Auren Sirri 29

153 15 7
                                    

🔐Auren sirri🔐 2️⃣9️⃣
Kamar daga sama haka labarin auren king da Ayisha ya isa gidan su king, iya rudewa Mummy ta rude tayi kamar ta fita hayyacin ta lokacin data nemi king a waya amma a kashe wayar, kuka kuwa kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa ko kuma wata yarinya karama haka Mummy ta dararrashe kasa tana wani irin kuka, Amira da Amatullahi na kokarin janta daki Mummyn tana fadar ku barni kawai in mutu sai uban ku da king suji dadin dunia, me na musu suke nema su kashe ni da rai na? Dama shigo shigo ba zurfi sukayi mani dansu hadu su cuce ni, ni Laurat na shigu uku na lalace yanzu da rai na ina ji ina gani haka Maryam zasu hadu da diyarta su mallake mani da guda daya da Allah Ya bani kamar yanda ta mallake Alh Ahmad lokacin yana raye? Wuu sai kuma ta kara fasa kuka, Allah Ya taimake su ma suma ba wasu mutane da yawa suka gayyata ba, da alama dai duka familyn biyu sun dauki wasu daga cikin halayen turawa sakamakon zaman su da su, hatta Amal dake Dubai saida Mummy ta kira tayi mata tass, ace warta da hadin bakin ta aka daura auren king da Ayisha, ita dai Amal ta lallaba ta bawa Mummy hakuri bata ma fara bata labarin itama daga sama taji batun auren bakin king ba dan tasan hakan ma saidai ya kara harzuka Mummy.
Tana cikin wannan yanayin ne wayar Maman Nadia ta shigo, cikin bala'i Maman ke ce mata yanzu Laurat duk yadda nike da ke haka aka hada baki dake aka daura auren yaron ki da waccan yarinyar? Kin sani kika kasa sanar mani domin in dauki mataki? Yanzu ai burin ki ya cika kin baiwa danki abinda yake so ko? Mummy ta katse ta da cewa waike Adama meyasa baki taba yin tunani kike furta wasu maganganun? Kina tunanin da son rai na zan amince yaro na ya auri irin wannan macan wacce yake wa irin wannan son? To ni a kira ni da wa? Inji dadin mi? Ko Nadia dana amince ya aura ai saboda ita ke son shi sosai, daga can bangaren Mama ta harzuka jin cewar Mummy wai Nadia ita ke son king shiyasa ta amince akai auren, tuni wani mugun tunani ya shigi Mama daga can bangaren dan haka sai kawai ta datse wayar tana mai kullatar Mummyn da shi kanshi king din, a take ta kira wata abokiyar su da tuni take musu tayin zagaya bokaye amma suna ki, yanzu kawai sai take ganin lallai lokacin amfanin ta yayi, cikin kan kanin lokaci tayi mata bayanin abinda ke faruwa ta kuma nemi da ta rike hakan ya zama sirri tsakanin su ba sai Mummy taji ba (batan basira irin na Maama taya zata nemi kawar da tasan su duka suka san juna? Kuma harma ta fada mata bata so ta sanarwa Mummy? Abu na gaba shine banda son kai irin na Mama taya zata dage akan nemawa diyar ta abinda take so amma tana tuhumar Mummy akan ta nemawa nata dan abinda yake so? Idan ma hakan ne to Mummy tayi laifi anan duba da yanda Maman itama ke nemawa diyar ta abinda take so? Bari dai mu bi su muga ya rayuwar zata kaya. Allah Yasa mu dace).

