CHAPTER 20

90 8 0
                                    

🧊🧊🧊 🧊🧊🧊
🧊🧊🧊
*MURADIN RAI*
*(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY :ZAINAB MUHMD CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page: 20

____Se wuraren ƙarfe uku da Rabi na dare sannan zirga-zirgar mutann dake bakin aiki ta fara raguwa, jakar da ake saka gawa idan mutum ya Mutu Dr. Arfat ya ɗauka ya nufi ɗakin da Hateem yake kwance, Allurar bacci me matiƙar ƙarfi ya buga masa dukda cewar bashida wata maraba da mataccen ya kinkime shi ya zura a cikin jakar ya zuge.

Sannan ya kinkimeshi ya fita dashi zuwa ɗaya ɗakin da aka maida sauran yaran ya Ajiye Shi a cikin jerin Waƴanda suka mutu, sannan ya kuma ɗaukar wani farin yaro daga cikin jerin waƴanda ke fafutuka da Numfashin su ya maidashi ɗakin da ya ɗakko Hateem ya kwantar dashi a Saman gadon Tareda lulluɓeshi da ƙaramin bargon dake gefe. Kasa tafiya yayi a lokacin dayake kallon irin yanda yaron ke shan baƙar wahala duk a sanadin cutar da aka sanya masa,

Kuka ne ya taso masa a lokacin daya auna irin Rashin imani da bushewar zuciyar da mutanan babban zaure suke da ita, tabbas dole ne ma Ubangiji ya jarabce mu da manyan bala'irorin da bamusan ikarsu ba Sakamakon innocent mutanen da ake kashewa waƴanda basuji ba kuma basu gani ba. Idanunsa dake zubar da hawaye ya ɗaga ya kalli Yaron tareda ɗaga hannayensa yace

"ya ubangiji karka karɓi Rayuwa ta har senaga ƙarshen Azzaluman da suka kafa wannan da'irar don su dinga zalintar marasa ƙarfi, ya Allah kaine a saman komai kuma babu wani al'amari daya isa ya ɓuya daga ganin ka, Allah kana jinsu kuma kana ganin su ubangiji ka Ruguza su kamar yanda ka ruguza Samudawa da Adaw......!!!"

Kasa ƙarasawa yayi sabida wani irin kuka daya taso masa.

Be daɗe da ajiye yaron ba Allah ya karɓi Rayuwarsa sosai hakan ya ƙara girgiza zuciyar Arfat Feruz, jikinsa a matiƙar mace ya fice daga ɗakin yana tsananta zubar hawayensa Kai tsaye Office ɗinsa ya wuce tamkar wanda ƙwai ya fashe masa a ciki, kan kujerar dake haɗe da table ɗinsa ya hau ya zauna yana ɗan jujjuyawa idanunsa a lumshe.

Be jima da zama ba ya samu Saƙo daga Babban zaure cewar a kwashe gawarwakin yaran da suka mutu aje a ƙona su A inda aka saba yin hakan don gudun kar maƙiyansu su samu hujjar dazasu ƙalubalancesu da ita.

Miƙewa yay bisa umarni Baban Zaure ya fita don aiwatar da abinda aka Umarce shi, wata babbar mota aka kawo me rufaffan baya wadda zata iya cinye adadin gawarwakin yaran aka fara zubasu a bayan motar, wasa wasa seda aka fitar da adadin gawarwakin yara sama da mutum Ashirin da biyar

Sabida tsabar tausayi Dr. Arfat besan sanda hawaye suka wanke mishi fuska ba seda suka gama jerasu tsaf sannan matuƙin motar ya shiga ya zauna yana jiran Umarni daga Dr. Arfat tunda shine ze jagoranci ƙona gawar a inda aka tanada don yin hakan.

Jikinsa a mace ya isa ga motar sa dake ajiye a gurin ya shiga ya zauna tareda yi mata key sukabar Harabar ma'aikatar, seda sukai tafiya me nisan gaske sannan suka iso get ɗin ƙarshe na fita daka Ma'aikatar, bayan sun fita wata hanyar daban suk kuma yanka tareda luluƙawa can cikin daji.

Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gurin da aka saba ƙunawar wanda yay dedai da bugawar ƙarfe huɗu na Asuba, wani babban gini ne me matiƙar girma da faɗi ƙofa ɗaya ce dashi kacal kuma bame girma bace tafi kamada normal ƙofa don haka mota bazata iya wucewa ta cikinta ba.

buɗe murfin motarsa Dr. Arfat yayi ya fito yana ƙarewa gurin kallo sabida wannan shine zuwansa na farko A Rayuwarsa, mamaki ne ya cika zuciyar sa na ganin ƙanƙanuwar ƙofar da akaiwa guri, wannan dalilin yasa yaji a ransa cewar akwai lauje cikin naɗi dan gane da wannan ginin

MURADIN RAI! (complete) Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang