MURADIN RAI chapter 4

135 10 0
                                    

🧊🧊🧊 🧊🧊🧊
🧊🧊🧊
*MURADIN RAI*
*(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page: 4

_____✍️Seda ta gama sharar kukanta sannan tama motan key ta kama hanyar gida, tana shiga ko perking bata gamayi dedai ba ta fita tabar motar haka nan ta nufi part ɗinta da wani irin sauri, tana shiga da Harirah ta fara cin karo cikeda girmamawa ta zube qasa tana gaisheta ɗaga mata hannu takawai Noor tayi sannan ta fara haurawa stairs, tsayawa tayi cak batareda ta juyo ba tace " Harira yau kada ku haɗamin breakfast kuma duk wanda yazo nemana kada kibarshi ya shigo indai ba Daddyna bane." Noor ta faɗi hakan tana haurawa da saurin gaske, tana shiga ɗakin wayar dake hannunta ta jefa a saman gadon a gurguje ta Faɗa toilet tayi wanka tareda ɗauro Al'wala.

Koda ta fito Sallah kawai ta iyayi sannan ta miƙe ta faɗa kan makeken Gadonta cikin ƙanƙanin lokaci bacci me nauyi yay Awon gaba da ita.

**********

A can Q/B special Hospital 🏥kuwa A hankali yake buɗe idanunsa yayinda siraran laɓɓansa ke motsawa a hankali wanda ba lallai ka iya jiyo abinda yake faɗa ba har indai har ba matso da kunnenka dabda bakinsa kayi ba, salati yakeyi har ya gama buɗe idanun nasa tar a saman kyakkyawan silin ɗin dake ɗakin.

ajiyar zuciya ya sauke meƙarfin gaske a lokacin da komai ya shiga dawo masa fila-filla tamkar a lokacin abin ke faruwa, wani irin tsoro ne ya tsirga masa a lokacin daya tuna halin dayabar Hateem ɗinsa a ciki, a razane ya fara ƙoƙarin miƙewa cikin wani irin yanayi wadda ke baiyana ujilarsa ga abinda yakeson yin, wata ƴar siririyar ƙara ya saki tareda dafe saitin gefan hannunsa na dama inda aka nannaɗe da bandeji, se a yanzu ya tuna harbin bindigar da akai masa

Sake Yunqurawa yay da sauran Qarfin daya rage masa a karo na biyu ya zauna tareda zarewa
kansa igiyar ruwan dake ɗaure a hannunsa, tsoro ne ya ƙara mamaye duk wani lungu da saƙon dake cikin zuciyarsa sabida rashin sanin a wace mazahabar yake, wata ƙofa ya maida hankalinsa akai tareda nufarta kansa tsaye cikin yaqinin gamida sanya ran cewar Toilet ne,

Yana turawa kuwa yay katari da hakan Yana shiga ya maida qofar ya kulle tareda kafe kansa da kallo cikin haɗaɗɗen mirror ɗin dake toilet ɗin, a hankali yakai hannunsa ya shafo kwantaccen sumar datayima kyakkyakwan fuskarsa ƙawanya,

Wani sabon tsoro ne ya sake wanzuwa a san zuciyarsa ji yake kamar mutannan dake farautar Rayuwarsa ne suka samu nasarar kamashi, idan kuwa har hakanne tabbas babu wanda ya isa ya kuɓutar dashi daga shartinsu!! Yana kaiwa nan a zancensa wata zazzafar ƙwalla ta tsatsafo a cikin fararen idanunsa waƴanda ke zagaye da sirrin kyau a taredasu, tap ɗin dake cikin sink ɗin toilet ɗin ya kunna tareda sanya zara-zaran hannayensa a qasan ruwan dake gudana ya fara ɗiba yana zubawa a saman kyakkyawar fuskarsa wadda tai wani irin fayau da ita.

Ya jima yana hakan sannan ya ɗaura Al'wala ya fito don rama tarin sallolin dake kansa, a nitse ya fito cikin yanayi na nuna jarumta ɗakin ya dingabi da kallo amma sam besamu nasarar Ganin abinda yake hasashe ko zargi ba akai ba, a hankali ya sauke idansa akan Uniform ɗin asbitin dake jikinsa wanda ya kasance me launin kalar sky blue da yarfen fari a jiki, gabansa ne ya faɗi a lokacin daya tuna number daze iya bin diddigin inda Hateem yake tana cikin aljihun wandonsa da aka cire masa aka sa masa wannan ɗan iskan Uniform ɗin.

ƙofar ɗakin yaji an buɗe don haka ya juya da sauri yana kallon Direction ɗin inda qofar yake yana jiran yaga wanda ze shigo ɗin cikin nutsuwa.

Ɗaya daga cikin Masu kula da ɓangaren tsafta na Asbitin ne ya shigo hannunsa ɗauke da bokiti da mop a ciki donya share ɗakin kuma ya goge, da hanzari Abou Hateem ya isa ga mutumin ya danƙi wuyan rigarsa da dukkan ƙarfin daya rage masa cikin kakkausar murya yace "A ina nake? Waye ya kawoni nan sannan kuma ina kayana suke?" ya jera masa tambayoyin duk a lokaci guda tareda tsareshi da manyan idanunsa waƴansa suka fito sabida fisara.

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now