**  **
Tun bayan da aka sanar da Mamy an daura auren King da Ayisha ta fadi tayi sujjada shukriya harda hawayen ta na farin cikin diyar ta ta auri wanda take so kuma bata aikata abinda ita ta aikata shekarun baya ba. Mamy tayi knocking kofar Ayisha jin shiru bata bata izinin shiga ba sai ta murda kofar ta shiga, Ayishan na kudundune akan gado da alama zazzafan ciwon kai ne ya same ta sakamakon tunanin da take addabar kanta da shi, tun sadda suka dawo Nigeria take tsammanin ganin sakon king a email dinta amma shiru har kusan wata daya babu wani bayani daga gare shi hakan yasa ta tattara laptop da wayar ta ta aje waje daya tunda dama ba fita takeyi ba kullum tana gida a daki, tun bata nuna damuwar halin da take ciki har damuwar taci karfin ta shiyasa ma Mamy ta fahimci Ayisha na cike da damuwa, ko dazu da safe dasu Abba zasu wuce Airport saidai su suka shigo dakin ta suka mata sallama. Mamyn tayi saurin isa wajen ta tana yaye duvet din data rufa dashi tana taba wuyan ta taji zafi sosai, Subhanallahi Ayisha jikin ne yayi zafi haka? Tashi ki danci abinci ki sha magani sai ki kwanta, Mamy duk ta gigice ta fice kawo mata abinci da magani, ganin rudanin da Mamyn ke ciki yasa Ayishan ta dan ci abincin tasha maganin tabi gadon ta koma ta kwanta, Mamy sai sannu take jera mata har bacci ya dauki Ayisha kasancewar Mamy tasa mata maganin bacci, Mamy data shigo da nufin tasa Ayisha tayi kwalliya saita buge da jinya har Ayishan tayi bacci, ganin hakan saita mike ta nufi kitchen ta bada umarnin abinda za'a dafawa bakin. Tana fitowa taci karo da Hibba cikin farin ciki suka tari juna, Mamy cikin mamaki tace zuwa babu sanarwa haka Hibba na? Hibba tace wallahi Mamy naso sanar maki kamar yanda Inna Rahane taso in sanar maki amma sai na fasa nace zanyi surprising din ki ne kawai kuma dama naso inzo tun sadda kuka tare wannan aljannar duniyar gidan naku mai kama da anguwa daya, Mamy tayi daria tace lallai kam kinyi surprising dina, Hibba tace Mamy sai mukaji abin alkhairi irin haka? Mamy tace bari kawai Hibba saiga auren Ayisha kamar daga sama, Hibba ta mike gami da cewa shiyasa na kasa hakuri nace lallai yau dani za'a karbi wannan angon na diyata, Mamy tayi saurin janyo Hibba tana cewa yi hakuri Maman Ayisha tana kwance bata jin dadi kuma duk damuwar king ne, na shiga dakin ta dazu insa tayi wanka ta shirya kafin su iso amma na kasa saboda ganin bata jin dadi kuma dama so nayi ayi surprising din ta kawai, Hibba ta dawo ta zauna tana cewa lallai soyayya mai dadi ta kwantar mani da diya, bari to mu bari ta tashi ni nan da Usman ya fada mani harda angon za'a taho yasa ba shiri nace zuwa Abuja yau ya kamani in fara hada diya ta koda kadan ne, Mamy tace Hibba masu diya ai anga rayuwa sai anbi an mallake ma Laurat da kamar yanda ta tsana dai, Hibba tace wallahi saidai tayi hakuri amma sai mun banbanta diyar mu da wacce suke so ya aura din, bari ma ki gani in fara fiddo abubuwan dana tattaro in fara hadawa kafin ta tashi.
