanciyar hankali ke gudana ga ko wanne bangare, harta matar Alhaji Ahmad wato maman sister din Adnan, ta nemi Mamy ta bata hakuri akan abinda tayi mata, harta wasu kadarorin Alhaji Ahmad sai da ta kawo su duka tace gashinan abinda ke akwai wanda ta batar ba yawa ne gare shi ba, wai a raba gado yanda musulunci yace, to haka dai rayuwa taci gaba da tafia cikin jin dadi da mutunta juna.
Alhamdulillah! Anan na kawo karshen labarin Auren Sirri.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now