Auren Sirri 26

133 15 7
                                    

🔐Auren sirri🔐 2️⃣6️⃣

Ahmad ne yayi wa Malam Isuhu maganar sake daura auran su shi da Mamy, Malam yayi addu'a cike da farin ciki kafin yace to ya sanarwa iyayen sa dan su zo. Ahmad ya kira Umman su babu bata lokaci yayi mata bayanin abinda ke faruwa, ita jin batun Ahmad da gaske dai yana da diya ma kadai ya isa ya sata farin ciki sai kawai ta hau addu'a tana cewa babu bata lokaci tunda duk an amince sai kawai iyayen sa maza suzo a daura auran ya dauko mata jikar ta ya kawo ita shine bukatar ta dan haka ta kashe wayar ta kira baban su Ahmad din shima ya zayyana masa abinda kenan, shima yayi farin cikin batun Ayisha dan haka yace gobe goben nan zasu tafi kaduna ayi a gama tunda dukan su ba yara bane kuma duk an amince da batun, kafin kace me? Suka hau buga waya suna fadar daurin auren Ahmad din, a haka labari ya iske hakima hady, hauka da buge buge babu wanda hady batayi ba, zage zage dai tayi shi kamar babu gobe tana kuma shan alwashin yanda taga bayan wancan auran nasu haka ma yanzu sai taga bayan wannan auran, wato shi yasa daya dawo baiko biyo nan ba ya dauki hanyar kaduna, data rasa me ma zatati sai ta kira salma ta fashe mata da kuka da kyar salmar ta samu hady ta hada mata en bayanan da zata iya cewar Ahmad zai sake auren Maryam.
Salma ta ja ajiyar zucia tace hady nifa na daina ja da ikon Allah dan ina tabbatar maki karshen ta sai na hadu da Maryam da Ahmad na roki su yafe mani saboda abinda na musu, dan yanzu haka ina gidan mu bana gidan miji na kishiya ta kore ni kuma exactly abinda mukai wa Maryam shi aka mani yanzu shiyasa nake tabbatar da cewa hakki ne ke bibiyata dan haka idan shawarar kirki kike so in baki to Hady kiyi hakuri ki karbi Maryam da hannu biyu ku zauna lafia shi yafi, in ma kina iyawa ki nemi ta yafe maki hakkin ta dake bibiyar ki... Hady da idanun ta sunai kanana saboda azabar masifar kishi ta dakawa Salma tsawa tace dalla dakata mani salma, bangane in zauna da wata mace a matsayin matar Ahmad ba, to ina tabbatar maki ko zan tafi tsirara sai na sake raba Ahmad da tsinanniyar matar nan, bazan taba bari su zauna lafia ba bare shegiyar diyar da aka ce suna da ita, salma na kokarin yin magana amma tuni hady taja tsaki ta kashe wayar gami da kiran wata kawarta da suka hadu shekarun baya bayan nan, hady bata rage komai ba tana kuka tana sanarwa Hajia Rabi halin da take ciki, Haj Rabi ta saki uban ashar tace kinzo wajen Hajia Hadiza indai ina raye babu uban daya isa ya hada ki da wata macan saidai idan babu bokayen kan dutse dan haka gobe goben nan ki shirya mu nufi garin yarbawan nan, bari in kira waya ayi mana booking ticket na Lagos, ki kwantar da hankalin ki domin kuwa da kafafun ta zata gudu ta bar maki Ahmad.
Ko bayan gama wayar su da hajia rabi bata wani samu salama a zuciyar ta ba dan babu abinda idon ta ke hange daya wuce Ahmad da Maryam sai kuwa diyar su, a haka ta rika kiran Ahmad amma baya dauka, daya lura dame shi da kira shine ya rufe wayar gaba daya ma, wanda yin hakan ya kara rikita hady sosai, sai kawai ta shirya ta nufi gidan hajia rabi can ta zube mata tana risgar kuka kamar karamar yarinya, hajia rabi ta rika lallashin ta da kalamai na kwantar da hankali akan cewa ta kwantar da hankalin ta dan inda zata kai ta aikin bokan kamar yankan wuka ne, kuma dama itama tana so taje saboda ta lura nata mijin kamar ya fara dage mata kai to itama tana cike da shi, dan haka tayi kwanciyar ta a nan gidan gobe da safe sai su wuce Lagos.
Bangaren su Ahmad kam banda tsabar farin ciki babu abinda ke gudana, ji yake kamar ya jawo gobe iyayen shi suzo a maida auren sa da sanyin idaniyar sa, dama masu ita magana sunce soyayya bata tsufa saidai masoyan su tsufa, idan mukayi duba ga Ahmad da Maryam dai to zamu iya cewa wannan gaskia ne, domin ita kanta Maryam din harga Allah a can kasan ranta tana jin dadin hakan amma bata so ta nuna ne sosai, harga ran en gidan su sunji dadin hakan kuma suna farin ciki da faruwar hakan.
