CHAPTER 16

106 7 0
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

*MASU MIN SHARING ƊIN WANNAN LITTAFIN  WAƳANDA NA SANI DA WAƳANDA MA BAN SANI BA UBANGIJI YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNA DON ALFARMAR MUHAMMADURRASULILLAHI🤲*

Banyi editing ba 🙅‍♀️

Page:16

___Kauda kai Dr. Arfat Feruz yayi sannan ya maida kallonsa ga Dr. Mainasara yace "Ranka ya daɗe ni'a ganina zefi mu maida hankalin mu ga ƙaramin Yaron da Samfurin cutar ke jikinsa a madadin mu tsaya bibiyar ƴan leƙen Asirin da sukai mana kutse, tunda a zahiri koda ƙalubalantar mu suke son yi basu da wata ingantacciyar hujjar da zasuyi hakan tunda Akwatin da suka sata ɗin ta ƙone tareda motar gabaɗaya, sannan kuma idan mukai la'akari irin ƙarfin jinin da yaron yake dashi kaɗai ya isa yasa mu cimma nasarar da kake Sabida kaf yaran da akawaiwa allurar sun mutu amma kumashi har yanzu yana numfashi."

Dr. Feruz yay maganar yana ɓoye zallar fargaban dake cikin zuciyarsa.

Murmushi Dr. Mai-nasara yay cikeda gamsuwa da magan-ganun Arfat Feruz yace "maganar ka gaskiya ce amma dukda hakan be kamata mu zubawa lamarin idanu ba dole ne mu binciko su akan lokaci Tun kafin su ɓallo mana wata matsalar me zaman kanta." 

Da wannan tattaunawar taron Babban zauren ya dasa aya don haka kowa ya miƙe yabar harabar gurin  gabaɗaya .

          *****

Tunda Dad yabar zaria be dire ko ina ba se babban Asbitin sa dake unguwar rimi inda Noor ke aiki, kana kallonsa zaka fahimci irin zallar tashin hankalin daya ke ciki gameda condition ɗin da Hajiya Aishar, buɗe masa murfin motar guards ɗinsa sukai ya fito, ɗaga idanunsa yay yana kallon tamfatsetsen Ginin Asbitin sannan ya fara tafiya cikin Sauran ƙarfin dayay masa saura masu tsaronsa na take masa  baya.

Tun daga harabar Asbitin ma'aikatan suka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa yana ɗaga musu hannu har ya isa ƙofar ɗakin da aka kwantar da mom ɗin. Murɗa handle ɗin dake jikin ƙofar yay kafin ya shiga ciki ya dubi guards ɗinsa dake bayan shi yace "ku dakata daga nan."  be jira cewarsu ba ya kunna kai zuwa cikin ɗakin,  ɗaki ne na gani a bada labari sabida kyau da kuma ƙawatuwarsa Abinka da masu abu da abun su,

Jikin gadon ya ƙarasa tareda zuba mata dara-daran idanunsa A kan fuskarta wadda ta sauya a lokaci guda, wani irin abu ne yazo masa wuya ya tokareshi a lokacin dayaga siraran hawaye suna zubowa daga hutsiyar idanunta  dukda kasan cewar su a rife.  Tabbas yasan abinda kecin zuciyarta ne yake bawa hawayen nata damar zuba babu ƙaƙƙautawa.

Safa da marwa ya shigayi a tsakiyar ɗakin Zuciyarsa na wani irin tafasa tabbas yasan yana matiƙar son Aisha Irrin sonda  baze taɓa bari wani tsautsayi ya hau kanta ba koda Kuwa abinda ya mallaka ze ƙare ne gabaɗaya, yafi kowa sanin cewar Aisha ita kaɗai ce Rauninsa a duniyar nan bayan ita se ɗiyarsu wato Nooreyn.

A zahiri sonda yakewa Mom a cikisa ne ya ɗaki kaso ɗaya ya ɗorawa Noor wadda duniya suke mata kallon cewar itace Rayuwar sa ma gabaɗaya.

Zarya ya dingayi a ɗakin yana tunanin yanda zeyi da Abubakar Jardawa  wanda ke ƙoƙarin ya warware masa duk wata tufkar sa daya daɗe yana kitsawa, kujerar dake gefan gadon yaja ya zauna  tareda dafe kansa dake masa barazanar tarwatsewa.

*WAI MENENE AINIHIN ALAƘAR DAKE TSAKANIN ALHAJI ABUBAKAR JARDAWA DA KUMA ALHAJI ALQASIM BENAZI?*
FLASH BACK

Alhaji Abubakar jardawa Amini ne ga Alhaji Alqasim Benazir wanda suka taso tun daga yarinta, komai nasu tare sukeyinsa Tun daga kan sutura   har makaranta, idan ka gansu zakayi tsammanin cewar Ƴan uwan taka ce a tsakanin su bawai abota ba Sabida komai nasu iri ɗaya sukeyinsa, wannan amintar tasu ta samo asalin ne a sanadin amintakar dake tsakanin iyayensu maza

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now