Auren sirri 14

331 17 1
                                    

🔐Auren Sirri🔐1️⃣4️⃣

ASALIN LABARIN

Asalin Mamy Yar Nigeria ce yar garin Zaria ne amma a cikin Kaduna suke zaune, mahaifin ta Malam Isuhu nada matan aure uku Inna Fulera ce Uwargidan sa ta haifi yara biyu maza sai dai Allah Baisa sun zauna ba duk sun rasu kuma bata sake haihuwa ba amma ta dauko rikon diyar kanwar ta data rasu wajen haihuwa ana ce mata Fatu, sai matar malan Isuhu ta biyu wato Inna Fatsima tana da yara biyu mata Amina da Hawwa, sai kuma Amaryar su Inna Rahane tana da yara Uku, Maryam ce babba wato Mamy sai maibi mata Muhammad, sai autar su Muhibba ana ce mata hibba. Inna Rahane tasha wahalar kishiyoyin ta saboda yanda Allah Ya tsayar mata da yaranta babu wanda ya rasu cikin duka ukun kuma Allah Yasa tana kyautatawa Malam Isuhu sai kishiyoyin da ada suke gaba da juna kullum cikin fada suke amma sai suka hade kai suke musguna mata, yaran ta basu isa su fito tsakar gida ba zakaji sun koma dakin su da gudu suna kuka an buge su, saidai Inna Rahane ta kama su tana rarrashi, harya kasance da kansu yaran suka dai na fita tsakar gidan kafin girma ya fara cin masu.
Malan Isuhu su biyu rak Allah Ya baiwa Iyayen su kafin su rasu, shida kanwar sa Aisha ana ce mata Inna Indo, yaran ta biyar maza uku mata biyu, Inna Indo masifaffiyar mata ce ta bugawa a jarida ga shegen kwadayin abin dunia, ta hade kai da matan Malam Isuhu suna cusgunawa Inna Rahane da yaran ta.
A kullum Malam Isuhu sai ya baiwa Inna Rahane Hakuri kan halin da take ciki dan sarai yana sane da takurar da ake mata shekara da shekaru amma bata taba daga kai da niyyar masa magana dan a samu gyara ba, to shi kansa matan nasa ba wani mutunta shi suke ba bare harya iya tsawatar masu, wannan dalilin ne yasa inna Rahane kullum take kai kukan ta ga Allah, idan kuma Malam Isuhu ya fara mata magana bata iya cewa komai har se yakai aya sana tayi murmushi tace haba Malam duka duka rayuwar nawa take? Wata rana duk wannan abin baza'ai ba dan haka ka dena damun kanka indan tani ce. Da haka suke rufe babin wannan maganar kafin wani lokaci a sake dago ta.

