Auren Sirri 32

152 13 3
                                    

🔐Auren sirri🔐 3️⃣2️⃣
Rayuwa mai dadi King da Ayisha keyi a kasar ta Abu  Dhabi, sunyi masauki a Al-Hayat Hotel Suites dake nan Sharjah, suna dai more soyayyar junan su da kulawa da junan su, kullum sai yammaci suke fita zaga gari, sukan fara da shiga kasuwa duba kayayyaki kasancewar Ayisha nada burin ta siya kaya da yawa idan suka koma Abuja ta bude shop, King kullum cikin karfafa mata gwiwa yake akan kasuwancin da take so ta fara dan haka bai taba gajiya dayi mata rakiya cikin kasuwar Souq Al Wasl ba, ta fara da duba Abaya a shops din Farasha, Wahad, Niqab shops dai gasunan kala kala duk inda ta shiga saita zabi designs da take so da sizes sana ta basu order, daga baya ta rika shiga cikin sharjah sosai wajen su Royal tana zaben kayan gida, harda su Gold souq take shiga neman fashions kala kala. Idan Amal nada interval wani lokaci takan rakasu don itace ke fada mata sunayen shops din, idan bata da time takan tura musu agent din data sani saiya kaisu, wani lokaci sukan shiga mall ne, Al Raha Mall, Abu Dhabi mall, Marina Mall ko su tafi wajen shakatawa musamman idan su biyu ne.
Wata rana sun shirya zasu fita kenan wayar Ayisha ta hau kara, bata san number ba shiyasa bata daga ba saboda tasan ba mutane da yawa ma ta sani a rayuwar ta ba to waye ne zai kira ta? Amma ganin mai kiran yaki denawa sai ta yanke shawarar ta daga taji ko waye, bayan tayi sallama an amsa mata sai tayi shiru domin jin muryar namiji kuma da alama babban mutum ne, Baban Nadia daga dayan bangaren ya gabatar da kan shi wa Ayisha, cikin faduwar gaba Ayishan ta gaida shi ta sakeyin shiru tana sauraren abinda zai fada mata, Baban Nadia ya bukaci magana da King, Ayisha tace eh yana kusa bari na mika masa, bata jira cewar king ba bayan ta bashi wayar sai kawai ta fita daga dakin ta wuce reception wajen wasu kujeru tayi zaune tana kallon fountain ba tare da tasan me take tunani ba, tadai tabbata bazai wuce maganar Nadia ba, ita kuma yanzu bayan wannan dan lokacin data fara sabawa da king ko yaushe suna manne da juna anya kuwa zata iya hakurin ganin shi da wata macen? Wasu hawaye masu zafi suka zubo mata tayi saurin gogewa kafin ta hau Istigfari tana Hailala sai ma kawai ta fiddo dan karamin kur'anin dake cikin handbag dinta ta hau karatu, cikin kankanin lokaci taji ranta daya cunkushe yayi wasai amma bata dena karatun ba har zuwan King. Bayan ya zauna ne ya jira ta ta idasa suratul Maryam data ke karantawa, sukayi wa juna murmushi king ya mika mata wayar yace ga wayar ki Ayshh, Ayishan ta karba gami da cewa mu tafi? King yace eh.
