MURADIN RAI chapter 7

140 11 0
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page: 7

_____✍️Kallonsa tayi tace "muje ko?"   Ba musa yabi bayanta Har suka isa inda motar take, cire lock ɗin motar tayi sannan yasa hannunsa na hagu ya buɗe mufin motar ya shiga Ya zauna tareda zubawa glass ɗin gaban motar dara-daran idanunsa.

Bata sake cewa komai ba haka shima bece da ita koman ba ta jefa motar kan titi ta ɗauki hanyar gida a madadin ta Asbiti, kallonta Abou hateem yayi  zuciyarsa na bugawa da manyan fararen idanunsa waƴada ke ƙara masa kwarjini yace " ina zaki kaini?"

Batareda ta kalleshi ba ta ɗora hannunta akan lips ɗinta alamar yay shiru tukunna, be sake magana ba ya maida kallonsa kan titi yana kallon mutanen dake wucewa jefi-jefi, seda sukaɗanyi tafiya me nisa kafin  yaga ta saita hancin motar a gaban wani danƙareren gida

Horn tayi  meɗan ƙarfi sannan Ɗanjuma mai gadi ya buɗe mata get ɗin cikeda girmamawa,  kasancewar motar a lulluɓe take da tinted yasa mai gadin be samu zarafin ganin Abou Hateem wanda ke zaune a gaban motar ba,  direct parking lot ta nufa tayi parking motar sannan ta dubeshi da murmushi kwance saman fuskarta tace "sakko mu shiga."   Yatsina fuska yayi wanda ta lura hakan ya zame masa tamkar ɗabi'a tun kafin ya kaiga faɗar abinda ke ransa ta dakatar dashi ta hanyar cewa "kaga yallaɓoi ka adana duk wata magana dake bakinka zuwa Ɗan wani lokaci   sekayi Bayan Munci abinci na huta."   Ɗaure fuska yayi babu alamun wasa a taredashi still He's  eyes on her face amma kuma ya gaza cewa komai.

Ajiyar zuciya yaɗan sauke a ɓoye sabida yarda da shawarar da zuciyarshi ta bashi, tabbas idan har Ciwon dake Hannunsa be warke ba duk wani shirinsa baze Taɓa tafiyar masa a yanda yakeso ba, dole ne yayi haƙuri har zuwa lokacin da hannun ze warke kamin ya cimma manufarsa a halin yanzu. "to amma Abou Hateem haka zakabar yaro ƙarami a wani gurin yana rayuwa da Mutanan da bakasan irinsu ba menene  tabbacinka na cewar yana cikin ƙoshin lfy?"  "Shin kasan irin halin dayake ciki a yanzu?  Idan kuma ya kasance ciwonsa ya tashi fa?"      Wani ɓangare na zuciyarsa ya gaya masa hakan.

Damuwa ce ƙarara ta sake baiyana a saman fuskarsa, kamar daga sama ya sakejin muryar Noor wadda ta kasance tamkar shamaki a gareshi na hanashi tunanin daya samu kansa a ciki  a wannan lokacin.  "sakko." shine abinda Noor ta faɗa yayinda ta buɗe masa murfin motar daga ɓangarensa.

Ba musu ya sakko kamar yanda ta buƙata kasancewar  lokacin sallar magaruba yayi ne yasa babu securitys sosai a gidan se kaɗan daga ciki ne ke zagaye kasancewarsu kiristoci,  gaba ta shige yana binta a Baya a haka har suka isa part ɗinta

Shidai kawai binta yake yana Ƙarewa  ko ina Kallo a ransa yana girmama irin tarin dukiyar da aka ɓarnatar wajen  gina wannan gida, uwa uba kuma irin kayan alatun da aka zuba a gidan

A hankali tasa hannu ta murɗa handle ɗin dake jikin ƙofar wanda zata kaisu asalin maine perlour ɗin , tana buɗewa da wani kantamemen hotonta yay karo wanda a tsaye frame ɗin hoton ya ninka girmanta so ɗaya da rabi, furkarta ɗauke da wani kyakkyawan murmushi a jikin hoton, taɓe baki yayi tareda kauda fuskarsa gefe a ransa yace "Almubazzaranci."

Suna shiga da sauri Harira mai aiki wadda ke kula da duk wata hidima na ɓangaren Noor ta iso garesu tana faɗin "sannu da zuwa Ranki ya daɗe." Mun riga mun gama shirya komai a daining da zarar kinyi sallah da sauran buƙatunki kamar yanda kika saba sakkowa kawai zakiyi."

Wata gajeriyar Ajiyar zuciya Noor ta sauke sannan ta dubi Harira tace "ga baƙona nan ki kaishi wancen  ɓangaren sannan ki bashi duk wani  abinda yake buƙata pls." Noor ta faɗa tana nuna wata ƙofa dake cikin falon itama

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now