Auren Sirri 17

133 17 5
                                    

🔐Auren sirri🔐 1️⃣7️⃣
Bayan shigowar Malam Isuhu daga masallaci, ya nufi dakin Inna Rahane anan ya same su shiru babu mai magana, ya mikawa Hibba yalon daya siyo mata as promised, Muhd ne ya kasa hakuri yace 'Baba da gaske yanzu Yaya Maryam auren Adamu zatayi'? Malam Isuhu yayi gyaran murya gami da murmushi yace indai ina raye kuma Adamu ba canja hali yayi ba to da izinin Allah bazan bashi auren nutsatstsiyar yarinya kamar Maryam ba dan haka ku duka ku kwantar da hankalin ku babu abinda zai faru sai alkhairi. Wata ajiyar zucia su duka suka saki sana ne suka samu nutsuwa a zukatan su amma duk da haka ita Maryam har yanzu da sauran tsoro a ranta shiyasa ta kudiri aniyar gobe idan sun hadu da Ahmad zata fada masa duk abinda ya faru.
Washe gari saida Maryam ta tabbata ta sanarwa Ahmad abinda ke faruwa tun kafin su shiga exam hall, Ahmad yayi shiru kamar ruwa ya ci shi ga wata irin fargaba saboda tsakani da Allah yana son Maryam har baisan yawan son da yake mata ba, da kyar ya iya kwantar da hankalin sa kafin ya kwantar mata da hankali akan cewa tunda Malam ya fadi bazai ba Adamu auren ta ba to ba zai bayar ba din.. Maryam ta katse shi da cewa Ahmad bawai Baba nake ji ba, Inna Indo nake ji da sauran matan Baba lallai zasuyi duk abinda zasuyi dan suga auren nan ya tabbata.. shima ya katse ta da cewa yana kallon agogon hannun sa kije kiyi exam kafin ki fito zan nemo mana mafita daga haka Maryam ta shige exam hall, shi kuma ya juya staff room ya danna kiran Usman.
Bayan ya zayyanewa Usman halin da ake ciki sai sukai shiru su duka, daga baya Usman yace mezai hana tunda ka tabbata kana son ta kuma da aure kawai to ka aika iyayen ka gidan su a nema maka auren ta kuyi auren ku kawai.. Ahmad yai saurin katse Usman da cewa haba Usman wai menene nawa baka sani ba da zaka fada man maganar in aika iyaye na gidan su Maryam? Halin iyayen nawa ne baka sani ba ko kuwa nawa qudirin ne baka sani ba? To jeka ma naji zan iya hakura da qudiri na in auri Maryam tun yanzu amma kai har a ranka kana ganin iyaye na zasu amince in auri Maryam ne bayan ga waccan manaciyar yarinyar data like zaune gidan mu wai tana jira na, yaja wani dogon tsaki saboda tuno er uwar shi mai son shi da yayi. Usman ya saki ajiyar zucia yace gaskia ne aboki na na fahimci me kake magana akai, to amma ga wata shawara, cikin sauri Ahmad yace yawwa ko kaifa fadaman ina jin ka, saida Usman ya nisa kafin yace kuyi aure kaida Maryam a boye kawai.. Ahmad ya tari Usman ban gane muyi aure a boye ba, kamar yaya? Usman ya dan saki daria yace abokina Maryam dai ta ruda ka baka ko fahimtar abubuwa sosai to ina nufin kuje wani wuri a daura maku aure kuyi auren sirri wato auren da babu wanda ya sani, matsalar shine iyayen Maryam basu da matsala ko yanzu kaje zasu aura maka ita amma kai naka iyayen ba zasu je nema maka auren ta ba kuma bana tunanin iyayen Maryam sun cancanci ka nemo iyayen bogi ka kai musu a matsayin iyayen ka aida na baka wannan shawara dan haka auren sirri kai da Maryam shine daidai daku, ta yanda ko nan gaba aka dauko maganar Adamu indai Maryam zata fadi tana da auren ka ai kaga dole su shafa mata lafia koya ka gani? Ahmad ido ya rufe ya kasa gane cewar gurguwar shawara ce wannan sai kawai yayi na'am da shawarar harma nan take suka shirya inda zasu a musu auren, wajen wani kakan Usman din dake nan cikin kauyan zaria a hunkuyi, tuni suka aje magana da Usman akan zai isko Ahmad kaduna gobe da safe in yaso sai suje zariyar goben ko jibi, da wannan suka aje wayar, Ahmad kuma ya tsaya jiran Maryam ta fito daga exam hall dan ya fada mata abinda ake ciki.
Ba'a jima ba sosai suka kare exam din suka fito, Ahmad ya zayyanawa Maryam shawarar da suka yanke shida Usman din sana ya kafe ta da ido ya wani marairaice yana neman amincewar ta karta bari a raba su, Maryam mai cike da kuruciya da bata san komai ba tayi shiru tana tunanin iyayen ta da en kannin ta, yanzu idan ta aikata haka tayi musu daidai kuwa? Maryam ta nisa tace Ahmad gaskia ba zan iya yiwa iyayena wannan butulcin ba dan basu da laifi ko yanzu ka aika gidan mu zasu baka aure na da ace ba zasu baka bane toda na amince amma tunda ina da tabbacin basu da matsala gaskia bazan iya yin aure basu sani ba, daga haka Maryam taja jiki ba tare da ta saurari komai daga bakin Ahmad ba tayi gida.
