CHAPTER 17

99 7 0
                                    

🧊🧊🧊 🧊🧊🧊
🧊🧊🧊
*MURADIN RAI*
*(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : ZAINAB MUHMD CHUBAƊO ✍️_*

*kukan kurciya..👇*

*Duk wata marubuciyar data ɗau alqalami to dole tanada manufar datake son ta cimma a Rayuwata Walau me kyau ko akasin hakan, Shiyasa dukkan abinda hannun mu ze rubuta ubangiji ke ajiye mana shi a cikin record ɗinmu Har zuwa ranar da ƙiyama zata tsaya, badan komai ba sedan ya zama hujja a garemu Ranar Sakamako, idan kunga dama ku tsaftace alqalaminku Iya ruwa fidda kai 🤷‍♀️*

Banyi editing ba🙅‍♀️

Page:17

____Har suka shiga Mota be dena kallonta ba matsawa tai daga jikinsa zuwa ƙofar wani shop tareda buɗe jakarta ta ɗakko kuɗi suna magana da matar dake cikin shagon, daga yanda sukewa juna dariya kaɗai zaka fahimci cewar sun san juna ajiyar zuciya Benazir ya sauke lokaci guda kuma ya lumshe idanunsa tareda jingina da jikin kujerar dayake zaune akai.

Seda sukai tafiya me ɗan nisa sannan Jardawa katse musu shirun ta hanyar faɗin "da alama dai wannan budurwa ba ƙaramar sa'a ta taka ba yau da alama ta gama birkita maka lissafi da salonta."

Yay maganar yana kallon Aminin nasa lokaci guda kuma ya maida hankalinsa ga tuƙin motar yana ƙara tsananta murmushin sa.

Shidai bece dashi ƙala ba kamar wanda ke ciwon baki bayan sun isa gida Sallar la'asar sukayi sannan Jardawa ya dubeshi cikin shirin fita yace "to ni zan koma gurin Hajara don ɗazu ban samu mun tattauna da ita yanda ya kamata ba muka tafi, idan kana buƙatar wani abin sekamin waya." yana gama maganar ya juya tareda fara ƙoƙarin buɗe ƙofar falon .

Buɗe lumsassun idanunsa Benazir yayi ya dubi abokin nasa yace "da mota zaka fita ne?"

Yay maganar yana jiran amsa daga gareshi. Murmushi yayi tareda nuna masa mukullin motar dake kan stand ɗin dake falon sannan ya fice zuwa gidansu abar ƙaunar sa wato Hajarah.

Jardawa na fita shima ya miƙe tareda ɗaukan key ɗin motar ya fice daga gidan bayan ya kulle, kai tsaye gidan tarihin da suka je ɗazu ya koma tareda samun guri ya faka motar ba tareda ya fito ba kimanin wasu ƴan lokuta sannan ya fito ya nufi wannan shop ɗin da yaga ta tsaya ɗazun sunyi magana da matar dake ciki.

Kasancewar ta ba musulma ba yasa be mata sallama ba amma dukda hakan be hanashi gaisheta cikin girmamawa ba yace "madam don Allah yarinyar datazo bakin shagon nan ɗazu wadda ke sanye da baƙar riga tareda wata ƙaramar yarinya nake nema, shin ko kin san unguwar da take pls?"

Yay mata tambayar yana kafeta da dara-daran idanunsa alamar yana jiran jin amsa daga bakinta.

Dariya matar tayi tace "oh kana nufin Aisha kenan ai a nan baya suke zama tareda mijinta da kuma ƴarta Fatimah, kullum tana zuwa nan gurin se yamma yayi sosai sannan mijinta Abdullahi ke zuwa ya ɗauketa bayan ya taso daga aiki, suna matiƙar son juna ita mijinta Hasali ma ban taɓa ganin masoyan da sukai ƙarko Wajen nunawa junansu zallar soyayyar gaskiya ba kamar su.!"

Ta ƙarasa maganar da murmushi kwance a saman fuskarta, wanda ke nuni da irin yanda masoyan ke matiƙar birgeta

Tunda ta fara magana zuciyarsa ke lugudan bugawa har zuwa lokacin data dasa aya, kallo ɗaya zakaiwa ƙwayar idanunsa ka fahimci zallar tashin hankalin dake kwance a cikinsu lumshe idanunsa yay tareda buɗesu tar a kanta, lokaci guda kuma ya gaiyato jarumtar datai masa saura tareda wadata fuskarsa da murmushi yace "kai amma ni kaina sun bala'in burgeni musamman yanda suke nunawa junansu so, nikam zanso na gana da mijin nan nata kodan na ƙara jinjina masa." dariya matar tayi sannan tace "ai gidansu daga nan ba nisa sosai kana fita hannunta na dama zakabi har zuwa ƙarshen titin to gidan farko shine nasa."

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now