Auren sirri 15

162 13 4
                                    

🔐Auren sirri🔐 1️⃣5️⃣

Ranar Monday Maryam ta koma makaranta saidai taje a makare dan har an shiga first period, cikin dari dari ta shiga ajin ta nemi ta wuce ga seat din ta sai jin wata murya tayi an daka mata tsawa gami da cewa get out stupid zaki shigowa mutane aji muna tsakiyar darasi, tun kafin ya idasa magana tuni tayi waje ta samu kasan bishiyar kusa da ajin su ta zauna sai hawaye shaa, a rayuwar ta babu abinda ta tsana irin fada sai taji hankalin ta gaba daya ya tashi shiyasa take jin dadin Iyayen su da basa masu fada sai nasiha da rarrashi. Tafi awa daya tana jiran ya fito ta shiga amma dayake double period ne shiyasa bai fito ba da wuri.
Tun daga nesa ta cikin glasses din shi ya hango ta tayi tagumi ta dena kukan sai idon ta da sukai ja ya tabbata kuka tayi sai haka kawai shida kanshi  yaji rashin dadin abunda yayin, tunda ya fara bautar kasar shi a wancan satin bai taba ganin ta ba sai yau, yasan dalilin ta na makara? Meya kaishi yiwa 'yar mutane tsawa alhalin ba halin shi bane? Kai koyarwar ce gaba daya baya so dan baida yanda zaiyi ne, yayi yayi Baban sa ya nema masa inda zaiyi Service a Abuja amma kiri kiri Baban yaki acewar sa shi namiji ne dan haka ko duk inda aka kaishi service nan zaije da haka zai saba da rayuwa a duk yanayin da ya samu kanshi. Tunda ya fara koyarwar ya zama wani masifaffan karfi da yaji kullum cikin hantarar yaran mutane yake yana kiran su dakikai, laifi kadan zai zage ki koya kore ki daga ajin ya kuma biki da harara da tsaki gani ma yake kamar laifin yaran ne.
Har ya gitta ta gefen ta yana wannnan en tunane tunanen, saida maryam ta tabbatar daya wuce sana ta lallaba ta shiga ajin. Babu wani bata lokaci wani malamin ya shigo suka ci gaba da karatu.
Basu samu lokacin hutu ba sai da aka kada break sana duk 'yan ajin suka fita sai itace karshen fita, wajen da ake en saide saide taje ta siyo ruwa ta dawo ajin su ta zauna ta dauki biro taci gaba da copying notes da akai bata nan na wancan satin, wajen seat member dinta Fatima ta ansa. A hankali en ajin suka fara dawowa daga break anan Fatima take bata labarin sabon Malamin su. Not interested ta kada kawai tace Allah Ya sawake Fatima, daga haka itama Fatiman taja bakin ta ta tsuke.
Tun sadda Ahmad ya fito daga ajin su Maryam ya kuma hango ta zaune tayi tagumi ya kafa mata ido har ya shige staff room amma gaba daya ya rasa nutsuwar shi yarinyar ce keta dawo mashi a idanun shi, kyakykyawar fuskarta yake hangowa cikin yanayi na damuwa, bazai iya cewa ga halin da yake ciki ba amma ya tabbatar da baida nutsuwa tun sanda ya mata kyakykyawan gani cikin halin damuwa.
A haka lokaci yaja lokacin break yayi har aka dawo yana nan zaune bisa kujerar shi, kasancewar shi marar barin abu ya dame shi sai tsulum ya mike kafin ya ankare kafafun shi sun kawo shi ajin su Maryam, jin shirun da ajin yayi Maryam ta dago kai daga rubutun da takeyi ganin malamin dazu ne sai ta tsora ta ta nemi gyara zaman ta sai gani tayi yana yafito ta da hannu alamun tazo, jiki a sanyaye ta mike ta biyo shi har zuwa gaba kadan daga ajin su, ganin ya tsaya itama sai ta tsaya amma gaban ta faduwa yakeyi sosai.
Menene sunan ki? Kamar daga sama taji yana tambayar ta, tayi hanzarin ansawa da Maryam Yusuf, ya kuma cewa ya akai kika makara yau? Nan ma tai hanzarin ansawa mashin din da muka hau ne ya lalace a hanya sai daga baya ya tashi shiyasa na makara, Ahmad ya saki murmushi ya samu kanshi da cewa kiyi hakuri dazu na maki tsawa da fada, cikin sauri Maryam tace babu komai Malam. Sukai shiru na wani dan lokaci kafin Ahmad ya nisa yace shikenan kina iya komawa aji Maryam, sai a lokacin ta daga ido ta kalle shi tsaf kafin ta saki murmushi tace nagode Malam gami da juyawa cikin nutsuwar ta ta wuce aji.
Ahmad ya bita da ido harta shige ajin kafin ya saki huci ya wuce staff room cike da tunanin yarinya karama irin Maryam wanda a ganin shi duk zagaya kasashen waje da yakeyi shida iyayen shi da en uwan shi bai taba ganin mace ya Maryam ba, har kuwa a USA dayai karatun shi na gaba da secondary shidai a ganin sa baiga mace ya Maryam ba.