Malam Isuhu baiyi karatun boko ba sai makarantar Allo sai zuwa gona amma daya girma saiya fahimci amfanin karatun dan haka yayi kokarin saka yaran sa makarantar boko bayan ta Allo da suke zuwa kasancewar yana da rufin asirin sa kuma makarantar gwamnati ce ma ya saka su amma dai dan uniform da litattafai da kudin tara duk bai gaza ba, inda aka samu akasi shine wajen Inna Fulera da Inna Fatsime kasancewar duk babu wanda yayi bokon cikin su sai abun bai dame su ba bare su matsantawa yaran su da zuwa, yaran kuma suke abinda suka ga dama kuma dama kansu daya ne wato diyar rikon Inna Fulera Fatu sai kuma yaran Inna Fatsima Amina da Hawwa, Inna Rahane duk da itama batai bokon ba sai ta Allo ba zaka taba ganin ta kace ko Primary batai ba yanda take da fahimta ga nutsuwa, ko fada ba zaka tarar tanawa yaran ta ba idan sukai ba daidai ba saidai kaji cikin taushin lafazi tana hankaltar dasu abinda suka kuskure, ta kuma tsaya tsayin daka wajen ganin yaran suna karatu na boko dana Allo. Inna Rahane tana sana'ar kulle kullen kayan amfanin gida su kuka,daudawa,magie,gishiri,sabulu,omo yan kananan kayayyaki dai haka, kuma Allah Ya sakawa abun albarka dan duk abunda yaran ta ke so ita keyi musu cikin rufin asirin Allah, kullum yaran zaka gansu tsaf abunsu ko sunje Makarantar boko kota Allo daga baya ma sai Inna Rahane ta shawarci Malam Isuhu akan tana so ta maida yaran Islamiya sai su rika zuwa da yamma da dare kuma sai su rika zuwa makarantar allon amma ta dare, Malam Isuhu bai wani ja ba ya amince yaran suka fara zuwa Islamia.
Nutsuwar yaran da kyawun Yaran da suka debo wajen Inna Rahane kasancewar ta bafulatana kuma fara mai fara'a yana bala'in yiwa sauran matan Malam Isuhu ciwo, ba karamin bakin ciki suke yi ba da wannan abubuwan har basa iya boyewa suke fitowa fili suna fadan maganganu na bacin rai amma daidai da rana daya Inna Rahane bata taba tanka musu ba, wannan ma yana kara musu ciwo sosai. Kamannin su daya yaran kamar an tsaga kara, wato suda Inna Rahane har gara Maryam data debo fatar Malam Isuhu sai hasken ta yadan dakushe ta zama kamar en matan morocco.
Maryam ta tashi da wata irin basira don duk tafi sauran en uwan ta ga wani irin shiru shiru kamar miskila kuma halitta ce kawai da Allah Ya halicce ta da shi ga wani irin diri na ban mamaki, ba za'a iya cewa yaran suna da wata babbar matsala ba idan aka cire matsalar matan Baban su to amma koda yaushe Inna Rahane tana yawan musu nasiha da babu abinda yake tabbata har mu din wata rana zamu mutu ne dan haka su zama masu yawan yafiya ko suma Allah Zai gafarta masu, da ire iren wannan maganganun na Inna Rahane ne yaran suka tashi har Maryam ta kai aji uku na sakandire, muhammad ya samu shiga aji daya na sakandire sai hibba dake ajin karshe na primary. Yayin da Sauran yaran gidan banda tara samari babu abinda sukeyi, kullum sai anyi sallama da daya daga cikin su, abinda zai baka mamaki irin yanda suka hade kai su ukun nan ba'a ko jin kansu, kuma kusan kansu daya da Maryam amma suna al'amuran su kamar ma basu san da zaman su Maryam din ba a cikin gidan, sai dai suna tsananin jin haushin kyawun yaran Inna Rahane musamman Maryam wacce farat daya baka iya banbance jinsin data fito,babu ruwan da Arabi bare Boko sai harkar samari.

