Auren Sirri 24

107 16 5
                                    

🔐Auren sirri🔐 2️⃣4️⃣
 
Kullum da kalar wulakanci da habaicin da mutanen gidan suke mana ba Innar mu ba bare mu dake yara a lokacin, Adamu kuwa kamar zaiyi dan karamin hauka saboda ashe shi da gaske yakeyi son maryam yakeyi kuma yana son auran ta, sai shaye shayen shi ya kara hauhawa ma kuma kusan kullum sai yazo nan gidan.
A wannan halin wata rana na samu Malam bayan mun fito masallaci nake tambayar shi yanzu shikenan saboda Innar mu tayi fushi ba za'a dawo da yaya maryam ba? Malam yayi shiru kamar bazai ansa ni ba sai daga baya yaje fada mani yaje yayi iya neman da zai iya amma bai samu ganin ki ba, anan nima nake fada mashi iya nawa binciken da nayi, hankalin malam ya tashi kwarai ta yanda har saida ya kasa boyewa koda ya dawo gida ya fadawa Innar mu abinda ke nan sai itama ta hau kuka tana fadin bata san hakan zai faru ba, lallai tayi fushi dake akan cikin amma batayi zaton zaki iya barin garin zuwa wani guri mai nisa ba, tun daga ranar sai muka dukufa addu'ar Allah Ya bayyanar mana dake lafia. A haka aka dauki tsayin lokaci har kusan shekara daya, bamu taba fidda ran samun labarin ki ba kota wani bangare kamar yanda bamu fasa addu'a ba.
Saida aka kwashe shekara biyu sana wata rana Ahmad yazo har gidan nan yayi sallama da Malam, bayan Malam ya fita ne ya dawo yake fadawa innar mu Rahane muna da baki sunzo akan maganar maryam, ai ba Inna ba hatta ni da Hibba saida muka waiwaya a razane muna kallon malam. Bayan Malam yawa bakin iso suka shigo har dakin Inna akai gaisuwa sai cikin su aka rasa wanda zai fara magana har saida Malam yace to samari kunzo kunce kuna san magana damu akan Maryam kuma kunyi shiru, ina fata dai Maryam din tana lafia? Ahmad cikin rudewa ya fara tambayar Malam cewar Maryam din bata gida ne? Sai kuma duk aka rasa mai magana, daga karshe dai abokin Ahmad ne wanda ya kira kanshi da Usman ya bamu labarin abinda ya kawo su wato sunzo neman Maryam ne domin su roke ta gafara akan yanke hukuncin da Ahmad yayi cikin tsananin kishi saboda makircin da aka hada mata dan a raba su wanda shi kuma baiyi bincike ba ya yanke hukuncin saki a tsakanin su, nan dai suka bamu labarin Ahmad da Maryam sunyi aure ba tare da sanin kowa nasu ba, Inna banda kuka babu abinda takeyi cike da tausayin Maryam, Malam da bai cika fada ba ranar sai gashi ya zage yana ta masifa wulakanta mashi yarinya da akayi bayan an hure mata kunne tayi aure ba tare da sanin su ba kuma har korar cin mutunci aka mata, Ahmad da Usman suka rika bada hakuri amma hakan baisa Malam ya hakura ba, haka suka tashi suka tafi da niyyar zasu sake dawowa idan  su Malam sun huce.
Duk abinda ya faru mutanen gidan mu na sane amma babu wanda ya tanka saima suka nemi su fara juya maganar ta yanda suka so. Saida su Ahmad suka jera yafi kwana goma suna zuwa baiwa Malam da Inna hakuri amma babu wani canji har saisa na fada musu suje su samu aminin Malam din wato Malam Iro su fada mashi abinda kenan shi zai samu Malam din ya masa magana, haka kuwa sukayi daga nan sukai sallama da Malam Iro, basu boye mashi komai ba, shima dai yayi godia ga Allah da yasa maryam ba cikin shege tayi ba, sana ya hau musu nasiha akan rayuwa, duk suka ansa laifin su kafin Malam iro yace musu su bashi kwana biyu kafin su sake dawowa zai yi magana da malam isuhu.