Ayisha bata samu tashi ba sai bayan azahar, da alama kuma taji dadin jikin ta, ta mike ta shiga wanka tana fitowa Hibba na shigowa da tray a hannun ta da wasu kananan cups, Su duka suka saki murmushin jin dadin ganin juna, Ayisha tayi saurin karbar tray din tana fadin Aunty na bari na taya ki da wannan, Hibba tace barshi kawai yau ji nakeyi da ke kamar kwai, dan haka zauna kedai ki bani hadin kawai in gudanar da aiki na kafin ki dawo kina mani godia wata kila yau wata kila gobe ko kuma cikin satin nan, dan mazan yanzu basu da hakuri muddin aka ce kai nasu ne, ita dai Ayisha bata fahimci ina Hibba ta dosa ba sai kawai tayi mata murmushi tace uhum. Hibba ta zuzzuba wasu abubuwa cikin kananan cups wani tasa ruwa, wani tasa madara haka dai harta gama ta mikawa Ayisha tace idan tana iyawa ta shanye duka lokaci daya idan bata iyawa kuma ba dole, Ayishan tace ai naga kamar kadan kadan ne kuma cup uku ne bari muga, babu gardama ta shanye dukan su, Hibban tace masha Allah to ga wannan naman maza kici iya cin ki. Ayisha dai kodan bata kasance mai gardama bane yasa bata tsaya tambayar abubuwan menene ba? Tadaiyi duk yanda Hibba tace mata, a haka Mamy ta karaso tare da wata mata, Mamyn tayi murmushi tace tunda naji Hibba shiru na san Ayisha ta tashi ne shiyasa na kira Joy nace tazo, ta maida duban ta ga Ayisha tace ina fatan kinyi wanka ba? Ayishan tace eh nayi Mamy, Mamy tace madalla to ya kuma jikin? Ayishan tace tunda na tashi bacci naji kai na ya saki sosai, Alhamdulillah to ga mai make up nan tazo zatayi maki, nadai fada mata tayi maki light make up dan nasan halin ki yanzu zaki fara gunaguni. Ayisha ta kasa hakuri tace Mamy make up kuma, zamuje bikin aure ne? Hibba ce wannan karon tace kedai ki tsaya ayi maki na tabbata daga baya zaki zo kina mana godia, Ayisha ta kada kai tace to a bari inyi sallar Asr tunda baifi minti ishirin ba sai mu fara make up din, Mamy tace bari to nima inje kitchen in dubo abinci ko an gama sai inje nima inyi sallar, Hibba ma ta mike da tray data shigo da shi tace nima bara na maida wannan kitchen sai inzo nan inyi tawa sallar in kuma duba make up din ko joy tayi aiki mai kyau ta karishe cikin wasa da fadin idan kuma bakiyi mai kyau ba to rabin kudin ki zani baki dan ni zan biya, Joy na daria tace to Aunty ai dole inyi mata mai kyau.
Bayan ta idar da sallar Asr suka fara make up din, awa daya suka gama light make up din mai masifar kyau, idan kaga fuskar Ayisha a lokacin zakai marmarin ka kara duban ta, babu haukan abubuwa da yawa a fuskar ta, tayi kyau sosai, Hibba ta mike ta isa wardrobe din Ayisha tana fadin kinga tun dazu ya kamata in fiddo mata kaya amma sai yanzu na tuna ban fito da su ba, kaya ne zube cikin wardrobe din da aka dinka mata bayan dawowar su Nigeria kasancewar duk bata da Native yasa aka dinka mata su, idon Hibba yakai ga wani lace na HKG black mai digon chilly red da onion, Ayishan ta ansa ta saka sai duk suka saki baki suna kallon ta, gaba dayan ta ta canja sosai, Joy ta zizara mata head din, Hibba ta dauko saitin gold din Ayishan ta saka mata sana ta dauko agogon ta na Cartier ta saka mata. Ya Allah! Masha Allah! Wannan halitta tayi kyau inji Mamy dake shigowa, Hibba tace to zamu tari ango Mamy ai dole muyi kyau, bayan sun sallami joy harda kara mata kudi tana ta godia ta tafi.