Washe gari iyayen Ahmad suka zo babu bata lokaci aka maida auren Ahmad da Maryam, anan kuma aka hau gaisuwa ana murnar hakan daga bangare duka biyun, aka kira Ayisha da Adnan domin suka iyayen Ahmad, Tsoho mai ran karfe wanda idan kallin jikin sa zaisa ka fadi shekarun sa to lallai mutum bazai gane ba, saboda kyawun jikin sa Alhaji Aliyu Mainasara ya rungume Ayisha yana farin cikin kasancewar ta jikanyar sa, ya kamo hannun Adnan ya rike yana ta shi musu albarka. Har cikin gida su Alh Aliyu Mainasara wato mahaifin Ahmad suka shiga wajen iyayen mamy matan aka gaisa gami da kara neman afuwar abinda ya faru na auran da sukayi babu wanda ya sani. A haka dai aka rabu cikin mutunci ana jin dadin abinda ya faru, a ranar saida Ahmad ya san yanda yayi ya kebe da Mamy a gidan Hibba da Mamyn taje ansar wasu kaya wajen Hibbar, ashe sun hada baki akan cewa Ahmad din ya jira Mamyn a dakin tunda ya musu complain akan taki kula shi banda gaisuwa babu abinda ya hada su.
Mamy na shiga dakin da niyyar bude wardrobe sai ji tayi anyi mata wata tsatstsaurar rungumar data firgita ta, Ahmad ya rada mata a kunne shine, Mamyn ta saki ajiyar zucia kafin kuma ta turbine fuska kamar karanar yarinya tace Ahmad yadai a gidan mutane... Ahmad ya katse ta da cewa gidan Hibba da Usman ba gidan mutane bane a waje na kuma su suka bani damar jiran ki a cikin dakin, mamy na meyasa baki kulani ba duk na damu, mamy tayi murmushi gami da cewa dama saboda wannan ne ka biyo ni har nan? Bata jira ansar shi ba taci gaba da cewa ina jin kunyar mutane kar suka nima na biye maka babu ko kunya, Ahmad ya saki ajiyar zucia yace nayi tunanin wani abu ne nayi maki ban sani ba.
Mamy tace haba haba wane abu kuma? Babu komai. Ahmad yace yanzu ya batun tarewar ki? Mamy tace komai yana hannun ka, yanda duk kayi dani haka zanbi ka, Ahmad yayi wata irin daria ta jin dadi yace Mamy nayi kewar ki da ladabin ki, har abada bazan daina son ki ba, mamyn ma tayi murmushi tace nima nayi kewar ka sosai Ahmad. Nan dai suka daidaita akan akwai gidan daya gina dama da niyyar zai koma ciki shida Hady to ashe rabon Mamyn ne dan haka ta zama cikin shiri any time za'a idasa gyaran gidan wanda dama furnishing gidan kadai ya rage kuma am fara tuni.
**
Washe gari zakara ya baiwa Hajia Rabi da Hady sa'a suka hau jirgi suka wuce Lagos, anje wajen boka an dawo akan hanya bayan saukar su jirgin yamma sosai suka biyo suka dawo Abuja, hanyar su ta dawowa gida suke sake tattauna batun abinda ke damun su da alwashin da suka sha na raba mazan su da duk wata diya mace, drivern ya saki baki yana ta sauraren su kasancewar daga airport suka dauko drivern basu tsaya jiran nasu drivern ba ganin dare ya fara, hankalin drivern na ga hirar da suke yana mamakin irin wannan rashin imanin baiyi aune ba kuma bai san daga ina ba sai jinsu sukai karkashin katuwar motar daukar kaya truck, motar ta take su wanda anan take Allah Yayi wa Hady cikawa yayin da kafafun Hajia Rabi da hannun daman ta fit ya fice, fuskar ta daga gefe ta tsage sakamakon wani karfe daya yagar mata fuska, drivern kuma ya samu kariya a kafar sa ta hadu shima karfe ne ya buge shi.
Dandanan aka yo asibiti dasu, mutane da yawa sunyi tunanin ba za'a samu mai rai cikin su ba. Bayan kusan awanni uku ne aka samu number Ahmad sakamakon wani doctor daya gane hady, babu abinda ya samu jikin ta sai dan kurjewa da tayi, Ahmad wanda a lokacin ya samu dawowa Abuja domin ya azalzali masu furnishing gida suyi su gama, ya saki salati yayi hailala ga Ubangiji, yayi musi godia ya kashe wayar ya kira umman su ya sanar mata, dandanan aka sanar a dangi kafin kace me? Gidan Ahmad ya cika da en uwa na kusa yayin da na nesa suka ce zasu samu isowa da safe domin aui janazar Hady da su.