Kaddarar Maryam ta fara ne daga shigar ta aji uku na secondary, a lokacin aka kawo wani sabon Malami dan bautar kasa, dazai ci gaba da daukar su English Language, satin su daya da fara farkon zangon aji uku Maryam ta kwanta rashin lafia dan haka bata nan sadda malamin ya fara koya musu sai a sati na uku da fara karatun su ta samu komawa makaranta. Kawar ta daya a dunia itace 'yar tilon kanwar ta hibba duk da shekarunta kanana ne haka zakuji duk rashin son surutun ta ta saka hibba a gaba tana mata hira har akance idan kana son ganin maryam na surutu to ka nemo hibba kusa. Wani irin so Maryam takewa hibba, Muhammad bai cika shiga sha'anin su ba dan shi kuma ina ka fito biro ina zaka biro da takarda ne sune abokan hirar sa sai kuma Inna Rahane shi kuma yafi shiri da ita akan yayar shi da kanwar shi.
Amma wannan jinyar da Maryam tayi kusan su duka sukayi ta harshi Muhammad din da kyar suke tafia makaranta su barta gida gani suke da sun dawo za'a ce musu Maryam ta mutu, dan haka a satin ba karamin kara shakuwa da juna sukai ba wanda hakan yai sanadiyyar Muhammad ya dawo suka dinke suka zama su hudu in aka hada da Inna Rahane saboda bata wani kunyar yaranta, jansu take a jiki sosai suna hirarrakin su da daria, idan aikin ta ne harda Malam Isuhu zasu zauna dakin Inna Rahane ana hira wanda hakan ya kara assasa azabar da sauran matan Malam Isuhu kewa wa Inna Rahane
Mafiyawanci Inna Rahane takan tsoratar da yaranta akan sabon Allah tun basu san wasu kalaman ba har suka sani wajen Inna musamman Maryam tana yawan fada mata ta guji duk wani da namiji, inta samu mai son ta kuma itama tana son shi to ita da Malam ba zasu hana tayi aure ba duk da kasancewar ta yarinya kuma tana tsaka da karatu don auren shi yafi a musulunce, Maryam kanyi daria tace haba Inna wane irin aure in tafi in barku keda Hibba na, ga Muhammadu na shima yanzu muna dasawa sai duk su kwashe da daria, to ahaka rayuwar su take, sune abokan junan su,abokan shawarar su, kuma basu da hayaniya ga tsabta dan duk ayyukan gidan su uku sukeyi indai suna nan hatta abinci sun koya wajen Inna Rahane, Hibba kadai ce basu turawa wajen wuta saidai ta musu yanke yanke da share share koda ba aikin Innan su bane haka zasu tsabtace gidan saboda tsabtar muhalli data kama jikin su. Matan Malam Isuhu basu wata kasuwa sai abinda Malam ya samo ya kawo kuma cikin yardar Allah kullum bai gaza abincin su ba, amma ganin yanda Inna Rahane da yaranta kullum tsaf suke sai suke zagin Malam akan baya adalci kullum a gindin Inna Rahane da yaranta yake karewa alhalin ba haka bane, Inna Rahanen ce keyi musu cikin albarkar kasuwar ta.
Inna Indo na yawan zuwa gidan Malam Isuhu roke roke duk da shima ba wani shike gare shi ba a hakan yake dan bata wani abun amma bai hana gobe ko jibi ta sake dawowa saboda Allah Ya mata son abun dunia ga wani irin miji da Allah Ya bata kwata kwata baya tabukawa kullum yana kofar gida ana zaman kashe wando sai itace keyin buga buga tana samowa gami da roke roken ta, kaf layin su babu wanda baisan da zaman Inna Indo ba saboda bako dan roke roke ba sai don azabar masifar ta da bala'i baka isa ka taba mata yara ba saita tadda ka har gaban uwar ka ta nemi dukan ka dan akance ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi to amma banda Inna Indo, kadai abunda zaisa ta raga maka shine idan kuna da dan arziki ta kuma lura zata samu wani abu, da wannan halayen yaran ta suka gurbata gaba dayan su barin ma babban su Adamu shi kam har shaye shaye yakeyi gashi ba arabi bare boko sai bin lunguna ana busa hayaki a dawo gida ciki a fafare ba abinci in kuma akai rashin sa'a bai tarar da abinci ba sai kaji tus tus yana kashe robobin gidan cikin zafin zucia to cikin wannan halin ne ya kyalla ido wata rana yaga kyakykyawar maryam mai cike da hankali da nutsuwa ya haukacewa uwar sa shi son maryam yakeyi kawai a bashi auren ta. Sani kebi mashi shima dai dan tasha ne amma baya shaye shaye saidai mugum jahili ne kuma shi yakan dan taba sana'ar dako saidai daya samo dan abinda ya samu sai a garzaya gidan magajiya anan en kudin zasu kare bai tsinana komai dasu ba. Salisu ke binshi shi kuma dayake ya dan zauna gidan Malam Isuhu wajen Inna Fulera kuma Malam Isuhun bai yarda da zaman shi haka ba saida yasa shi makarantar boko da allo amma yaki ta bokon sai allon yadan tabuka kafin itama yaji ya gaji kawai an takura shi sai ya tattara yanashi yanashi ya dawo gaban iyayen shi yaci gaba da sakarci da yaran anguwa. Sai matan Larai da Karime suma dai babu arabin ba boko har gara Karime ita tana dan tallar fura, to a haka dai suke tasu rayuwar suma.
Wannan kenan..

Mrs sS ❤️ ✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now