Tun daga wannan rana Ahmad ya tabbatar da wani irin mugun son Maryam ne ya kama shi, sai ya rasa yanda zaiyi, bakin cikin zuwan shi kaduna ya yaye aka kuma denawa dalibai tsawa da fada sai fara'a duk inda zaka ga Ahmad, a hankali ya rika jan maryam a jiki ya ribace ta akan taimaka mata da karatu tunda wannan shekarar zasu gama karamar sakandire, da wannan Maryam ta saki jiki da Ahmad suke hira sosai ta saba dashi hatta a gidan su saida suka sanda labarin Uncle Ahmad kamar yanda take kiran shi, Inna ta ja mata kunne koda wasa bata yarda ta kebe dashi inda ba jama'a ba kuma ta kara kama mutuncin kanta.
Maryam yarinya ce karama da bata san wani abu waishi so ba amma a zahiri duk wanda ya santa ya kuma ga yanda take da Ahmad kai tsaye mutum zai ce Maryam tana cikin mayen so ne kamar yanda gogan Ahmad yake ciki, wannan ba karamin dadi yayi ma Ahmad ba amma sai bai hankaltar da ita ba har aka dauki tsayin lokaci.
  Sun saba sabo mai wuyar baruwa, sun shaku sosai fiye da tunanin mai karatu komai na Maryam saida Ahmad ya sani hatta gidan su Maryam da tafiya tai tafiya saida yaje yaga iyayen ta da kannin ta ya kawo alheri ya ba Malam Isuhu amma kiri kiri Malam Isuhu ya maida ma Ahmad abunshi yace a'a ya gode dole Ahmad ya maida kudin shi yana kara jaddada halin iyayen maryam, lallai su basu da shi amma suna da godiyar Allah ga dattaku da karamci kamar ace su din mutanen Katsinawa ne.
Hankalin Ahmad bai fara tashi ba saida aka shiga zangon karatu na uku wanda babu jimawa su Maryam zasu fara exams na gama karamar sakandire, shi kuma zai koma gidan su dake Abuja shikenan ya gama bautar kasar shi. Idan Ahmad ya tuna da hakan sai gaba daya hankalin shi ya tashi a haka ya sanar wa babban abokin shi Usman, Usman din ya bashi shawarar tunda yana son Maryam ya fito ya gaya mata duk da tayi karanta kuma ya fito neman auran ta, Ahmad yai shiru kafin yace Usman ka fini sanin babu batun aure yanzu a gabana muddin buri na na siyasa yana nan ko? Gashi kuma bazan iya hakura da Maryam ba dan haka ka bani wata shawarar mana, sai sukai shiru kafin Usman yace 'kaje ka fara fadawa Maryam son da kake mata tuku na kafin nan zamu nemo abinyi', da wannan Ahmad ya samu Maryam har gida ya warwarewa yarinya karama sa'ar kanwar sa cikin sa akan son da yake mata tun sanda ya fara ganin ta.
Maryam ta rufe fuska tana daria cikin jin kunya sai kuma ta gudu zuwa gida, Ahmad ya kira Usman ya masa bayanin yanda sukai da Maryam sai Usman din ya kama daria yace babu wahala aboki na yarinyar ma tana son ka kuma tana da wayo da alama duk da kace karama ce dan haka yanzu kasha soyayya na dan lokaci kafin mu samo babbar mafita da wannan sukai sallama.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now