Ahmad ya kira mamy ya sanar mata, jiki na kyarma ta hau salati tana masa gaisuwa tace bari ta sanar da su malam, kuma suma suna nan tafe da safe In Sha Allahu. Da safen kuwa dukkan su suka shirya harda Muhd da iyalan sa da Hibba da nata iyalan da su Inna Indo, da su Inna Fulera da Inna Fatsima da Inna Rahane da Malam da aminin sa Malam Iro da mai dakin sa, haka dai sukayi motoci suka nufi hanyar Abuja tun bayan gama sallar asuba dan su samu janazar suma.
A gidan Ahmad din akai janazar Hady da karfe sha daya na safen ranar, 'yan uwa duk sun hallara, aka sallace ta aka kaita makwancin ta, bayan sun dawo ne Malam yace suma saisu dauki hanyar Kaduna kafin dare yayi, amma sunyi shawarar akan Mamy ta zauna kawai ita da yaran ta domin ta taushi Ahmad ta ruka tuna mashi kowa ma zai mutu ya koma ga Allah saboda rashi baya da dadi. Malam ya kara damkawa Ahmad amanar Mamy da Ayisha da Adnan sana sukayi sallama da iyayen Ahmad kafin suka dauki hanyar Kaduna suna mai jimamin al'amarin duk da ba sanin hadyn sukai ba bare daga inda ta fito har hadarin ya faru.
Ahmad yaji dadin hukuncin Malam na barin su Mamy da yayi, tuni ya nunawa Ayisha dakin ta haka Adnan ma, sana ya basu hakuri da suyi hakuri da wanda suka samu kafin su koma gidan su, yaran suka ce Abba babu komai nan ma wajen ya isa ai. Haka aka shafe kwana uku ana karbar baki masu zuwa ta'aziyya, a kwanan na uku ne salma ta samu isowa, tayi kuka kamar ranta zai fita, ta kuma kara tsoron Allah harta nemi afuwar Mamyn akan abinda suka mata shekarun baya, mamy tace ta yafe mata harga Allah. Gidan bai samu dagawar baki ba har sai da akai bakwai da mutuwar Hady, a lokacin kuma aka gama gyaran sabon gidan da hady taciwa buri, ashe ba zata shige shi ba wacce ta tsana ce zata shige ita da yaran ta. Allah Ya mana kyakykyawan karshe, ameen.
Ahmad tamkar ba'a masa mutuwa ba, sai idan ya tuna da hadyn ne ma yakan mata addu'a, rayuwa suka bude shida sabbin iyalan sa mai cike da aminci da ganin girman juna uwa uba ga soyayyar junan su, tuni ya maida adnan makaranta yayin da ake jiran lokacin da za'a bude nysc portal saboda Ayisha tayi registration. A lokacin ne kuma Ayisha ta fara tunawa sosai da King data baro a can London batasan wacce duniyar yake ba yanzu ma, koya mance da ita ne? Ko yana ina? Mi yake ciki? Duk bata sani ba sai Allah, wasu hawaye suka zubo mata tayi saurin gogewa jin shigowar mutum dakin ta.
Mamy ce da Abba (Ahmad) bayan sun zauna ne mamyn ke fadawa Ayisha itama yanzu hankalin ta ya dawo jikin ta dan haka tana bukatar Ayishan ta taya ta da addu'a domin zata fara neman dangin Adnan musamman Alima yayar shi sai kuma dangin baban shi domin ta sada su, Ayishan tayi murmushi tace wanna tunani ne mai kyau Mamy, Allah Ya shige mana gaba ya kuma ansa mana addu'ar mu. Gaba daya suka ansa da amin, Ayishan tace Mamy ina ganin zaifi sauki mubi ta hanyar maman Nadia tunda yayar maman Alima ce amma ya kike tunani? A wanna karon Abba ne ya ansa da cewar tuni mukayi wannan tunanin kuma nasa wasu dana sani mutane na dake London domin su bincika ita maman nadiyar amma bamu samu sa'ar samun su ba wai sun kwana biyu da barin kasar, Mamyn ta anshe da cewar zanbi ta hanyar bincikar garin Alh Ahmad domin ya taba sanar mani shi mutumin Niger ne, dan haka mun shirya akan zamuje Niger din nida Abban ku ranar Monday In Sha Allah, Ayishan tace amma dani za'a je ko Abba? Mamyn tayi saurin cewa idan kika bimu waye zai zauna da Adnan idan ya dawo school? Ayisha tace hakane kuma Mamy, to babu damuwa Allah Ya kaiku ya dawo daku lafia, suka amsa da ameen.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now