Kwanan biyu na cika suka sake dawowa, anan suka samu tabbacin yafiyar su Malam, tun daga lokacin Ahmad ke tsananin kulawa da mu, shine shan mu shine cin mu shine suturar mu, shine karatun mu domin a lokacin yake fada mana yayi niyyar ya koma kasar waje ya karo karatu amma tunda ya rabu da maryam bai sake samun farin ciki ba hatta auren er uwar shi da yayi baisa yaji wani farin ciki ba, azabar kishi ne ke dawainiya da shi bawai ya dena son maryam ba, yanzu ma hirar abinda hady da salma sukayi ne yasa ya fahimci tuggu suka hada a lokacin shi kuma idon shi ya rufe. A takaice dai Ahmad shiya dauki nauyin karatun mu ni da Hibba ya fidda mu Dubai mukai university din mu bayan mun gama secondary, tun Inna tana dari dari dashi hardai ta saki ta maida shi wani kanin ta suke shiri sosai bare Malam, Ahmad da mu gaba daya bamu fasa addu'ar bayyanar ki ba. Yayin da babu yanda mutanen gidan nan basui ba dan Ahmad ya auri daya daga cikin yaran Inna Fatsima ko we rikon Inna Fulera amma baina san sunayi ba. Ganin arziki ya wadata sosai gare mu yasa suka fara janyo jikin su wajen mu, musamman da rayuwar ta fara juya musu baya, a lokacin ne itama Inna Indo ta rage yawancin halayen ta wata kila ganin yanda duk yaran nata suka bi suka lalace ni oho.
Ahmad shi ya rushe ginin gidan mu ya canja shi haka yanda kika gani, ya kuma gyarawa Malam Iro shima nashi, har Inna Indo ma da mijin ta ya mutu saida ya gyara mata nata gidan, bayan mun gama karatu ne Hibba tayi aure da abokin Ahmad wato Usman yanzu suna da yara uku da Maryam da Raihana mai sunan innar mu sai kuma Ahmad shine dan karamin su, nima na samu mata wata ce mukai karatu tare yanzu muna da yara biyu twins akwai maryam nima dana saka sai Yusuf mai sunan Malam, wannan shine abinda ya faru.
**
Mamy ta goge hawayen da suka fara zuba tunda muhd ya fara maganar Ahmad, ba karamin jin dadi tayi ba ta yanda ya tsaya ya kula da iyayen ta da en uwan ta, lallai ko a haka yaci ace ta yafe wa Ahmad wanda dama ita bata kullace shi ba saboda ta riga da tasan halin sa akan kishi, ko a lokacin tana yawan fada mashi ya rage yawan kishin da yake dashi saidai ya mata daria kawai, a fili ta bude baki ta masa addu'ar alkhairi na abinda yaiwa dangin ta da iyayen ta, gaba daya suka amsa da amin. A lokacin ne akayi sallama aka shigo, su Inna Fulera da Inna Fatsima ne da Amina da Hawwa da suma suka tafi dubo jikin Fatu tare, gaba daya nan suka baje dakin Inna Rahane ana canja sabuwar gaisuwa gami da neman gafara, mamy ta tabbatar musu da babu komai aiya wuce dan Allah Ya basu zaman lafia. Nan suka hau tattaba su Ayisha da Adnan suna fadin masha Allah yara kamar yaran larabawa, wana ne ciki na Ahmad din? Hibba ce ta nuna Ayisha tana cewa gata nan babbar dayan kuma shima baban shi daban amma Allah Ya masa rasuwa, nan sukai addu'ar Allah Yaji kanshi kafin kowa ya nufi dakin shi domin su samu hutu da gajiyar hanya.