Wannan karon Amal suka kaiwa ziyara a School, tayi jarabawa dazu da safe kuma jibi ma tana da ita shiyasa tace babu inda zata zata zauna tayi karatu ne, wayar ta dama ta rufe ta tunda ta fara exams, Muhd ma kanin Mamy sai a wayar Ayisha suke gaisawa idan suna tare kuma bai takura ba kasancewar yasan halin da take ciki, yau ma bayan haduwar su Ayisha ta kira Uncle din nata ta mikawa Amal. Bayan barin Amal daga wajen ne King ya kasa hakuri yace Aysh ba zaki tambaye ni wayar da nayi da baban Nadia ba? Ayisha tayi murmushi tace meyasa zan tambaye ka King? He must have his reason da yasa ya kira ka shiyasa ma na baku wuri, King yayi ajiyar zucia yace gaskia ne, ya ansa number wajen Daddy kuma akan Nadia ne ya kira wai... Ayisha tayi saurin cewa for God's sake I am not interested King, cikin mamaki King din yake kallon Ayisha amma kasancewar yana da wasu halaye na turawa na rashin son takura mutum musamman idan mutum ya nuna baya da ra'ayi sai ya kyale ta kawai amma a ranshi yasan akwai dalili saidai ya kasa hangowa. Shi yana so ya bata labarin cewar baban Nadia ya takura shi akan ya saki Nadiyar saboda bata da hali mai kyau, kuma tana bin zugar Uwar ta, shi kuma yana neman hanya dama na rabuwa da Nadiyar amma akace kunya da mutunci ma wani abu ne dan haka ya kasa aikata abinda mahaifin Nadiyar ya bukata da yayi har saida mahaifin Nadiyar cikin subdued voice ya bayyanawa King abinda suke shirin aikatawa ita da uwar ta da kuma hukuncin daya yankewa uwar Nadiyar, ya karashe maganar shi da cewa nasan ina da wasu halaye da bai kamata ina aikata su ba amma maganar bokaye da 'yan tsubbu ban taba kawo ta a rai na ba bare in aikata kuma itama Adama nayi tunanin hakan ne daga wajen ta sai ranar da Allah Ya toni asirun su naji su suna maganar, kuma nasan harda laifi na cikin rayuwar da Nadia ta tashi ganin cewa ita daya Allah Ya bamu yasa muke mata duk abinda take so ba tare da musawa ba ko nuna mata dai dai da rashin dai dai. King yayi shiru kamar ruwa ya ci shi, Baban Nadia yace kaje kayi shawara Mu'azzam duk abinda ka yanke hukunci zan saurare ka, Allah Ya dawo daku lafia, king yace ameen ameen daga nan sukai sallama.
Amal ta dawo tana daria ta mikawa Ayisha wayar tana cewa wannan Uncle din naki dan soyayya ne Ayisha, sukai daria su duka. Sun yini anan kafin sukai mata sallama suka wuce hotel din su. Bayan sunyi wanka sun kimtsa ne King ya kira Daddy bai boye mashi komai ba akan yanda sukai da Baban Nadia, Ayisha na kwance cikin bargo tana sauraren su kasancewar a speaker wayar take, a ranta tace Allah Yafi karfin duk wani mai taqama da bokaye kuma da Allah na dogara nasan Allah Ba Zai basu sa'a ba da izinin Allah, ita daga nan ma sai bacci ya dauke ta bata san ya king ya kare da Daddy ba.
Daddy da King sun jima suna magana akan Nadia da hukuncin da Baban ta ya yanke, Daddy dai ya cewa King yaje yayi shawara da kan shi duk abinda ya yanke hukunci sai ya sanar masa tunda shi ne zai zauna da Nadia ba kowa ba, daganan Daddy ma ya sanarwa King halin da Mummy, Ameera da Amatullahi suke ciki, King yayi ajiyar zucia yace Daddy kayi hakuri ka yafe musu tunda sun gane kuren su nima In Sha Allahu gobe zan kira Mummy, Daddyn yace ni kaina na gaji da sharewar da nake musu amma daga gobe nima zasu ga canji In Sha Allahu, kuma kayi kokari ka kira Mummy sai ka hada su da Ayisha ma suyi magana a waya tunda da alamun ta gane kuskuren abinda ta aikata, daga nan sukai sallama.
