Auren Sirri 27

145 14 4
                                    

🔐Auren sirri🔐 2️⃣7️⃣

Cikin satin Mamy da Abba (Ahmad) suka shirya suka nufi Minna wajen neman dangin Alhaji Ahmad, abun yazo da sauki ne sakamakon sanin sunan anguwar daya taba fada mata ne sadda yana raye, gida ne babba daka gani kasan gida ne mai cike da dangi. Aka sauke su bangare guda jin cewa baki ne da suka danganci marigayi Alh Ahmad, bayan gaisuwa ne Mamy ta gabatar da kanta gurin dattijan matan ta kuma sanar masu abinda ke tafe da ita da maigidan ta dake kofar gida, dan danan akaje aka shigo da Abba (Ahmad) sana akai gaggawar kiran dattawan mazan domin suji abinda ke tafe da bakin. Bayan sun iso an sanar dasu har share hawaye saida wasun su sukayi kafin wani yayi gyaran murya yace shi sunan shi Alh Jafar kuma shine babba a wajen iyayen su kafin su rasu, sai Alh Ahmad da shima ya rasun sana mata biyu da wani namijin daya duk ya nunawa su Mamy su, yace lallai Alh Ahmad ya taba kira na lokacin yana Italy ya sanar mani zancan auren shi da wata yarinya da kaddarar rukon ta ya koma hannun shi a wancan lokacin, ban wani ja da nisa ba nayi addu'a na kuma sanar da sauran en uwan mu gasu nan ko ba haka akayi ba, ya tambaye su yana mai maida duban shi gare su, duk suka amsa da cewa wannan gaskia ne Yaya. Alh Jafar yaci gaba da cewa bayan nan muna yawan yin waya da shi saboda kaf din mu shi kadai ne Allah Yayi wa arziki mai tarin yawa kuma Allah Ya bashi ikon daukar nauyin mu daidai bakin iyawar shi a lokacin yana raye, ko jarin da muke dashi yanzu gaba dayan mu shine ya bamu shi a lokacin yake fada mana saboda halin rayuwa yana so yaga kowa cikin mu yana da abinyi, Alhamdulillah yanzu kowannen mu muna da kasuwancin mu muna rike da iyalan mu sai godiyar Allah da kuma yawan addu'ar Allah Ya gafartawa Alh Ahmad daya yi tsaye akan rayuwar en uwan shi. Alh Jafar ya danyi shiru kafin yaci gaba da cewa bayan wani lokaci Alh Ahmad ya fada mani matar shi daya aura ta haifa mashi yaro namiji kuma yasa mashi sunan shi wato Ahmad. Munji dadi mun kuma yi murna sosai saboda diyar shi daya Alima a lokacin kuma shi mai son yawan iyali ne, bayan wani lokaci kuma sai labarin rasuwar shi muka samu wanda daga nan bamu sake jin wani batu daya dangance shi ba bare na yaran nashi, dama can matar shi Halima ba son kasancewar mu da dan uwan mu takeyi ba to bare baya raye. Baifi shekara daya ba kenan da ita Alima ta neme mu da kanta, ta bamu hakuri akan rashin zuwan ta tace mana mahaifiyar tace ta tura ta France domin tayi karatu kuma data dawo bata bata damar neman dangin mahaifin ta ba acewar ta bama son ita Alimar, tunda bamu taba neman su ba bayan rasuwar dan uwan namu mu kuma munsan mu ya kamata tazo ta samu kodan rabon gadon dan uwan namu duk da munsan ba zamu samu wani abu ba tunda yana da yara mace da namiji kuma wa'anda zasu iya samun wato Iyayen mu suma babu ran su amma duk da haka munyi tunanin zata neme mu. Bayan Alimar tazo ta nemi mu yafe mata muka tabbatar mata ita tamu ce kuma bata mana laifin komai ba, daga karshe ta fada mana yanzu ma mahaifiyar tata ta amince da tazo wajen mu saboda maganar auren ta ne ya tashi, daga karshe ta sanar mana batun kanin ta wanda take nema duk da bata san inda zata same shi ba ta kuma sanar mana daga baya da maman ta ta tura ta France tayi karatu daga can din saida ta je Italy da fatan zata samu kanin ta da maman shi amma batai nasarar samun su ba kuma bata san inda zata neme su ba amma bata taba mantawa da su ba kuma tana fatan Allah Ya hadu su, sana ta sanar damu maman ta ta dauke duka dukiyar mahaifin ta bata barwa kanin ta da maman shi komai ba kuma ita a lokacin bata da wani wayau na sanin abin yi yanzu ma ta sanar mana ne dan kawai mu sani amma daga baya tayi nasarar samun takardar wasu kadarorin Alh Ahmad din ta kuma dauke ta boye da niyyar duk randa Allah Ya sada ta da kanin ta da mahaifiyar shi zata damka masu domin suna da kaso a cikin dukiyar mahaifin nata, Alh Jafar ya karishe da fadin yanzu haka tana nan Abuja tana aure da danta guda daya wanda ta mayar wa sunan mahifinta da kuma kanin ta wato Ahmad, ko jiya ta kira ni mun gaisa amma yanzu nan tunda gaku bari in kira ta ku gaisa saiku anshi number ta tunda kunce kuma a Abuja kuke idan kuka koma saiku sada ta da dan uwan ta dan Allah.
