CHAPTER 19

90 9 2
                                    

____Gabaɗaya ya gama saddaƙarwa da kansa irin Mummunan haɗarin da zasu tabka Ta sndi wannan me baƙar jib ɗin dake gabansa, Rintse idanunsa Yay da wani irin ƙarfi babu abinda yake iya furtawa face kalmar ''innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!"

Gabaɗaya mutanen dake gurin babu wanda be shiga tashin hankali ba shiyasa duk suka tsaya suna kallon sarautar Ubangiji da kuma buwayar sa.

Amma Cikin Ikon Allah da hikimarsa se matuƙin ɗaya motar yay saurin taka birki tareda juya motar zuwa wani gefan daban, shirun dayaji tayi yawa ne yasa ya buɗe idanunsa a hankali don ganin abinda dake shirin faruwa, Wani dogon fasali yaja tareda fara jerawa ubangiji godiya da kirari sakamakon ƙudurarsa daya saukar a wannan lokacin.

Haƙiƙa ubangiji me hikima ne akan dukkan komai, babu shakka duk wanda ya riƙi ubangiji a matsayin ma jinginar sa to tabbas ya isar masa. Kafin kace me tuni mutane sun fara taruwa kowa da abinda da yake faɗa akan akan ƙudurar da ubangiji ya nuna a wannan lokaci, sabida kowa ya gama yanke ƙauna akan se hatsarin ya abku seka hukunci daga me kowa me komai ya sauka.

dayake Wani abu mumuna be faruwa ba yasa kowa ya watse ya shigaharkan gabanshi, da wannan damar Saleym yay amfani ya tsaya a bakin wani Babban pharmacy yana sauke numfashi akai-akai, ya jima a zaune cikin motar sannan ya fito jikinsa a mugun saliɓe ya rufe murfin motar da sauran ƙarfin daya rage masa, da ɗan hanzari ya nufi cikin Phamarcy ɗin harda sassarfan shi ya shige ciki kamar wanda ze siya wani abin a ciki se kuma ya fice ta ɗaya ƙofar kasancewar gurin ƙofa biyu ne dashi.

Mutumin dake Biye dashi shima parking yayi a gaban gurin ba tareda ya fito ba yana jiran fitowar Saleym ɗin, seda ya ɓata lokaci me tsayi yana aikin jiran fitowar sa amma yaji shiru, hakan yasashi fitowa daga motar ya shiga gurin se faman Raba idanu yakeyi koze ganshi.

Ɓangaren Saleym kuwa yana fita Wayarsa ya cigaba da nema amma bega babban ba se ƙaramar Wayan ya gani, number Noor yay dailing bugu ɗaya ta ɗauka cikin sanyinta tace

" Sweet ya mukaji ka shiru har yanzu?"

Lumshe idanunsa yay tareda sauke numfashi yace "ba yanzu ya kamata muyi wannan maganar ba baby, yanzu dai kiyi duk me yuwuwa ki ɗauke Abou Hateem daga wannan Asbitin zuwa gidan mu, sannan karki yarda wani baƙuwar fuska ya ganshi balle har ki tsaya rubuta mishi takardan sallama, kiyi sauri kuzo yanzu don na fahimci akwai waƴanda ke bibiyar mu a cikin Asbitin naku."

Gabanta ne yay wani irin faɗuwa lokaci guda kuma idanunta suka firfito tace

"innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un to yanzu ya zamuyi kenan?"

Numfashi ya kuma saukewa sannan yace "Duk wannan ba maganar Yanzu bace just do as i say pls."

Saleym yay maganar tareda katse wayar yana ƙoƙarin tare me keke napep ɗin dake shirin wucewa ta gabansa yace

"nan cikin Unguwan Rimi zaka kai ni pls."

Shiga yay ba tareda ya tsaya jin ta bakin me Keken ba suka nausa cikin Unguwan Rimi, a ransa yana hamdala ga ubangijin daya bashi ikon tsira daga makircin waƴanda ke bibbiyarsu.

tun kafin su shiga layinsu Saleym ya sauka sabida gudun abinda ka iya biyo baya idan har yabar me Keken yasan gidan daya shiga, a yanda yakeji a ransa sam be yarda da kowa ba yanzu musamman ƴanda mutanen wannan zamanin suka canza tsaf zasu iyayin komai akan kuɗi. 1k ya zaro daga aljihun gaban riganshi ya mikama masa sannan yay gaba abinsa, seda ya tabbatar da me keken ya wuce sannan ya juya ya shiga layinsu Cikin hanzari ya isa ƙofar makeken Get ɗin gidan.

Malam Musa Mai gadinsu dake zaune yana ɗaura Alwala yaji ana ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar dake jikin get ɗin cikeda Sababi yace

"yau naga abinda ya isheni be ishi Ubangiji na ba, wannan wace irin jarabace ni kalamu? Sabida Allah mutane kuyita dukan ƙofar gidan jama'a sekace tsoho da tsohuwa ne suka sai musu ƙofar fisabilillahi?"

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now