Washe gari King saida ya tabbata suna tare da Amal sana ya danna number Mummy, a lokacin Mummy suna zaune ita da Amira da Amatullahi sunyi zugum zugum kamar kullum, Amatullahi ta mikawa Mummyn wayar ta tana cewa ga number nan daga Dubai na kiran ki kila ko Amal ce, Mummy tayi saurin daukar wayar saboda ko Amal din ta dena ji daga gare ta, amma sabanin hakan muryar King taji yana gaishe ta cikin kyawun lafazi, Mummy sai kuka ma ya kwace mata cewa take Mu'azzam kai ne da gaske? Ka bude layin ka? King kana ina? Dan Allah kazo in ganka nayi nadamar abinda na aikata, King din yace Mummy dan Allah ki dena kuka hakanan zaki sa inyi ta jin babu dadi saboda kukan ki, Amira da Amatullahi sai cewa suke Mummy dan saka speaker muji muryar shi muma, amma da alama Mummy bata san suna yi ba, King yace Mummy kiyi hakuri akan rashin kiran ki da banyi ba da kuma abinda nayi... Mummyn ta katse shi da cewa King ni ya kamata in fadi kalmar hakurin nan kuma ni baka man komai ba dan ka auri yarinyar nan Ayisha, domin wa'anda na dauka sune muke tare ashe a ransu ba haka bane, mummy ta kara share hawaye tana cewa tunda nake rayuwa ta ba'a taba cin amanata irin yanda Adama da diyar ta Nadia sukai mani ba, haka kawai na biye musu na hana yaro na abinda yake so yayin da ita take nemawa diyar ta abinda take so.
King yace ai yanzu komai ya wuce domin baban Nadia ya kira ya kuma fadaman da in saki Nadiyar shima ya raba kan shi da fitina domin ya rabu da Maman Nadiyar shima, dan nima yace in masa arziki in rabu da Nadia sai yaga ta yanda aikin boka zai bata abinda Allah Bai bata ba, har Mummy ta bude baki zata ce ka sake ta kawai sai kuma ta rufe bakin ta saboda tunawa da abinda Daddy ya fada mata, ita ina zata so auren ta ya mutu saboda wata banzar mushirikiya? Sai kawai tace to Allah Ya zaba abinda yafi alkhairi, kafin ma yace ameen taci gaba da cewa yanzu daka kira ni da number Dubai yaushe ka tafi can ne? Kuma kana tare da Amal ne kome ya kaika can? King yace munzo ne nida Ayisha bayan ta tare gidan mu dake Abuja sai muka yanke shawarar mu bi Amal Dubai mu jira ta ta gama exams din ta sai mu juyo gida tare, Mummy tace yanzu kuna tare da Ayishan da Amal? King yace eh ga Ayisha ku fara gaisawa gami da matsawa can kusa da su yana mikawa Ayisha wayar yana fada mata mummy ce (kasancewar da zaiyi wayar sai kawai ya anshi wayar Ayishan yace ta bashi zai kira Mummy ne sai kuma ya matsa nesa kadan dasu) Ayisha tayi sallama gami da gaida Mummy cikin fara'ar nan tata tamkar yau ne ta fara sanin Mummyn (wato ta nuna ta manta da abinda suka mata a school din su a London) cikin jin nauyi Mummy take amsawa Ayishan tana tambayar ta suna lafia dai ko? Ayisha tace lafia lau Mummy muma aimun kusa dawowa baifi sati daya ba nan gaba kuma ta nan Lagos zamu sauka In Sha Allahu, cikin jin dadi Mummy tayi ta shiwa Ayisha albarka tana mai nuna farin cikin ta, daya bayan daya Ayisha ta gaisa da Amira da Amatullahi kafin Ayishan ta mikawa Amal waya itama suka gaisa da Mummy da sauran en uwan ta mata.
Itama Amal saida taja gefe ta bar king da Ayisha ta matsa suna magana da mummy tana kara tabbatar wa mummy Ayisha da iyayen ta mutanen kirki ne na sosai, tazo Nigeria ai har Abuja lokacin tarewar su Ayisha a gidan su kuma Daddy ma yazo ana gobe zasu tafi Dubai, daga karshe bata tsaya boye boye ba ta fadawa Mummyn maganar Muhd kanin Maman Ayishan da kuma matsayar su, Mummy tayi ajiyar zucia tace Allah Ya tabbatar mana da alkhairi nima zanyi kokari insa Daddy ya shirya mani tafia nida su Amira zuwa Abujan sai inje har gidan su Ayishan in baiwa Maryam hakuri akan abinda nayi mata, Amal tace to Mummy Allah Yasa mu dace, daganan suka aje waya.
