Auren sirri 05

293 19 0
                                    

🔐 Auren sirri 🔐 5️⃣
Washe gari ciwon kai mai tsanani ya hana Ayisha zuwa school bare su hadu da king, wanda ita a ranta rashin zuwan ya mata dadi kasancewar tasan idan ma sun hadu da King tambayoyi ne zaita mata wanda a nata wajen bata da amsar bashi ko kuma bata shirya bashi amsar ba kuma ita ba makaryaciya ba bare ta sharara mashi karya.
Yinin ranar kuma Adnan ne yaita kula da 'yar uwar shi, yayin da a ranshi yana jin tsananin damuwar ciwon kan da take ji a nashi jikin, a nashi ganin ciwon kan ne ya matsa mata wanda a zahiri wajen Ayisha tsabar tunani ne kala kala suka mata yawa, Mamy kuwa na can office amma gaba daya hankalin ta na gida sbd tunda safe bata ji motsin Ayisha ba, amma data gama shirya zuwa office ta biya dakin nata sai ta tarar tana fama da ciwon kai, ta shiga damuwa sosai a haka ta tafi office amma tayi waya da Adnan tana tmbyr jikin Ayishan yafi so a kirga. Sunyi sunyi suje hospital kuma amma Ayisha ta kafe akan ciwon kai ne kawai kuma tasha magani dan haka zai sauka.
Gefen King kuwa tunda ya ga lokacin zuwan Ayisha yayi bata zo school ba ya fitarwa ransa da zuwan nata, dan haka ya ji school din ta fita a ranshi sai kawai ya shige mota drivern sa yajashi suka fice, gidan su Ayisha ya nufa amma koda suka zo saiya kasa fita daga motar, tunano yake yasan haka kawai Ayisha ba zata ki zuwa school ba, lallai akwai dalili kuma koma meye yana da nasaba da kukan da tasha daren jiya. To wai menene ya faru ko yake shirin faruwa? Wannan tambaya ita ke yawo wajen King amma ya rasa wazai furtawa bare ya samu ansa, jiki a mace yaiwa drivern sa umarnin ya wuce dashi gida kawai.
  Har suka isa gidan baima sani ba yana can duniyar tunani wanda idan tsare shi kayi ma saiya fada maka abinda yake tunani bazai iya ba, sai dai daka ganshi zaka san wani abu yana taba zuciyar shi. Main parlor kai tsaye ya wuce wanda shigar shi keda wuya ya tabbata yayi nadamar shigowar tasa a parlorn sakamakon ido hudu da sukai da kyakykyawar farar doguwa kuma matashiya maiji da kudi,ilmi,kyau da mukami wato  Nadiya. Yayi tsaye kamar an dasa shi ance karya matsa yayin da ya kasa kauda idon shi cikin na Nadiya wacce keta doka masa murmushin ta dake tasowa tun daga kasan zuciyar ta tsabar murnar ganin mutumin da a dunia bata ga kamar saba, mutumin da take tsananin so kamar tayi hauka, yayin da gefen King gaba daya dan sauran annurin dake fuskar shi ya dauke tsaf, yanda kasan kaje masa da labarin mutuwa. Wani irin tsananin bacin rai ke tasowa a zuciyar shi, ji yake kamar yaje yaita kwashe Nadiya da mari sbd tsananin kin ta da yakeyi.
Salin alim ya nemi ya juya zuwa inda dakin sa yake, kamar an jeho Nadiya sai gata tasha gaban sa cikin dai murmushin nata, tayi saurin riko hannun sa gami da cewa 'haba King, inyi doguwar tafiya in dawo yau ko hutawa banba na taho dan kawai in ganka amma ka kasa tsayawa ko gaisuwa muyi? Anya kuwa kana man adalci King? Bata tsaya nan ba ta juya kanta gefe inda momyn king take taci gaba da cewa 'momy anya babu Aljanu tare da king kuwa? Ki duba yanda yake mani halin ko in kula. Momy dake can gefe tana daria tace 'Nadiya kinfi kusa keda King, kila dai tabo shi akai waje yake nema ya huce kan mu'. Nadiya ta juyo da duban ta kan King gami da daga mai gira cikin kaskantar da murya tace 'what's the matter King'?
   Wani abu ya tasowa king cikin makoshi amma yayi kokarin controlling ya kakaro murmushin yake sana yace ' Nadiya sannu da zuwa, kai na ke ciwo can u please leave me alone? Kafin ma yaji ansar ta ya cire hannun sa data kama ta rike ya kuma cewa 'thank u' gami da wucewa ba tare daya juyo yaga sarara din da Nadiya tayi ba sakamakon abinda king ya mata. Wani abu ne da bai taba faruwa ba, eh lallai tasan king baya son ta kuma baya kula ta amma wani abu makamancin ya share ta haka bai taba hada su ba, to meke damun king?  Ansar da bata da shi kenan dan haka cikin sanyin jiki ta juyo ga momy tace 'momy ga tsarabar ku nan kowa da sunan sa bara na wuce gida inje in huta, zan sake dawowa idan na huta.
Momy ta mike gami da riko hannun Nadiya tace 'kiyi hakuri Nadiya, king zaya daina maki duk wa'annan abubuwan wata rana, kedai ki kara daurewa kuma kisa a ranki kinga baya da wata matar aure sai ke'. Nadiya tayi murmushi na jin dadin maganar momyn kafin tace 'thank u momy, sai na sake dawowa, bata jira komai ba ta wuce wajen motar ta drivern ta yaja suka bar gidan.
Yayin da gefen momy bata bi takan tsarabar da Nadiya ta kawo masu ba sai kawai ta wuce wajen King domin ganin halin da yake ciki. Lallai tayi sa'a tunda kofar sa a bude take dan haka tayi knocking so biyu kafin tasa kai ciki. Gabanta ya fadi sosai ganin king yayi tagumi alamar yana zuzzurfan tunani. Ganin alamun hakan tasan kota masa magana ba zaiji ba dan haka tasa hannu tana jijjiga shi, ya kuwa ja doguwar ajiyar zucia gami da kallon momyn ba tare da yace komai ba.
King, lafia kuwa kake dogon tunani haka? Ganin bai ansa ba sai momy ta mike ta isa ga fridge dake dakin ta tsiyayo ruwa ta dawo ta mika mashi, ya kuwa anshe ya kafa kai ya shanye, gami da sake sakin ajiyar zucia.
Kamar an bude bakin shi ya furta momy bansan meke faruwa da ita ba, yau ko school bata je ba, momy damuwar ta ta saka ni cikin damuwa nima, momyn bansan halin da take ciki ba, kamar zai karasge da kuka.
Cikin faduwar gaba da razana momy tace 'wacece king, damuwar wa? Kai tsaye king yace 'Ayisha ce momy'.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang