MURADIN RAI Chapter 1

626 21 0
                                    

*MURADIN RAI*
*(Abou hateem)*

*ZM~CHUBAƊO_*
✍️

*_Da sunan Allah mai Rahama mejinqai, salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira Annabi muhammad (s.a.w).

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page: 1

____A Shekarar 2019 wanda yay daidai da 28/12/ na wannan shekarar, Gudu yake rungume da qaramin yaro wanda baze wuce shekaru bakwai zuwa takwas ba, gudu yake bilhaqqi da gaskiya wanda daga kallon farko zaka fahimci cewar gudun ceton ransa dana ɗan dake hannunsa yakeyi, ko ina ya samu jefa qafarsa kawai yakeyi a cikin qungurmin dajin wanda ke cikeda tarin bishiyu, bakajin sautin komai iface na nishin sa gamida qarar busassun ganyayyakin dayake takawa sabida yanayin bazarar da ake ciki a wannan lokacin

Can daga bayansa haniniyar dowakai ce ke tashi gamida ihun mahaya kan dokin wanda suka nufoshi a sukwane kuma sukeda muradin kama wannan matashi wanda baze wuce shekaru 35 ba.

Ganin da sukai wankin hula na shirin kaisu ga dare ne yasa ɗaya daga cikin mahaya kan dokin ya zaro Bindigar dake saqale a bayan wandonsa ya saita wannan matashin dake gudun tsira da rayuwarsa cikin baqin zafin nama ya sakar masa harbi a gefan hannunsa na dama, take matashin ya kurma wani uban ihu wanda yasa sumammen yaron dake hannunsa ya farka tareda kafe matashin dake riqe dashi da manyan fararen idanunsa waɗanda suke farare dasu tas tamkar bana namiji ba.

Azabar harbince tasa matashin ya fara qoqarin sakin yaron amma kuma se yaron ya qanqame wuyan rigarsa qyam tareda runtse idanunsa a lokacin daya saddaqar da cewar tabbas rabuwarsu tazo koda kuwa basu shiryawa hakan ba.

Burki yaja a lokacin da suka iso gabar wani babban dutse wanda ke fitar da ruwa daga tsakiyarsa, daqyar yake iya ɗaga qafafunsa wanda ke cikin wata farar safa wadda sabida wahala ta koma nau'in wata kalar daban, gabaɗaya qarfinsa ya gama qarewa amma sabida baqin naci gamida wutar Muradin dake cin zuciyarsa yasa har wannan lokacin be yanke qauna ba akan cewar zasu iya cigaba da rayuwa ba.

A haka ya samu wani guri daga jikin dutsen ya kwantar da yaron tareda bubbuga kumatunsa Alamar ya buɗe idanunsa, a hankali yaron ke buɗe idanunsa harya gama buɗesu tas akan hannun matashin wanda keta zubarda jini tamkar an buɗe bakin fanfo, lokaci guda kuma ya zabura ya qanqame matashin tareda fashewa da wani irin kuka yace "Banaso wani Abu ya sameka Dady idan har wani abu ya faruda kai a sanadina har abada zanyi dana sani!!!

Zareshi daga cikinsa yayi lokaci guda kuma wasu zafafan hawaye suka keto masa sannan ya dubi ɗan nasa cikeda soyayya irinta ɗa da kuma mahaifi yace " lokaci yayi HATEEM dole ne mu rabu a wannan ranar muddin kanaso ka sake ganina da raina a tareda gangar jikina, don haka ka saurareni dakyau Hateem nasan shekarunka sunyi qaranci su fahimci abinda nakeson sanar dakai, duk rintsi duk wuya kada kayi wasa da shan maganin ka!!!! Matashin ya faɗa a lokacin da yake miqa masa wata qaramar jaka dake rataye a bayansa.

hawayene suka sake zubowa Hateem a karona biyu sannan ya buɗe baki dayar yace " idan ka tafi kabarni a nan Dady waze dinga kula dani idan ciwona ya tashi?

Haniniyar dawakai sukaji a dabda su alamar mahaya kan dawakan na dabda riskar inda suke lokaci guda kuma suka juya a tare suna masu kafe ƙofar kogon dutsen da idnu cikeda tsoro.............. Cikin sauri matashin ya janye yaron daga gabansa zuwa bayansa lokaci guda kuma ya fuskanci yaron yace "ka saurareni da kyau Hateem a kwai wata qaramar waya a cikin jakar nan lallai karkayi wasa da ita idan har Allah ya nufa na tsira da rayuwata to da ita zanyi amfani wajen gano inda kake...

kuka sosai Hateem yakeyi tareda qara qanqame rigar mahaifin nasa dake hannunsa yace "kayi min alqwari cewar zaka dawo gareni a raye ba tareda wani abu mara kyau ya faru dakai ba!!!

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now