Ahmad ya dinga bin Maryam yana hadata da Allah akan ta saurare shi amma taki, dan har wani bacin rai ya fara taso mata, fincikar hannun ta yayi wanda yasa dole ta tsaya gami da fisge hannun ta tace Ahmad ka barni in tafi gida kafin su fara nema na.. Ahmad bai tsaya jin batun taba ya hau yi mata baya ni cewa tsakani da Allah shi bashi da matsala inta shi ne amma iyayen shi ba zasu taba bari yayi aure ba saboda akwai wadda suke so ya aura er uwar shi ce, kuma shi yana ganin iyayen Maryam sunfi karfin ya nemi wasu iyayen ya kai musu a zuwan iyayen shi ne amma ya take gani ya nemi wasu mutanen ya kai wa su Malam da sunan iyayen shi ne ko yaya? Maryam tayi shiru kafin tace ka bari zuwa gobe zan fada maka shawarar dana yanke, da wannan suka rabu.
Ilai kuwa tana zuwa gida ta iske Adamu zaune kofar dakin su an shinfida mashi tabarma wai yazo zance wajen Amaryar shi ne, sai wangale baki yake wai murmushi ne a wajen shi, yayin da Inna Indo ke can kofar Inna Fulera suna maganar bikin, gaban Maryam ya fadi ganin Adamu ita tsoron shi ma take ji ta fara sanda zata nemi shigewa daki aikuwa Adamu yasa kafa ya tado ta sai gata kasa ta saka kara saboda zafin buguwa, Inna Indo dake can gefe ta gyada kai gami da cewa kayi man daidai Adamu dan uban ta tana ganin ka amma tayi kamar bata ganka ba zata shige daki, to haka za'a aura mashi ke kina masa rashin ji ai gara tun yanzu ka koya mata hankali, sai Inna Fulera ta anshe da cewa lallaikam ai uwar ta Rahane wata kika ta gama zuge ta kaf shiyasa kikaga ta fara wa Adamu rashin kunya, nan dai sukai ta tofa albarkacin bakin su, shigowar Malam Isuhu yasa su yin shiru, da hanzari ya isa wajen Maryam ya mikar da ita gami da cewa lafia dai Maryam kike kwance kasa kina kuka? Kafin ta ansa mashi Hibba ta fito daga daki tana cewa Baba ai Adamu ne ya kada Yaya Maryam waita ganshi zata shiga daki bata masa magana ba, sai Inna Fulera ta anshe da cewa kinji ko Indo aina gaya maku Rahane banda hurewa yaranta ido babu abinda takeyi kiji wai waccan lalatacciyar yarinyar abinda take fadi.. Malam Isuhu yayi hanzarin katse ta da cewa Hibba ba lalatacciya bace kuma ba zata taba zama haka ba da izinin Allah sana kuma na kara jin kin fadi wata magana makamanciyar wannan akan yarana wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! A bakin auren ki, sai koke koke ya fara tashi cikin gidan kowa na fadin abinda yaga dama duk dai akan Rahane da yaran ta, cikin fushi Malam Isuhu ya daka musu tsawa sana yace aure ne tsakanin Adamu da Maryam ba za'ayi shi ba har abada domin basu dace da juna ba faqat kowa ya tashi ya san inda dare ya masa, sai kuwa Inna Indo ta aza hannu akai ta rusa wani uban ihun da yasa makwabta fara shigowa suna tambayar lafia dai ko mutuwa akayi? Yayin da Inna Fulera da Inna Fatsima suka hau kukan karya suma suna sallallami wai andai shanye Malam to gaya nan Rahane zata raba zumuncin Allah.
Duk abin nan da ake Inna Rahanen tana daki tana ji amma batai magana ba kuma da alama bata da niyyar magana saida taji cewar wai zata raba zumunci sana ta fito tana basu hakuri tana cewa indai Maryam ce gata nan yau din nan ma a daura mata aure da Adamu, amma kada wani ya kara fadin zata raba zumunci, Malam Isuhu ya tare Inna Rahane da cewa cikin fushi Rahane maza ki koma daki sana kuma idan ke kadai keda ikon aurar da Maryam saiki sanar dani, Adamu kuma dana ne amma nace bazan bashi auren Maryam ba duk abinda zasu ce suce ke Maryam tashi maza ki shiga daki bari inje in nemo maki maganin ciwon jiki.
Adamu banda ashar din mashaya babu abinda yake saki, yanayi yana alwashin saiya dauki fansa indai ba'a bashi auren Maryam ba to babu wanda zai aure ta dan zai shiga zai fita dan ya tabbatar da hakan bai faru ba, da kyar Inna Indo taja shi suka tafi yanata zage zage a haka suka bar gidan.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now