Kaf hirar da mummy tayi dasu king a kunnen Daddy kuma har a ranshi yaji wani irin farin ciki mara misaltuwa dan haka mummy na aje waya daddy ya fito yana murmushi kai tsaye ya tari mummy ya rungume ta yana cewa ina maki barka daga fitowa cikin duhun da kika saka kanki kuma ina maki albishir da cewa har abada ba zan dena son ki ba, soyayyar ki ce tasa na aure ki dan haka mezai sa in rika bata maki rai? Nayi abinda nayi ne ko za'a samu ta silar hakan ki gane gaskia kuma Alhamdulillah a yanzu na tabbatar da kin fahimci gaskiyar, mummy ta rungume daddy sosai tana share hawaye tana cewa ada nayi tunanin ka dena so na ne duk da dunbin laifin dana aikata amma nima yanzu wannan tunanin ya gushe kuma ina kara baka tabbacin wani abu makamancin abinda na aikata a baya ba zai kara faruwa ba da izinin Allah, daddy ya hada da Amira da Amatullahi da mummyn duka ya rungume, yau dai kam wannan iyalin suna cike da farin ciki mara misaltuwa, daddy daga karshe yake sanar musu ya siya gida a Abuja wajen Alhaji Ahmad mahaifin Ayisha kuma cikin gidajen su Ayisha ne, da yake su Ayishan kadai ne suka fara shiga gidajen, kuma har furnishing yasa anyi dama yana jiran ranar da zasu dawo daidai ne sana ya sanar masu da batun komawar su Abuja amma tuni ya sanarwa king da Amal kuma sunji dadin hakan acewar su gara mummy tayi nesa da Maman Nadia, mummy dasu Amira sun nuna jin dadin su sosai akan hakan amma suka cewa daddy to ya bari sai nan da dawowar su king tunda sun fada musu nan da sati daya zasu dawo kuma zasu sauka ta nan Lagos ne, idan suka dawo suka huta gajiya sai su wuce Abuja gaba dayan su, da wannan suka yanke shawarar hakan.
Bangaren Muhd kanin Mamy kuwa ya matsa ma Mamy tare da Abba akan cewa shifa so yake su Amal na dawowa ahau bikin su, Mamy tayi daria tace Muhd zumudin me kakeyi ne? Yarinya daga dawowa ta hau hidimar biki ka bari kawai ta huta inyaso daga baya sai ayi maganar bikin tunda dai an baka kuma yarinyar na so, Muhd ya sosa keya yace Mamy tafia ce ta kama ni kuma da alama zama na zai koma acan ne shiyasa nake so na samu wacce zamu tafi tare ko kuma mu tafi mu duka ma, Mamy tace har ina? Muhd yace Turkey, domin Alhamdulillah furnitures din da mukeyi suna ta kara samun karbuwa shine naga bari kawai in koma kusa da inda nake sana'a ta wacce tafi karfi, Mamy tace Alhamdulillah hakan yayi kyau, Abba ma yace nima naji dadin hakan kuma zan tuntubi shi baban yarinyar inji yaushe ne zasu aurar da ita, in yaso sai in fada maka duk yanda mukayi.