Cike da farin ciki Mamy ta kira Alima ta gabatar mata da kanta, Alima sai ta sa kuka wanda da kyar mamy ta samu tayi shiru, ina kani na Mamy? Yana nan Abuja Alima ina dawo wa zamu zo ki gansu, Alima ta kuma cewa Mamy yanzu Ayisha ta girma sosai ko? Mamyn cikin daria tace Ayisha harta karashe First Degree dinta, me yiyuwa ta sake komawa yin Second Degree ma. Nan dai sukai exchanging contacts da alkawarin neman juna.
Cikin jin dadin saukin al'amurran su Mamy suka rabu da iyayen Adnan bayan Abba (Ahmad) ya cika su da alkhairin sa da kuma alkawarin kawo Adnan dansh gan shi.
As promised  bayan sun dawo Abuja Mamy ta sanarwa Ayisha da Adnan yanda suka samu dangin mahaifin sa da yayar sa Alima, suma sunji dadin hakan har suka kasa hakuri aka saka mamy gaba akan ta tashi su tafi gidan Alimar, babu yanda mamy ta iya haka suka isa maitama gidan Alima. Alima harda kukan ta bayan sun hadu, iya dadi su duka sun jishi Alima ta roki mamy ta yafe mata, Mamyn tace baki man komai ba Alima, har mahaifiyar ki na yafemawa. Har mijin ta saida Alimar ta kira Sadik ya dawo suka gaisa da su Mamy cikin tsokana yake cewa Alima yau dai naga Mamy dasu Ayisha da Adnan dan haka no more crying bansan inda dan kani na yake ba, su duka suka kwashe da daria, Sun jima gidan suna sada zumunci kafin suka bar gidan da alkawarin ziyartar juna akai akai cike da farin ciki.
Daren yau Mamy ta raya shi ne tana wa Allah godia marar iyaka akan ni'imomin dayayi mata, kusan dukkan abinda ke damun ta a baya yanzu sun zama tarihi, Abba (Ahmaad) daya gaji da jiran ta ya isko ta kan sallaya ya kamo hannun ta yana mai sakar mata murmushi yace indai ba hanjina kike roko Allah Ya baki ba ai kin jima da samu na Mamy na da duk abinda na mallaka da ni kai na naki ne, Mamy tayi daria ta mike gami da rungumar sa ta rada masa a kunne da cewa sanin hakan ne yasa nake godia marar iyaka ga Ubangiji Da Ya mallaka mani Abban mu da duk komai nasa, babu abinda zanyi daya wuce godia da kara kaskantar da kai na wajen Allah... Abba ya katse ta da cewa idan hakane nima muje a kara gode mani ta hanyar nuna mani wannan soyayyar da aka shayar dani shekaru da yawa da suka wuce, mamy tana zare hijabin jikin ta take ansa mashi da cewa Abba wai bamu tsufa bane, dubi Ayisha da Adnan duk sun girma fa... shshsh a ido na mamy na kullum kamar Ayisha take dan haka muje in samu nutsuwa a tare da ke mamy na. Lallai ne gaskiyar masu magana domin na kara tabbatar da soyayya bata tsufa saidai masoyan su tsufa, ga dai Abba da Mamy an samu nutsuwar da ake bukata, bayan sun fito daga restroom Abba yayi drying hair din mamy sana suka kwanta bisa gado da niyyar yin pillow talk. Kansu akan pillow daya yayin da suka makalkale juna sai kuma ajiyar zucia ta biyo baya daga wajen Mamy, Abba yace yadai Mamy na, wannan ajiyar zuciyar fa? I hope all is well? Mamy tace Ayisha ce Abba, cikin hanzari Abba yace meya faru da Ayishan? Mamy tace soyayyar data faru damu ita ke faruwa da Ayisha.
