Auen Sirri 33

167 15 19
                                    

🔐Auren sirri🔐 3️⃣3️⃣

Kwanan su uku da dawowa suka fara shirin komawa Abuja, ana gobe zasu tafi da dare suna zaune falo su duka suna hira sai Daddy da bayanan yaje yiwa wasu mutanen shi sallama, Nadia da Maman ta suka shigo falon, kowa ya bisu da kallo fuska a daure sai Ayisha kadai daba zakayi saurin cewa ga yanayin da fuskar ta take ciki ba, Nadia ta fara gaishe su abinda bata taba yi ba a tarihin rayuwar ta, babu wanda ya kula daya amsa gaisuwar na ta, Maman Nadia ma ta kalli mummy tana gaishe ta saidai tun kafin ta ida gaisuwar mummy ta tsaida ta tana cewa ya isa hakanan Adama gaisuwa ki rike abin ki bana bukata, abu daya da nake bukata wajen ki yanzu shine ki tashi ki ja diyar ki ku fice min daga gida bana bukatar ganin ku, na riga dana fito daga cikin duhun da kika saka ni, yanzu haske ne a idanu na, tashi maza ku fice man daga gida kafin insa ayi muku korar karnuka, maman nadia da alama ranta ya baci dama gata da saurin fushi sai itama ta nemi ta hayayyako wa mummy, dan nazo gidan ki Laurat shine zaki wulakanta ni kin manta koni wacece? Kin manta yanda muke ni da ke? Dama ke butulu ce? Duk alkhairan dana maki a baya... cikin zafi mummy tace alkhairai ko sharri Adama? Aike tauraruwa ce mai wutsiya ganin ki ba alkhairi bane, nadia dake ta kuka tana fadin dan Allah maama kibi a hankali kada kija mani king yayi fushi ki dena yi musu fada... Maman Nadiyar cikin tsananin fushi ta daka mata tsawa tana cewa to sai mi? Idan ya rabu dake mutuwa zakiyi? Nace mutuwa zakiyi? Ko shi ka dai ne namiji a dunia? Nadia dai tana kada kai alamun kiyi hakuri kada kija mani maama, yayin da maman ke kara harzuka.
Suna cikin wannan hayaniyar ne king ya zame ya wuce dakin shi, babu wanda ya lura da tafiyar sa sai Ayisha kuma saida tayi tunanin ta bishi sai wata zuciyar ta hana ta, bai jima sosai ba ya dawo kai tsaye wajen nadia ya isa yasa hannu a aljihu ya fiddo da takarda ya mika ma nadia, nadiyar tana ta kada kai alamun a'a ba zata iya amsa ba tana kuma kuka, king yace kiyi hakuri nadia amma rayuwa ta da taki akwai banbanci sosai kuma bamu dace da juna ba tako ina, yayi nuni da hannun sa inda Ayisha take yaci gaba da cewa kinga waccan wato Ayisha itace wacce nake fatan na karashe rayuwa ta tare da ita a matsayin mata ta, itace komai nawa dan haka kiyi hakuri kije na sake ki saki biyu kuma ga takarda nan idan kin bude ma saki biyun zaki gani, nadia ta hau ihu da kururuwa tana cewa Mu'azzam kayi mani rai dan Allah badon hali na ba wallahi nima kai ne komai nawa kuma nima da kai nake so in karashe rayuwa ta, wallahi zan canja halaye na amma dan Allah kayi hakuri kada ka rabu da ni, ina zansa kai na idan ka rabu dani? Ina zan kai soyayyar da nake maka? Wane da namiji zan iya baiwa wannan soyayyar da nake maka? King yace ina kara baki hakuri Nadia, ban manta zaman amincin da mukai ba lokacin karatun mu, kuma harga Allah ina tausaya maki amma nasan kamar yanda maman ki ta fada ne wato idan na rabu dake ba mutuwa zakiyi ba wannan gaskia ne kuma zaki iya samun namijin daya fini komai dan haka ina kara baki hakuri, daga haka king ya juya da nufin barin wajen Nadia amma tayi kamkam da kafar shi tana wani irin gunjin kuka, tsakani da Allah nadia tana son king so mai yawa.
Maman Nadia ta kama jan hannun Nadiyar cikin fusata tana cewa ba zaki sakar mashi kafa ba dan uban ki? Tunda yace baya yi ana dole ne? Ko wani mijin zaki rasa ne dan kin rasa wannan fitsararran? Nadia ta buge hannun uwarta tana cewa duk abinda ya same ni maama ke kika ja mani, kuma ran ki yayi haske yanzu kamar yanda mijin ki ya rabu dake nima kinyi sanadiyar rabuwata da miji na, sai kuma ta cakumi uwar cikin fitar hayyaci tana cewa cikin daga murya maama mena maki baki bani tarbiya mai kyau ba? Mena maki kika lalata mani rayuwa? Meyasa baki so na? Meyasa ba zaki bani abinda nake so ba? Mutuwa zanyi mama.... Cikin wani irin kuka maman ke girzgiza nadia tana fadin 'nadia ki dawo hayyacin ki dan Allah nadia ki rufa man asiri kada wani mummunan ciwo ya kama mani ke, ni kadai ma na ishe ki rayuwar dunia domin nike son ki marar iyaka, amma kafin maman nadia ta ankara tuni nadia ta kai kasa tana buga kanta akan tiles.
Gaba daya falon babu wanda ya tanka musu da alamun ma babu wanda yaji tausayin su, amma acan gefe idanun Ayisha sun cika taf da hawaye na tausayin nadia, harga Allah ta fahimci nadia da gaske tana son King, to amma ita meye nata da zata saka baki? Sai kawai ta mike ta nufi dakin king din ba tare da tasan me zatayi ba, sai dai tana shiga king na biyo ta, yayi saurin riko ta ta baya gami da bata back hug yana sakin ajiyar zucia yace Ayisha what's wrong? Ayisha tayi kokarin cewa babu komai babe kawai naji tausayin nadia ne amma duk yanda zan so ta ai baikai yanda zanso kai na ba kuma yanda take jin son ka ni nafi ta son ka, amma bansan meyasa nake jin tausayin ta ba, tunda nasan babu abinda zan iyayi shine naga bari kawai in bar musu wajen idan sun tafi na koma, king yace Allah Ya bata wani wanda ya fi ni, daga haka suka ci gaba da faranta ran junan su, basu kuma san yasu nadia suka kare ba sai da safe da suka je wajen breakfast ne suke jin Amal na fadawa Daddy abinda ya faru suma anan suka ji karshen yanda akai su nadia suka tafi, ashe suma tayi daga karshe, maman ta da drivern su suka dauke ta sukai mota da ita daga nan basu san ya suka kare ba su ma, Daddy ma cikin tausayi yace Allah Ya kyauta kuma Allah Yasa hakan shi yafi alkhairi, kowa yace ameen.
Suna kan hanyar airport ne Daddy ya kira baban nadia bayan sun gaisa daddy ya sanar da shi abinda ya faru jiya a gidan shi bayan bayanan ya karashe da fadin nima yau da safen nan akw fadaman abinda ya faru jiyan, shine nace bara na sanar da kai kuma in roki alfarmar ka domin Allah! Dan Allah!! Dan Allah Alhaji kayi hakuri ka sassautawa nadia da mahaifiyar ta ka dawo dasu rayuwar ka ka tallabe su ka rage musu zafin da suke ji a zukatan su, kai ne bangon su majinginar su, kuma tsakani da Allah Alhaji ni da kai duka munsan muna da hannu cikin halin da iyalin mu suka tsinci kan su, mun riga da mun basu so mai yawa ba tare da sa ido akan rayuwar da suke yi ba, to me yasa yanzu dan sun kauce hanya ba zamu dawo dasu kan hanya da irin son da muka nuna musu a baya ba? Kaje kayi tunani Alhaji Abubakar ina fatan jin sakamako mai dadi daga gare ka, baban nadia yaja doguwar ajiyar zucia yace nagode Alhaji Ibrahim kuma In Sha Allahu zanbi shawarar daka bani, duk randa Allah Yasa na shigo Abuja kuma zan neme ka, da haka suka aje waya suna wa juna fatan alkhairi.
Sunyi landing a Abuja wajen karfe daya na rana sakamakon delaying din flight da akayi, Alhaji Ahmad da Mamy da Muhammad kanin Mamy sai Adnan su sukaje taryar su, suna fitowa arrival Ayisha taci karo da Adnan suka rungume juna Adnan yana fadin surprise Sis, daga nan ta rungumi Mamy kafin ta isa ga Abba, ya bude hannuwan sa duka Ayisha ta shige tana fadin nayi kewar ka Abba, Shima yace nayi kewar ki matar Mu'azzam, su daddy sukai daria, Mamy ta isa ga mummy tana mika mata hannu tana mata sannu da zuwa sana tabi su Amatullahi, Amira da Amal duka ta rungume su tana musu sannu da zuwa, Muhammad ma ya karasa yana gaishe da daddy, daddy ya mika masa hannu yana cewa babu musabaha sai gaisuwa ne Muhammad? Abba na daria yace waya sani ko surukuta yake so ya fara nunawa? Cikin sakin fuska daddy yace surukuta bata hana a samu ladar musabaha dan haka ka dena daga yau.
Bayan an gama loda kayan su cikin motocin da Abba yasa aka biyo su dasu domin daukar su daddyn sana suka nufi barin airport din, sun isa maitama Ayisha nata fadin wash wash ni wallahi na gaji sosai, Amal tayi tsulum tana cewa ba dole ki gaji ba da wannan katon kan babyn naki dake cikin ki, sai kowa ya bi Ayisha da idanu, ita kanta Ayishan sai ta tsaya tana kallon Amal tace ban gane ba, Amal tayi daria tace zaki gane ne, mummy ta kalli Amal babu was a fuska tace ke bana son wasa da gaske kike yi ne? Taya akai mu bamu gane ba sai ke? Amal na daria tace saboda kun tsufa idanun ku sun daina gani sosai ni kuma yarinya ce sharaf kuma Doctor dan haka ku fara shirin taryar masu hargitsa maku gida, sai hamdala tako ina kake ji suna fatan maganar Amal ta zama gaskia idan anyi test, king kuwa ko kifta idanu baya yi yake kallon Ayisha, har kunya ta kama ta ta rada mashi babe kallon fa? Yace I am out of words dan sai nake ganin duk abinda zan fada bazai taba kai yanda nake ji a zucia ta ba, Allah Ya maki albarka, Allah Ya albarkaci zuri'ar da zamu samu, Allah Ya faranta maki rai yanda kike faranta mani rai, Allah Ya bamu yara nutsatstsu, Ayisha ta lumshe ido cikin jin dadin addu'ar da yayi tace thank u babe.
Daddy ashe duk yana kallon su yayi tsoki cikin wasa yace yaran yanzu basu da kunya Alhaji Ahmad, Abba yace da sukai mi? Mamy ta amshe da cewa ai nima daddyn riga ni fada yayi dan nima ina kallon su, mummy da abba suka hada baki wajen fadin ku barsu suyi murnar su lokacin su ne. Daga nan masu aikin mamy suka ci gaba da kawo abincin da sukayi dan taryar bakin kasancewar gidan Abba suka sauka,  suna gama cin abinci ana fara kiran salla dan haka Abba, Daddy, Muhd da Adnan da king suka mike da nufin zuwa masallaci, Mummy kuma tayi cikin dakin Mamy ita da mamyn, Ayisha da su Amal kuma suka nufi dakin Ayisha na da wanda yanzu ya zama na saukar baki.
A dakin Mamy bayan sun gama salla ne mummy tayi kasa da kai tana tunanin taya zata fara neman afuwar mamyn, can dai tayi shahada ta furta abinda ke ran ta 'Maryam ki dubi Allah da Girman Sa ki yafe mani laifukana, na gane kuskure na dan Allah kiyi hakuri ki yafe mani, mamy tayi murmushi tace wallahi ban taba rike ki a rai na ba dan haka na yafe maki Allah Ya yafe mana gaba dayan mu, mummy tace nagode sosai. A can kuma dakin en matan Amira da taga karshen kanwar su na waya da Muhd tana ta fara'a da alamun wayar ta mata dadi sai take jin inama itace ashe itama Amatullahi abinda ke ranta kenan dan haka Amal na gama wayar ta sai Amatullahi tace anya ba gidan nan zan zauna ba kuwa nima? Amal da kuwa kinji dadin da baki taba ji ma na zama da mutane saboda karramawar mutanen gidan nan ta wuce duk inda kike tunani, Amira tace idan haka ne nima zanso in zauna da su koba dan komai ba dan nima in samu miji mai mutunci irin mutanen gidan da ahalin su gaba daya, Ayisha tayi daria tace gaskia zaku ji dadin zama da mamy amma fa zata rika saka ku shiga kitchen ku kuma na lura kamar baku so, Amira tace indai zan samu mijin nan wallahi duk abinda mamy tace inyi shi zanyi, Amatullahi tace ni dama ina da son abinci dan haka dan na koyi girki aiba laifi bane, Ayisha kiyi wa mamy magana idan ta amince to, Amal tace ashe dai zamu zo mu rika cin girkin manyan yayyen mu, sukai daria su duka.
Basu tashi tafia gidan su Daddyn ba sai bayan da sukai salla Asr sana suka nufi can amma tuni Abba yasa an kai luggages din da suka dawo dasu daga Lagos kasancewar drivers din sun san gidan, Amira da Amatullahi sai yaba garin sukeyi da weather garin, saida su mummy suka fara shiga gidan su king dake farko cikin gidajen shida dake compound din, sunata sa albarka, kafin suka fito suka shiga nasu gidan mai kama da gidan matashiyar amarya inji mamy, sukai daria su duka, gidan yayi kyau sosai. Bayan sun gama ganin gidan sun dawo falo ne Ayisha take fadawa mamy batun sabbin 'ya'yan data samu ai mamy baki har kunne take fadin taji dadi Allah Ya taya ta riko, Allah kuma Ya basu mazaje na kirki, Amira ta kalli mummy tace sorry mummy bamu fada maki ba ina fatan zaki amince? Mummy tace babu damuwa aiga Ayisha da King kusa da ni kuma suma su Mamyn aiba nisa ne dasu ba sosai tunda ta bayan mu ne suke, fatana Allah Ya kara hada kanmu duka, gaba dayan su suka amsa da ameen.
Basu bar gidan ba har aka kawo abinci daga gidan mamy sukai dinner sukai salloli duka har wajen karfe tara na dare sana Abba yace to zasu tafi sai kuma sun sake dawowa yi musu ya gajiya da bakuntar sabon waje, Amira da Amatullahi suka ce suma gobe suna nan tafe idan suka fitar da kayan su da aka hade cikin kaya, king da Ayisha ma sukai nasu gidan.
Washe gari kamar yanda Amira da Amatullahi suka fada hakan ya faru, da yamma king ya sauke su gidan su Mamy tare da tulin akwatunan su, adnan da masu aikin gidan suka shigar musu da kayan har dakin su wanda aka kara gyawa saboda zaman su, tun a ranar mamy ta fara jansu kitchen aka hada dinner dasu akai setting dinning table da su, gashi mamy ta sakar musu fuska sosai tana jansu wasa, dan haka da wasa da daria akai komai aka gama sana suka tafi suyi wanka sai suzo aci abinci gaba daya inji mamy. Mamy da Abba ne karshen zama dinning din bayan sun gaishe da Abban kasancewar tunda suka zo basu samu ganin shi ba sai yanzu ya dawo gidan, Abba ma ya kara ja musu kunne akan rayuwar dunia ya musu nasiha ya kuma yi addu'a akan Allah Ya zaunar da su lafia cikin aminci, bayan sun gama cin abinci Abba yake tambayar su game da karatun addini, saidai kamar yanda ya zata hakan ya faru dan haka yace musu tunda su basu aiki basu komai to malamin adnan zai rika zuwa daga karshe daya na rana yana koyar dasu har zuwa sadda Adnan zai tashi school ya canje su, Abba yace idan kuka maida hankali zaku ga abin yazo muku da sauki, Amira ta goge hawaye tana cewa mun gode Abba kuma In Sha Allahu zamu bi duk abinda kuka ce kodan mu ma rayuwar mu tayi kyau, har daki saida mamy ta raka su tayi hugging din su tana musu saida safe, ta saita musu alarm da zai rika tada su sallar subh tace koda yake zan rika shigowa da Asuba din ina duba ku, da haka ta musu saida safe.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWo Geschichten leben. Entdecke jetzt