MURADIN RAI chapter 6

134 8 0
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page: 6

____✍️ fasa maganar yayi illa wani ƙayataccen  murmushi daya sakar masa,  lokaci guda kuma suka gyara lab cord ɗin dake jikinsu kusan a tare,  Ajiyar numfashi ɗayan ya sauke tareda kallon  abokin aikin nasa yace "ka kwantar da hankalinka Dr. Senake gani kamar be dace ace ka tsareni da tarin tambayoyi ba a lokacin da muke gabda cimma nasarar da bamu taɓa samun kamarta ba."

Yay maganar yana tsare abokin aikin nasa da kallo.

Ajiyar zuciya yaɗan sauke a gajarce sannan yace " se yanzu na Fahimceka  nikaina nasan  A halin yanzu  aikinmu yana gabda kammala duba da yanda wancan yaro  yake fafutuka da ransa wajen jan numfashi a daran jiya amma kuma yau se gashi mun samu nasara wajen samar da dedaituwar komai cikin ƙanƙanin lokaci,  ni'a ganina wannan babbar  alama ce ta muna gabda cimma nasarar da muke fata akan binkicen ƙwayar cutar kansar jinin da aka ƙirƙira da kuma wadda ke  wanzu a jikin mutum da kanta."

Gyara tsaiwarsa ɗayan yayi yana me ƙara wadata murmushin dake kan fuskarsa yace "lallai Dr. Feruz har yanzu da sauranka, wannan yaron fa da kake gani  ba maganin da muka samar aka gwada a jikinsa ba, Shifa Allurar samfuri   ƙwayar cutar kansar jinin da aka ƙirƙira ce na gwada akansa don kawai muga irin tasirin datake dashi ne yasa nai hakan."  

Ya faɗi hakan yana nuna Hateem wanda ke kwance idanunsa duk a ƙafe

Zaro idanu Dr. Feruz yayi yana kallon Dr. Hamza bala cikeda zallar kaɗuwa yace "Hazbunallahuwani'imalwakeel !  Yanxu kana nufin wannan yaron da baiji ba kuma bai gani ba shi za'ayiwa wannan zaluncin?  Meyasa zakuyi masa haka? Tabbas wannan zalunci ne marar misaltuwa da kwatance, wannan yaron dake fama da  Asthmatic problem wannan kaɗai be isa yasa ku tausaya masa ba?"    

Dr. Feruz ya faɗi hakan idanunsa na cikowa da wata irin ƙwalla wadda tafi kamada ta zallar tausayinsa ga Ɗan yaro Hateem wanda idanunsa ke ƙafe har'i wannan lokacin.

Ɗaga kafaɗunsa Dr. Hamza bala yayi cikin yanayi na rashin nuna damuwa da abinda Dr. Feruz ɗin ya gama faɗa yayi sannan ya dafa kafaɗunsa yace "kaga Dr. Arfat Feruz wannan maganganun naka bani ya dace ka tsaya kana gayawa su ba,  Idan har da gaske kana ƙalubalantar hukuncin dana zartar ne tobani ya kamata ka fara tuguma ba illah Dr. Mai-nasara,  sedai kafin ka aikata wannan kuskuren yanada kyau ka fara tuna irin makomar da Dr. Muhammad Yusuf ya samu kansa a ciki a lokacin da yayi irin wannan abinda kake ƙoƙarin yi na ƙalubalantar mahukuntan Babban Zaure,  Idan kuma ka shiryawa hakan to bisimillah bazan hanaka ba."  

Dr. Hamza bala ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar ƙwayar idon Dr. Arfat Feruz wanda jin tinin da hamza bala yay masa akan makomar da Dr. Muhammad yusuf ya samu kansa a ciki shekara ɗaya data gabata yasa wata irin zufar Tsoro ta fara karyo masa.

Nan da nan wani irin tsoro ya tsirga masa a lokacin da abinda ya faru da Dr. Muhammad yusuf ɗin ya shiga dawo masa a kansa tamkar a lokacin abin ke faruwa, tabbas idan har yana son kansa da arziqi tofa ya zama dole ya manta da wannan maganar kuma ya sanya musu idanu akan dukkan abinda suke son aikatawa na zalunci, idan har ba haka ba tofa ze jawoma kansa bala'in daze kawo ƙarshen Ahalinsa ne gabaɗaya  kamar yanda akaiwa Dr. Muhammad Yusuf !!

Murmushi Dr. Hamza bala yayi yace "zefi maka kaja bakinka kayi shiru idan ba haka ba kuma kajanyoma kanka bala'i."       A haka dai suka fita daga ɗakin kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarsa

Har suka koma offisoshinsu  tausayin Hateem na ƙara yawaita a duk wani lungu da saƙo na zuciyar Dr. Feruz, tabbas yazame masa wajibi ya taimaki wannan ƙaramin yaron koda kuwa hakan yana nufin tsallake rijiya da baya ne, dole ne ya canza salo tayanda babu wanda ze zargeshi akan yunƙurinsa na taimakawa  wannan yaron, tabbas seya bijiro musu ta hanyar da basu taɓa zato balle tsammani ba wannan shin MURADINSA  insha Allah! 

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now