Da dare Abba ya kira Daddy bayan sun gama gaisawa tare da tambayar iyalin juna ne Abba ya shigo da abinda yasa ya kira wayar, Daddy yace to Alhaji Ahmad banda abin ka me kake tunanin muke jira ga diyar mu mace data samu mijin aure? Ai badon ma kada ace na zaqe ba toda a ranar da suka dawo zance a daura auren to muma kasan da batun dawowar mu Abuja tunda kai ne ka shige gaba wajen ganin anyi furnishing gidan ma, daba dan ina so mu dawo nan Abuja ayi auren anan ba aida nace tana dawowa za'a daura dan haka ka sanar mashi duk randa muka dawo Abuja da sati daya kacal za'ayi auren shi da Amal In Sha Allahu, Abba yayi ta godia har saida Daddy yace haba godiyar aita isa hakanan sana suka aje wayar, Abba ya kalli mamy yace to kanin ki dai mai sa'a ne an bashi Amal kuma an fidda ranar daura aure, ai duk kinji abinda ya fada dai, mamy tace Alhamdulillah muna murna Allah Yasa ayi akan sa'a. Mamy bata bar wajen ba sai da ta sanarwa Muhd da iyayen su wato Malam Isuhu da Inna Rahane batun auren Muhd din da Amal kuma suma addu'a suka bi al'amarin dashi yayin da Muhd bayan addu'a da yayi sai kuma farin cikin daya kara nunawa ya biyo baya.
Ranar da su king, Ayisha da Amal zasu dawo gidan sai gyare gyare da girke girke akeyi na taryar bakin, da kyar daddy ya samu mummy ta samu lokacin da tayi wanka ma, amma da matsawar shi yace duk dadin yau dan gaban goshin ki zai dawo ne haka kin gaza nutsuwa akan ta yanda zaki tarye shi amma da alama zai dawo ya tarar dake kaca kaca baki ko yi wanka ba, sana ne fa mummy aka shige akai wanka, driver daddy ya tura musu dan haka da suka iso duk a farfajiyar gidan suka tarar dasu, mummy kamar zata fadi saboda jin dadi, cikin hanzari ta budewa king kofa shima cikin sauri ya fito suka rungume juna, da kyar mummy ta sake shi sana tayi kan Ayisha da su Amira da Amatullahi ke rungume wa suna mata sannu da zuwa, mummy ma ta janyo Ayisha tana cewa ku bani diyata hakanan nima in rungume ta, Ayishan har a ran ta taji dadin tarbar data samu wajen iyayen king da en uwan shi, har falo hannun ta yana cikin hannun mummy datayi kam kam da shi, Daddy sai tsiya yake wa mummy waita samu sabuwar diya.
Amal dai sai ita ta kawo kanta ga mummy tana cewa nima ai nayi missing dinki mummy amma baki tawa sai ta Ayisha da mijin ta, mummy ta janyo Amal tace ina kewar ki sosai Amal musamman yanzu daba jimawa zakiyi ba zaki tafi naki dakin mijin, sai duk sukai daria. Yinin ranar daddy baije ko ina ba yana gida wajen iyalin shi, salla kadai ke tada su kuma da sunyi zasu dawo a dasa sabuwar hira, Ayisha dai tuni ta sake da su da zucia daya musamman da agaban kowa mummy ta nemi yafiyar Ayisha akan abinda suka aikata mata a school, harda su Amira da Amatullahi suma suka nemi yafiyar ta, Ayishan tace babu komai ya wuce dama bata rike su da komai ba dan haka Allah Ya basu hakurin zama da juna lafia cikin aminci. Kowa saida Ayisha ta bashi tsarabar da tayo musu, kuma sunji dadi sosai saboda bahaushe yace kulawa ma yabawa ce. Da daddare daddy yasa suka shirya da nufin zuwa anguwa amma sai gasu a wani Chinese restaurant a nan cikin Ikeja, ashe tuni daddy yayi booking komai su cake, abinci, drinks, dessert, snacks da proteins kala kala. Daddy yace surprise dinner naso inyiwa newly married da kuma graduate din mu Amal. Sunci sun sha sun yanka cake sunyi pictures na tarihi, gaskia sunyi enjoying dinner sosai dan basu koma gida ba sai after 12am, suna komawa kowa ya wuce masaukin shi, king dai babu kunya ya janye hannun Ayisha sukayi dakin shi, taso ta noqe amma Amatullahi tace sister ki tafi kawai mun hadu da safe, da haka kowa ya wuce dakin sa.
Asuba ta gari.

Mrs sS ❤️✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now