Suna zama falo Alima na danno kai cewa take ina er kanwata ne ina fatan Mamy ta shirya mana ita... sai murya ta sarke ganin Ayisha cikin black lace daya mata kyau sosai, ta saki baki galala. Daga can tsakiyar su Abba da Usman dake sallama ne Ayisha ta tsinkayo sallamar king, tasan ako wanne hali take ba zata gaza gane king bare muryar shi ba amma yanzu ganin a inda take da inda ta baro shi sai hawaye suka zubo mata na tuna tasan bama shi bane sai kawai ta mike zata koma dakin ta, Adnan yayi karaf yace Sister yau kuma king dinne da aka kawo maki har gida kike nema ki gujemawa? Wata irin juyowa Ayisha tayi tana kallon Adnan ta kasa magana, king kuwa daya kasa hakuri sai ya isa wajen ta da sassarfa ya rungume ta, Ayisha na hawaye cikin rashin abinyi sakamakon kwakwalwar ta data gaza yarda da abinda idanun ta ke gani, yayin da king ke sakin ajiyar zucia ba kakkautawa, sai duk falon suka tsaya suna kallon su cikin tausayi ba kamar Mamy da Abba suda suka san irin tasu wahalar da suka sha. Ayisha tayi kokarin zamewa tunowa da gaban mutanen da take amma king yayi kam da ita yaki saki, a hankali take furta mashi king gaban iyaye na nike ina jin kunyar su, king ya amsa mata da cewa tausayi na da sukeyi ne yasa suka bani auren ki dan haka dan na rungume ki gaban su hakan ba zaisa suce baki da kunya ba, Ayisha ta dago cikin sauri tace kamar yaya suka baka aure na? Wannan karon Adnan ne yace Sister it's a long story amma dai an daura auren ki da king a Lagos dazu da safe, Ayisha saita koma zare ido bayan ta fisge jikin ta daga king tabi wannan da ido tabi wannan da ido gani take kamar zasu mata daria suce tsokanar ta sukeyi, daga karshe ta dire duban ta ga Mamy tana neman tambayar ta, Mamyn bata bata damar tambayar taba sai tayi murmushi tace gaskia ne abinda kika ji Allah Babu yanda Bayayi ako ina ako yaushe, mu namu biyayya ne dan haka kuka da tunanin king ya kare an daura auren ku dazu sauran bayani ya rage daga gare shi ya fada maki yanda akayi, ai sai Ayisha ta kwasa da gudu tayi dakin ta, cikin sauri king ya rufa mata baya, sai duk aka kwashe musu da daria, Abba yace Mamy na yau ta yarinyar ki kikeyi baki ta Abban ta ne? Mamy ta karaso wajen sa ta rungume sa tace nina isa in share Abban yara na, sannu da zuwa Abba gami da ruko hannun sa ta zaunar da shi. Usman ya dan saki tsaki cikin korafi yake hararar Hibba yace yanzu fisabilillahi Hibba kina ganin yanda wa'annan tsofaffin ke kulawa da juna amma er rungumar nan baki iya mani sai ki fara jero batun yara to taya yaran zasu fahimci yanda ake kula da mazan aure idan basu ga Maman su nayi ba? Hibba cikin kare kai tace nidai ban tashi cikin turawa ba dan haka ban saba da wannan rayuwar ba gaban al'umma... cikin kufula Usman yace dunia ce ba al'umma ba, in kuma kika cika ni da yawa to lallai zan auro wacce zata kula dani a gaban koma waye.
Mamy da Abba dai daria suke yi, Alima kuma taja hannun Adnan suka wuce dakin Ayisha wajen su ita da king suga su kuma ya tasu rayuwar take ne.
Ganin cece kuce din Usman da Hibba yaki karewa ne yasa Abba yace wai ni fa banyi niyyar sa baki ba jin tsofaffin da Usman ya kira mu sai kace ni din girme mashi nayi, kuma ai gara ni na auri daidai ni kai kuwa fa baka kusa haihuwar Hibba ba? Usman ya kara kufula yace to aida na kusa haihuwar tata naga ai tana kula dani a gaban kowa, dan haka yanzu jikanya ta zan auro saita kula dani yanda ya dace, haka kawai da sauran soyayya ta a gaba amma ba'a nuna mani, jibe ku kamar a hade aka halicce ku kullum kuna like da juna ni kuwa ina tabbatar maku ko a gidan mu ne sai a cikin daki kadai Hibba ke like mani, da zarar mun fito falo zaku ga tana baya baya dani kamar taga abin cutarwa, da alama dai da gaske abun baiwa Usman dadi ba, Mamy tace to yanzu dai kayi hakuri zan mata magana kuma zaka ga gyara In Sha Allah! Usman yace Allah Yasa taji maganar ki dan ni kamar ma ta rai na ni dan bata saurare na kullum sai kiji tace yaran ta take tsoro, to ku meya samu naku yaran da kuke irin wanna rayuwar mai ban sha'awa? Abba yace Usman wai kai complain baya kare maka ne? Usman din yace bazai kare ba ina ruwan ka? Hibba dai tayi kuri uwa mayya ita harga Allah kunya ke hana ta yin hakan da kuma yaran nata da take tunani, ko dan a WhatsApp yanzu ana ta gargadin iyaye akan su dena irin wa'annan abun gaban yaran su ne oho dai. Tadai hau zuba musu abinci ba tare data ce komai ba, suma saboda yunwar da suke tafe da ita sai ba wanda ya sake magana suka hau cin abinci.