Ganin har la'asar amma daga muhd har hibba babu mai shirin tafiya gidan shi yasa mamy tace oya oya ku tashi kowa ya tafi gidan shi hirar ta isa hakanan, idan kuma dan yaran kune to kowa yaja daya ya tafi dashi gidan shi nima yanzu ina bukatar a barni da nawa iyayen, adnan ya shagwabe fuska yace mamy korar mu ma kikeyi to idan nabi uncle muhd ba zaki sake gani ba yanzu sai kinje kinyi biko na, Ayisha ma tace wlh nima abinda zan fada kenan lil bro, basu dai bar gidan ba har zuwan iyalan muhd din da na hibba.
Mamy taji dadin ganin su kowa tsaf dashi ga en yaran su gwanin sha'awa, nan suka kebe ita da usman mijin kanwar ta hibba kuma abokin ahmad, usman din ya fara bada hakuri akan abinda ya faru yake sanar mata lokacin baya nan sadda su hady sukayi abinda sukayi kuma baisan zai jima bai dawo ba ma, mamy tayi murmushi tace babu matsala koda ahmad ya mata laifi to ya wanke laifin shi saboda kulawar da yayi da iyayen ta da dangin ta gashi ta dawo ta same su cikin kamala da jin dadi, kuma naji dadin auren hibba da kayi duk da ka mata tsufa, usman yayi daria yace hibba akwai hankali ai naji dadin daba wani waje ta tafi ba waje na ne, sukai daria su duka sana usman ya fada mata Ahmad baya kasar amma labari ya isar masa na dawowar maryam tare da gudan jinin sa da har yau bai samu ba tare da hadyn da aka sashi aure dole, dan haka yana hanyar dawowa tayi expecting dinsa any time. Mamy tace Allah Ya dawo dashi lafia.
Da kyar mamy ta kora hibba tabi mijin ta da yaran ta zuwa gida amma saida ta wuce da ayisha da adnan, muhd yana cewa gaskia a bashi daya ya tafi dashi shima, hibba tace a'a yaya muhd daga baya su je gidan naku yanzu namu gidan zasu.
Washe gari kamar almara da sanyin la'asar Ahmad yayi sallama gami da sako kai kamar ana ingizashi dakin Inna Rahane, mamy da tasan ko shekara nawa tayi ta dawo ba zata gaza gane muryar ma'abocin zati da kazarniya irin Ahmad ba tayi saurin janyo gyalen doguwar rigarta zata rufe gashin ta dake bude ta dora kan ta bisa cinyar tsohuwa Inna Rahane tana sosa mata kai tana rufe ido, yanda dai takewa Ayisha haka itama yau tata mahaifiyar ke mata, Ahmad yai kuri yana kallon mamy daya tabbata ita ce duk da canjawar da tayi, baya ko kyafta ido yayin da mamyn ta kasa hada ido dashi tayi kasa da kai ta rasa mema zatayi sai Inna Rahane ta lallaba ta shige uwar dakin ta.
Ko sanyi Ahmad yaji kafafun sa sun fara ne oho? Yadai ja ajiyar zucia yace cikin sanyin muryar shi 'maryam why'? Mamy da sai yanzu ta iya dago kai ta kalleshi kafin ta furta 'what do u expect Ahmad? Ta saki ajiyar zucia kafin ta kuma cewa well, kaddarar bawa tana zo masa ne a yanda Allah Ya tsara bawai tsarin bawa ba, and I wasn't thinking straight, all i could think of was how can i leave this town? Ahmad ya durkushe gaban ta yace 'I missed u beyond imagination, dan Allah ki yafe mani maryam... shshsh it's okay Ahmad ni da kai amana ce tun jiya na fadawa usman na yafe maka ko dan kulawa da iyaye na da en uwa na da kakeyi, Allah Ya yafe mana gaba daya. Ameen.
