MURADIN RAI chapter 2

201 15 0
                                    


*MURADIN RAI*
*(Abou hateem)*

*_ZM~CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page:2

____✍️Yana faɗuwa ƙasa Ƙarar ihunsa ta kai ziyara zuwa ga kunnuwan wani dattijo, wanda daga kallon farko idan kai masa zaka fahimci cewar ya ɗan fara manyanta,  a ƙalla  shekarunsa zasu iya haura hamsin da biyar baya koma fiyeda haka, amma sam yanayin jikinsa be nuna yawan shekarun da yake dashi a fili ba sabida tarin kwanciyar hankali dayake da ita.

daga kallon farko idan kayi masa  bazaka fahimci komai daga gareshiba, balle har ka samu zarafin iya tantance launin kalar fatarsa ko kuma gogewarta ba, ko kaɗan dattijon be kasance a cikin jerin masu duhun fata da ƙiba ba, balle a siffantashi da kauri kokuma murɗewar jiki ba, mutumne shi me cikar zati da kuma haiba, fuskarsa a zagaye take da wani siririn gashi wanda ya zagaye  bakinsa har zuwa gefan fuskarsa,  yanayin gashin ya kasance fari da kuma sirkin baqi a cikinsa, hakan yasa launin gashin ya ƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini.  a hankali yake takawa masu tsaronsa suna take masa baya, sanye yake cikin wata kakkaurar sweater  mallakin companyn Quwaid. Sosai rigar tabi lafiyayyen jikinsa ta kwanta tamkar don shi aka tanadeta, kasancewar rigar baƙa sosai ne yasa ta ƙara haska farar fatarsa ta fito tai ɗau kai kace wani dattijon ba'amurke ne.  .

Suna qarasowa inda yaron yake dattijon ya sunkuya qasa yana me qarewa yaron kallo tamkar wanda keson gano wani abu a taredashi, da hanzari ya maida kallonsa ga matasan dake take masa baya yace "maza ku ɗaukeshi a sashi a mota zuwa Asbiti da alama guzarinsa ne yay qasa." ya faɗi hakan yana kai hannunsa jikin fuskar yaron

Da sauri ɗaya daga cikinsu ya kinkimi Hateem dake kwance babu Alamar numfashi a jikinsa ya nufi ɗaya daga cikin manyan motocin su da sukai perking a tsakiyar jejin. Yana shirin buɗe motar kenan ya tsinkayi muryar Alhaji na faɗin "daga nan zuwa Asbiti ze ɗaukeku tsahon mintuna nawa ne?"

Cikeda girmamawa matashin yace "kimanin awa guda ne Ranka ya daɗe." Ɗan jim kaɗan mutumin yayi sannan ya kalli tsadadden agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yace " idan kuma Headquarter ɗin mu zaku kaishi ze ɗaukeka mintuna nawa ne?"

A hanzarce matashin yace "mintuna talatin ne Ranka ya daɗe. "
Murmushi mutumin yayi sannan yace "maza ka kaishi headquarter tunda yafi kusa ka tabbatar an bashi duk wani taimakon daya kamata har lokacin daze dawo cikin haiyacinsa." Cikeda girmamawa ya amsa da "ok sir " sannan ya buɗe bayan motar ya kwantar da Hateem ɗin shikuma ya shiga mazaunin driver yay mata ya tashi motar da mugun gudu ya ɗau hanya.

Ajiyar zuciya mutumin ya sauke sannan yay murmushi a hankali ya juya da nufin yabar gurin idanunsa suka sauka akan qaramar jakar dake yashe a qasa duk busassun ganyen dake jejin sun fara qoqarin rufeta, sunkuyawa yayi tareda kafe jakar da idanu batareda ya ɗauka ba, seda ya ɗauki lokaci me tsahon gaske yana kallon jakar sannan yay Ajiyar zuciya ya kai hannunsa kan jakar ya ɗauka, beceda kowa komai ba ya nufi gurin da sauran motocin ke ajiye da hanzari daya daga cikin guads ɗin ya buɗe masa murfin motar ya shiga ya zauna sannan ya rufe masa motar ya shiga mazaunin Driver, cikin mintunan da bazasu gaza biyu ba sauran guards ɗin suma suka mara musu baya cikin sauran motocin da suka rage A gurin, a haka sukabar harabar jejin cikin jerin gwano kamar yanda suka saba gwanin ban shi'awa.

******

Ɓagaren Noor kuwa tana barin gurin shagalin nasu bata dire ko ina ba se Q/B Special Hospital 🏥 Dake anguwan rimi, sosai take shara uban Gudu kamar zata tashi sama kasacewar dare yadan farayi yasa ta isa akan lokaci sabida rashin cinkoson ababan Hawa, tana isa Asbitin tai parking a inda aka tanada don yin hakan sannan ta buɗe motar ta fito cikin takunta na isa da Qasaita harta iso cikin reception ɗin katafaren Asbitin, tafiya tkeyi cikin sauri harta isa Bakin wanta qofa wandda aka rubuta consultant 1 a jiki, murɗa handle ɗin dake jikin ƙofar tayi qofar ta buɗe sannan ta kunna kai zuwa cikin office ɗin.

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now