A can kuwa dakin Ayisha na hango su rungume da juna kamar zasu hadiye juna, da kyar suka saki juna Ayisha ta zauna bakin gado king ma ya yi saurin binta, Ayisha tayi saurin cewa won't you fill me in? Ko sai nace ka fada man yanda hakan ya faru? King yace har yanzu nima gani nake kamar almara Aysh gani ga ki a matsayin ma'aurata, anan ne Alima da Adnan suka shigo ganin yanda da alama zasu takura Ayisha da King sai basu ma tsaya ba Alima tace bari inje dakin Adnan inyi salla inci abinci kafin Sadik yazo daukar mu, bata ma jira cewar wanin su ba taja hannun Adnan suka bar dakin. King ya labartawa Ayisha duk abinda ya faru tun barin ta school har kawo wajen daurin auren su, Ayisha tace Alhamdulillah! Allah Nagode maka ina kara mika godia gare ka domin dukkan yabo da godia sun tattara gare ka wanda idan yace kasance zai kasance, hakika komai ikon ka ne mallakin ka ne Allah Nagode! Nagode!! King ya goge mata hawayen da suka zubo mata. Ayisha tace shine ka kasa hakuri saida ka biyo su Abba? King yace aiko Adnan kasa sakin hannun sa nayi a Lagos gani nakeyi dana sake shi zai bacce shikenan bazan kuma samun wanda zai sada ni dake ba, Ayisha tayi daria tace bari inje in zubo maka abinci, king yace kinsan kuwa rabo na da abincin kirki har bana iya tunawa, harta mike king ya janyo ta ta fado jikin shi yayi saurin rungumeta ya kura mata ido, itama shi din take kallo, wani irin magnet ke bin jijiyoyin jikin kowannen su, Ayisha tayi kokarin zamewa amma king bai bata damar hakan ba saima saurin kai bakin shi cikin nata da yayi, a cikin qugun Ayisha taji wani zarrrrrr bata san sanda ta biye mashi ba, king dai yaso ci gaba Ayisha ta taka mashi birki, dolen shi ya hakura ba dan rai yaso ba, abincin ma sai ya zame masa kamar dole yake ci saidai yunwar dake tare dashi da kuma zaman Ayisha wajen ya hana ya yi korafin hana shi abinda yake so duk da baiyi niyyar ya zarta abinda ya wuce kiss ba.
Aysh kinyi kyau sosai, black nayi maki kyau, Ayisha tace thank u Babe, king ya dan bata fuska yace yanzu fa dana nemi in kara yaba kwalliyar ki ta hanyar nuna yabawa ta saiki hana ko? Ayisha tayi daria saboda ta gane abinda yake nufi  amma saita wanye da cewa yanzu ma naji dadi daka yaba da kalaman ka, King yayi murmushi yace necklace ya maki kyau sosai ban taba ganin ki da shi ba, Ayisha tace saboda bana da sha'awar saka necklace shiyasa baka taba gani na da shi ba amma yanzu tunda ka nuna kana so ai zanyi ta sawa ne, king yace Aysh bansan yawan farin cikin da nike ba, ina ganin abin kamar almara, Ayisha tayi murmushi tace nima hakan ne waje na.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now