Mamy ta zayyanawa Abba komai game da Ayisha da King babu abinda ta rage wanda tasan ta sani hatta alakar ta da Maman Alima da yayar ta wato Maman Nadia da kuma ita kanta Maman King din saida ta sanarwa Abba da karshen haduwar su a school din su Ayishan da abinda ya faru, Abba yayi shiru bayan ya gama jin labarin kafin ya dora da cewa yanzu me nene mafita? Mamy tace mafita bata wuce addu'a ba Allah Ya zaba masu mafi alkhairi amma ni abinda ke damu na shine nasan halin Ayisha da boye damuwa haka zatayi ta boyewa tana barwa ranta ita daya, ni kuma ina sane da halin da take ciki to amma banda iko akan komai sai abinda Allah Yayi amma dan so lallai king yana son Ayisha kuma zanyi farin ciki idan ta aure shi dan ina da tabbacin zai rike ta amana zai kuma bata soyayyar da yake mata. Sun yanke shawara akan zasu dukufa yi mata addu'ar zabin mafi alkhairi har suga abinda Allah Zaiyi, da wannan suka mike domin gabatar da sallar subh saboda an fara kiran sallar.
**        **
Ina labarin king???
Idan masu karatu basu manta ba munbar Mu'azzamn Ibrahim Fari (King) a gadon asibiti sakamakon heart din shi daya tabu akan abinda ya faru a school, a gigece Alhaji Ibrahim Fari (Daddy) ya isa hospital din, gaskia ne King yana da farin jini saboda yanda halin shi ya fita daban dana sauran en uwan shi, baga Iyayan nasu ba bare ga mutanen sanayyar su, King kwance kamar matacce banda numfashin dake fita ta oxygen lallai da mutum zai iya cewa baya da rai ma, a wannan halin su Mummy suka iso suma, Mummyn har kuka tayi ganin halin da yake ciki, maimakon taji tausayi ta nemi da Allah Ya tada mata danta lallai zata cika mashi burin shi ta hanyar barin sa ya auri Ayisha a'a sai ma wani mugun tsanar Ayishan data kara mamaye zuciyar ta, ita kam Mummy a rayuwar ta ta tsani duk wata mace da danta guda daya jal zaiyi wa irin wannan mugun soyayyar, a wannan halin Mama da Nadia suka iso, banda kuka babu abinda Nadia keyi itama tana tsinewa Ayisha a fili, hakan ya janyo hankalin nurses din suka nemi dasu bar mara lafia shi daya, Daddy jin batun Nadia ya kalli Mummy ya tsare ta da ido yana cewa me Nadia ke fadi? Wacece Ayishar sa take magana? Sai aka rasa mai bawa Daddy amsa, saida ya daka ma iyalin shi tsawa ne da bai taba masu ba sana Amatullahi cikin in ina tayi wa Daddy bayanin abinda ya faru, idan ranshi yayi dubu duka ya baci, yama rasa irin fadan da zaiyi sai tsoki ya saki gami da cewa akan wannan issue din babu mai kashe mani da, Allah Yana bashi lafia zan bashi damar auren yarinyar da yake so, daga haka Daddy ya wuce cikin fushi.
Bayan dawowar su gida ne a falo suka zauna kowa da abinda yake sakawa a zucia, Nadia dama tun a hospital ta fara kuka jin batun daddy, Mummy ta nisa tace kai ina lallai Daddy ya canja maganar shi domin da ranta dai ba zata bari yaron ta daya ya auri waccan yarinyar ba, yayin da Maman Nadia ke kara zuga maganar akan lallai karta bari hakan ya faru, a haka Amal ta sauko kasa ta same su bata ko kula su tayi hanyar fita, Mummy ce ta daga murya ta kwala mata kira, Amal ta tsaya cak ba tare data juyo ba kumi ta tuna kuma oho, saita juyo cikin murmushi har wajen su tace Mummy naga kamar baku bukatar in saka maku baki akan kudirin ku, amma abu daya da nake so in tambaye ki shine shin kinfi son Nadia ne akan dan cikin ki ko kuwa farin cikin Nadia kika fi so akan na King? Mummy kiyi hakuri amma kije kiyi tunani akan wannan tambayar da nayi maki, daga haka Amal tayi gaggawar barin falon ta isa hospital wajen king.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt