Auren sirri 06

285 16 0
                                    

🔐 Auren sirri 🔐 6️⃣

Gaban Momy ya fadi tare da maimaitawa a ranta Ayeesha! Cikin nauyin baki Momy tace 'king wacece Ayeesha? Meke damunta da kaima kake cikin damuwa irin haka saboda damuwar Ayeesha? Cikin raunanniyar murya king yace 'Momy tare muke karatu da ita, dalilin tane na koma school ina neman degree na biyu, ita ce tun ranar dana fara ganin ta naji bana da nutsuwa, dalilin in rika haduwa da ita kullum yasa naiwa Daddy magana na koma school neman degree na biyu wanda ko ita duk tarayyar mu bata sani ba, kuma baku sani ba sai yanzu da nake fada maki, Momy ina son Ayeesha, Momy ku aura man Ayeesha ita nake so...
Momy data saki baki tana sauraran King amma ganin kamar ma baya hayyacin shi ga wani bacin rai daya taso mata saboda ita a rayuwar ta tana kishin danta namiji guda daya da Allah Ya bata ace yana son wata mace irin wannan tsananin son data lura take kuma sauraro yanzu yana amayar mata da abin da ke zuciyar shi, tafi bukatar macen taso King ninkin yanda shi zai so ta saboda a tunanin ta inda yafi son mace to za'a iya raba su gashi Allah Yasa tana tsananin son King cikin yaran da Allah Ya bata wanda a fili ne kowa ya sani tafi son shi da kulawa dashi, ko Nadeeya ganin itace ke haukan son King shi baya damuwa da ita shiyasa Momy ta amincewa alakar kuma koba komi tana da burin King yayi aure gidan manyan mutane wato masu kudi a gare ta, kuma akaci sa'a  Nadeeya ta fito daga irin wannan gidan, duk da dai suma kudin suna da su nesa ba kusa ba, to ita ina tayi sake da har King yake son wata mace irin wannan son? Cikin fushi ta katse shi da tsawa gami da cewa 'kai saurara min bana son batun banza dana wofi, duk yanda kake ganin ina son ka ina maka abinda kake so anan gurin zamu saba nida kai, kananan mutane kake so ka mayar damu ko mene? Ita Nadeeyar fa? Me zaka fada mata da iyayen ta? Batun auren ku da ita fa wanda muka kulla kusan shekaru uku da suka wuce fa?
Cikin sanyin jiki King yace 'Momy tunda nake daku da ita Nadeeyar wani cikin ku ya taba kuskuren jin nace ina son Nadeeya?.. Momy ta kuma katse shi da cewar 'naji baka taba furta kana son Nadeeya ba amma zaka fada min bada amincewar ka muka kulla batun auren naku da ita ba? Murya a sanyaye king ya ansa 'da amince wata ne Momy, amma ko a lokacin saida na furta maku keda Daddy na amince da batun kuna so na auri Nadeeya amma duk sadda na samu wacce nake so to zan aure ta, Momy kin tuna a lokacin ku duka kuka ce kun amince da batu na?
  Momy tace 'yanzu a takaice me kake kokarin sanar dani? Bata ko rufe baki ba King yace 'na fasa auran Nadeeya ni Ayeesha nake so kuma nan da en watanni zamu kammala karatun mu kafin nai sai ayi maganar auren. Momy tace 'to baka isa ba kuma kayi kadan kasa muyi karamar magana, Nadeeya ce gata can ka aure ta ka gama, idan anyi auren ka yankata gunduwa gunduwa tsabar kiyayya, bata jira komi ba ta juya fuuuu tayi waje tabar King da dafe kai.
**    **
Gefen Ayeesha kuwa ba karamin kokari tayi ba ta kawar da damuwar ta ganin yanda Adnan ya kasa sukuni bare Mamy data dawo daga aiki sai duk suka bi suka tare dakin ta, ganin yanda suka damu yasa itama tai kokarin kawar da damuwar ta sukai ta hira wanda hakan yasa har a ranta taji dadin hakan kuma damuwar tata ta ragu sosai. Da dare bayan kowa ya kwanta ta lallaba ta kunna wayar ta data kashe, ta danna number King. Kamar jira yake taji ya ansa 'Hello babe ya kike? Ayeesha ta kakaro dariya tayi gami da cewa 'anya kuwa king ba zaka ragawa kanka ba? Bana son kana shiga damuwa, king yace 'it is simple kema ki dena shiga damuwa nima sai in daina kuma ma meya hanaki zuwa school yau? Ayeesha tace kaina ne yayi ciwo amma da sauki dan haka gobe zanje school saimu hadu acan ko? King yace banu damuwa kuma idan mun hadu zamui magana dake akwai abinda nake son sanar maki wanda na kasa sanar maki duk tsayin lokacin nan, yanzu ina kyautata tunanin lokacin sanin nashi ne yayi.
Ayeesha tace toba damuwa idan mun hadu sai muyi maganar kuma nima dazu Mamy take fada mana nida Adnan tana ganin zata aje aiki wai tana so mu koma kasar ta ta haihuwa amma indai mun hadu zamui magana kada kasa damuwa a ranka kaji, a haka sukai sallama kowa da abinda yake sakawa a ransa.
King dai ya kwana yana tunanin idan ya sanarwa Ayeesha komai batun Nadeeya ya zata yi? Sana idan ya sanar mata dalilin ta ya shigo school a karo na biyu neman degree na biyu shima ya zataji? Sana bazai iya boye mata batun Momy ba duk da dai baiji ta side din Daddy ba to shima ya duk zata ji? A haka bacci ya sace shi.
Yayin da Ayeesha ta kwana da tunanin meye damuwar Mamy?  Dama kusan wata daya kenan data lura Mamy na yawan tunani amma idan ta tambaye ta sai tace babu komai, ita kuma bata son damun ta shiyasa saita kyaleta, sana tayi shekaru tana tambayar Mamy meyasa suke rayuwa su kadai, daga Mamy sai ita Ayeesha sai Adnan? Sai Mamyn tai murmushi tace saboda su kadai suke da junan su nan ba kasar su bace amma wata rana zasu je kasar su, sai Ayeeshan tace to Mamy ina ne kasar mu? In Mamy ta ansa bai wuce kasar mu nada nisa Ayeesha kuma wata rana zamu je kada ki damu, sai Ayeeshan tace to Mamy mu tafi mana yanzu, Mamyn takance lokacin zuwa baiba Ayeesha amma ya kusa, Ayeesha bata gajiya da tambayoyi dan haka saita kuma cewa Mamy yaushe ne lokacin ya kusa? Mamyn tace idan kin girma kinyi karatu kinyi aure sai muje,  sai Ayeeshan ta bata rai tace Mamy ai kince idan mace tayi aure saita tafi gidan Mijin ta zata bar iyayen ta da en uwanta ni kuma babu inda zanje inbar ki da Adnan. Mamyn takanyi murmushi tace to Ayeesha yanzu baki da wayon sanin aure sosai amma idan kinyi girma sosai zaki fahimta da kanki.
  Ayeesha taja doguwar ajiyar zucia, kanta fa ya cushe, meyasa yanzu rana tsaka Mamy ta musu maganar zuwa kasar su? Ina ne kasar tasu ma? Dazu cikin maganganun Mamy lallai taji inda tace 'saboda halin rayuwa na canja tunani Ayeesha na karashe karatun ta zamu tattara mu koma kasar mu, na fasa batun sai Ayeesha tayi aure kuma koba komi yanzu hankali na yayi gida sosai. Ina son sanin halin da iyaye na da en uwa na suke ciki. A haka bacci ya sace Ayeesha.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now