Ahmad yace maryam ina da labari da yawa ta yanda har bansan ta ina zan fara ba amma bara na fara da tambayar ki gudan jini na, mamy tayi murmushi tace Ayisha sunan ta, yawancin halayen ta irin naka ne, tana gidan su usman tun jiya suka gudu dasu, Ahmad yai hanzarin mikewa yana cewa ashe babu zama sai gidan usman, mamy tayi daria kadan tace bama zaka tsaya ka gaisa dasu Inna ba? Ahmad ya dan sosa keya danshi wallahi yana manta da Inna yau dai. Mamy ta kirawo inna su gaisa kafin ya wuce, bayan sun gaisa ne sukaiwa juna barkar dawowar maryam, Ahmad din ya kuma bawa inna hakuri yana tabbatar mata dalilin abinda yaiwa maryam ne yasa maryam din ta kasa zama har saida tabar garin gaba daya. Daga nan Ahmad din yake fadawa inna zaije gidan usman amma zai dawo, mamy ta mike tana yafa mayafinta tace inna bari muje tare sai in gano gidan er kanwata data manyanta ba'a gaba na ba. Ahmad ya sakar mata harara cikin barkwanci yake cewa inna jibeta wai ita har wani girma take ganin tayi sosai ko kuwa dan an fada mani ta aje budurwa da saurayi ne oho? Innar da mamy sukai daria tare kafin su fita waje.
Motoci hudu ne sukaiwa Ahmad rakiya zuwa kaduna bayan saukar shi Abuja, kai tsaye ya fada masu kaduna zasu zo ba gidan shi dake maitama ba, dan haka ganin motocin sai mamy tayi tsaye tana wani dan tunani wanda ita kanta ba zata ga tunanin da take ba, motar tsakiya wani dan sanda yayi hanzarin saukowa yana bude ma ahmad kofa, ahmad din kuma ya budewa mamy kofar kusa dashi, saida ta zauna ya rufe kafin yayi hanzarin zagayawa ya shige inda aka bude mashi.
Ajiyar zucia ta biyo bayan shigar ahmad motar, mamy tace ajiyar zuciyar fa da kake tayi lafia dai ahmad? Yace maryam bazan taba iya kwatanta farin ciki na ba, wallahil azim tunda muka rabu dake ban taba kara samun irin wannan farin cikin da nike ciki ba sai shekaranjiya da usman ya kira ni ya fada mani dawowar ki kuma ma harda gudan jini na abinda nake nema ido rufe, mamy ta kalle shi tace kamar yaya kake nema ido rufe? Ahmad yace I will fill you later, dan yanzu wannan ya zama tsohon zance yanzu maryam ne sabo da tsohon zancan duka, mamy tayi daria tace to ahmad gara dai kana gyara bakin ka yanzu idan ina da aure fa? Ahmad daya damke hannun mamy saida tasa er kara kafin ya sake ta yana huci idon shi harya fara canja launi, yace maryam a kanki ba zan taba dena irin kishi da nake dashi ba dan haka ki kiyaye magana irin wannan koda bayan ido na ne bare gaban ido na, yarinya ta ba zata kara zama ba tare da babanta ba In Sha Allahu, niba ma dan kada inyi butulci ga Allah ba aida nace ko aure ba zai raba ni da yarinya ta ba, dake da ita babu mai kara rabamu. Usman ya fada man komai na abinda ya faru dake bayan barin ki gida kuma ina so ki sani kamar yanda Alh Ahmad ya rike man Ayisha kamar mahaifinta nima zanyi iyakar iyawata inga na rike gudan jinin sa Adnan tamkar nawa dan musanman ma da ni har yau banda yaran saifa yanzu da kika kawo mani abu na.
Mamy dai tunda ta samu ya sake mata hannun ta bata kara gigin magana ba, tana mamakin bayan wa'annan shekarun Ahmad bai canja ba na daga kishin sa, anya rayuwa da irin wannan mugun kishi na Ahmad? Tayi ajiyar zucia tace tunda na dawo babu wanda ya bani labarin abinda ya faru da kai, Ahmad may I have the pleasure of knowing what happened to you in my absence?

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now