CHAPTER 21

94 6 0
                                    

MURADIN RAI

zm~chubaɗo

21

A hankali  take buɗe idanunta har ta kammala buɗe su tsaf  akan kamilalliyar fuskar sa. wadda ke ɗauke da sahihiyar nutsuwa me tushe da kuma Asali,  da Sauran guzrin dayay mata saura ta miƙe tareda gyara zamanta bisa tattausan kafet ɗin da yaywa falon ƙawanya,  cikin Nutsuwa Baba Mairoji ta ce

"wace nasara zaka cimmawa a sanadin Rabomu da muhallin mu da kayi?"

Ta jefa masa tambayar cikin yanayi irin na wanda ke buƙatar ƙarin bayani.

Tsareshi tai da idanunta waƴanda suke ɗauke da baiwa irinta kwarjini  mara misali,  cikin yanayi na zallar ƙosawa ta buɗe baki tace "bansan meye manufar ka nayin hakan ba amma koma me kake shirin aikatawa ubangiji shine a saman komai na........."karki ce komai bayan abinda bakinki ya furta a ƙarƙashin rinjayin harshe ki Mairoji."

Malam dake bayanta ya furta hakan cikin yanayi na nutsuwa ba tareda hargowa ba,  juyawa tai itama a nitse tana me kafeshi da idanu tace "A iya sanin danai maka Malam baka taɓa aiwatar da wani abu ba tareda ka nemi shawarata ba, amma se gashi a wannan karon ka ɓalla tarihin daka daɗe kana ginawa a zamantakewa ta dakai, shin meyasa kayi hakan malam kodai akwai abinda kake ɓoye min ne?"

Mairoji tayi maganar tana jiran taji ta bakinsa.

Alhaji Abubakar ne ya dubeta cikin tattausan harshe ya fara magana kamar haka

"Baba dalilin daya sa na Ɗakko ku shine a jiya Al'uma  gari sun farga cewar Zainab bata mutu ba tana Raye."

A furgice ta juyo gareshi cikin yanayi irin na zallar kaɗuwa tace "what are you trying to say Abubakar?"

Tsohuwa Mairoji ta faɗi hakan zuciyar ta na bugawa da wani irin ƙarfi.

Ɗaga mata kai yayi Cikeda son tabbatar da zancen sa yace " shiyasa na yanke wannan hukuncin na ɗaukeku daga inda kuka ɓoye kanku tsahon shekara 1 ."

Wani irin kallo Malam Khabir Shamsuna  kebinsa dashi cikeda ɗaurewar kai yace "taya akai mutane suka san ƴata Zainab tana Raye bayan Rashin imanin da wasu daga cikin manyan ƙasar nan sukai mata?,  Sannan kuma kai taya akai kasan za'a bibiyi inda muke Rayuwa don a sake Farautar Rayuwar ta a karo na biyu  har kayi tunani ka taimake mu?"

Cikin yanayi na ƙarawa kai ƙarfin Gwiwa Alhaji Abubakar Jardawa ya buɗe baki yace  "don Allah Malam Shamsuna ka kwantar da Hankalinka wllh banida wata mummunar niya akanku face manufa ta Alkhairi"

Maganar mu kwantar da hankalin mu Alhaji duk bata taso ba,  indai har kaima ba'a cikinsu kake ba babu ta yanda za'ai ka samu wannan masaniyar na za'a farauci Rayuwar mu da kuma ta ƴar mu Zainab!!  Wannan maganar daka faɗa tasa naji  ina zarginka, Don manzon Allah ka gaya mana waye kai da kuma dalilin dayasa kake kusanta Rayuwar mu da taka?"""

Baba Mairoji tayi maganar cikin karaji tareda ƙoƙarin miƙewa tsaye zuwa inda Malam shamsuna da Zainab wadda ke gefansa take.

Wata irin zufa ce ta fara ketowa Alhaji Abubakar Jardawa sabida tsabar tashin hankalin da tambayoyin su suka jefashi.

Zare hular dake kansa yayi sabida gumin daya fara karyo masa ta cikin  sumar dake kansa,  ganin irin kallon da suke masa ne yasanya shi shan jinin jikinsa.

Goge zufar dake kansa yayi da farin hankicin dake hannunsa cikin gajeran lokaci alhini ya baiyana a saman fuskarsa Cikin yanayi na Rashin ƙwarin gwiwa ya dubesu da   gajiyayyun idanunsa  yace

"da farin kafin na baku amsoshin tarin tambayoyin ku zanso ku san cewa duk ɗuniyar nan babu wanda yake da kyakkyawar Alaƙa da Zainab shamsuna kamar ni Alhaji Abubakar Jardawa!..."

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now