MURADIN RAI CHAPTER 8

116 6 1
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

*_Alhamdulillah I'm back again bayan tsawon kwanakin dana ɗauka bana Online_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page:8

____✍️Tsayawa yay cak lokaci guda kuma ya tureta daga jikinsa yana bnta da wani irin kallo wanda yafi kamada na tuguma yace "kalamanki  da irin salon da kikai amfani dashi wajen yin maganarki yayi kamada nata, hakan yasa a raina naji  ina zarginki  wacece ke? !!!!

Abou Hateem yayi maganar yana wawurar cokali me yatsun dake ajiye bisa center table din dake gabansa tareda nufar inda Noor ke tsaye.

Ja ta farayi da baya tana kallonsa a tsorace  a zahiri so take tayi magana sabida yanda bakinta ke wani irin rawa  tsabar yanda ta tsorata dashi amma kuma ta kasayin hakan,   daga yanayin yanda yake nufarta gadan-gadan zakayi tsammanin mahaukaci ne shi, da dukkan ƙarfinsa ya isa gareta ya wani irin danƙo wuyan rigarta, Fashewa tayi da wani irin kuka sabida yanda ya haifar mata da tsoro marar misali.

Kamar wani ɗan daba haka ya fuzgota tareda sanya mata folk ɗin a saitin wuyanta har yana sukarta kaɗan yace "bazaki gayamin wacece ke ba  senasa cokalin nan na fasa miki wuya tukunna?

Idanunta ne suka tsananta tsiyayar hawaye kamar an kunna famfo still bakinta na rawa bata iya ce dashi ƙala ba, wurgar da ita gefe yayi yana fesar da wata  iska me zafi daga bakinsa, dafe kansa yayi tareda datse pink lips ɗinsa da fararen haƙoransa,  lokaci guda kuma ya ɗago jajayen idanunsa  yana kallonta a karona biyu jikinta se rawa yake kamar mazari.

Ja yay da baya yana dafe kansa kamar wani zararre  ya ƙara nufota tareda kafeta da wani irin kallo wanda yasa hantar cikinta ƙara kaɗawa da mugun ƙarfi,  murmushin gefan baki ya saki wanda ya ƙara birkita mata lissafi  sannan  ya Ƙara sunkuyowa dabda ita  a karona biyu tayanda har suna iya jiyo bugun zuciyoyin junansu  yace "sa'arki daya zargin danake miki be gama samun gurbi a zuciyata ba, amma tabbas idan kika bari kika faɗo cikin jerin waƴanda  zargina yafi yawaita akansu bisa  alhakin mutuwar zainab wllh bazan duba alkhairin da kikai a gareni ba kema zan kasheki har lahira. Abou hateem ya faɗi hakan yana nuna mata hanyar fita

Da sauri Noor ta miƙe ta nufi hanyar fita  daga falon har tana tuntuɓe sabida  waiwayensa cikin yanayi irin na  fitar haiyaci harta fice daga falon gabaɗaya, a ranta kuwa tsoronsa ne ya samu gurbin zama a zuciyarta yay kane-kane, sama ta haura ba tareda ta tsaya shafe-shafenta ba ta faɗa kan makeken gadonta tayi lamo lokaci guda kuma maganganunsa masu kamada kashedi suka shiga dawo mata a tsakiyar kanta, a haka wani wahalallan baccii ya ɗauketa.

Tana tsaka da kwasar baccin ne ta fara mafarki da  data sabayi a kowace rana muddin zata kwanta bacci to lazim ne a gareta tayi wannan mafarki

MAFARKI

Kwance yaron yake bisa gadon Asbiti hannunsa ɗauke da drip idanunsa a rufe ruf tamkar babu numfashi a taredashi, a hankali noor ke takowa harta iso jikin gadon da yaron ke kwance  ta shafi gefan fuskarsa tareda sakin murmushi, a hankali ta maida hankalinta kan drip ɗin dake rataye jikin qarfe ta fara ƙoƙarin saita yanayin saukar ruwan sannan ta maida kallonta ga fuskar yaron A karo na biyu, a hankali hawaye suka fara zuba daga idanun yaron waƴanda suke a rufe Ruf, hannunta takai zata share masa lokaci guda yaron ya buɗe idanunsa waƴanda  suka canza launi zuwa kalar green  tareda damƙe hannunta na dama cikin nasa yace "pls Dr.  Help  me out from here  I don't want to die plssssssss!!!!!!.    Yaron yaja pls ɗin  tareda sakin hannunta sabida yanda jikinsa ya fara  saki.

Da sauri ta fara jijjigashi lokaci guda kuma ta tsaya cak sabida ganin wata ƴar ƙaramar kwalbar allura dake damƙe a tsakiyar hannun yaron.

Zare kwalbar tayi daga hannunsa tana ƙarema kwalban kallo tamkar wadda keson gano wani abu a jikin kwalbar allurar. Muryar yaron ta sakeji a karona biyu cikin karaji  yace "pls help me !!!

Buɗe idanunta tai da sauri tareda miƙewa ta zauna a tsakiyar gadon, wata irin zuface take keto mata tamkar wadda aka watsama ruwa, ta daɗe a zaune ƙirjinta na bugawa jiki a matiƙar mace ta sakko daga gadon tana kai kawo ,  tabbas akwai abinda mafarkin nan yake nufi tunda har ta kasa cire abin a ranta, meyasa kullum takeyin wannan mafarkin idan ta kwanta bacci?

Kanta me ya ɗaure lokaci guda taci gabada zarya a ɗakin tana aikin tunani, tsayawa tayi cak yayinda ta ɗora hannunta na dama a saman tip lips ɗinta tana zaro idanu, juyawa tayi da sauri  ta nufi Inda take ajiye files ɗinta da sauran abubuwanta masu mahimmanci  wani blue ɗin file ta ɗakko jikinta a matiƙar saluɓe ta fara buɗewa.

Nan take fuskar wani kyakkyawan yaro ta baiyana gareta yayinda yake murmushi a jikin  hoton, a hankali tasa hannunta ta shafi fuskar yaron lokaci guda kuma hawaye suka fara sakko mata dukda kasancewarta  likita amma bata taɓa cin karoda abinda ya mugun tsaya mata a rai ba irin mutuwar  yusuf Muhammad Sardauna ba!!   Haka kawai takejin yaron Ranta, tabbas tasan akwai abinda yay silar mutuwarsa  wanda ita bata da masaniya akai,  gabanta ne yay wata irin faɗuwa yayainda zuciyarta ta fara aiyana mata  kodai mafarkin datake yawanyi idan ta kwanta bacci yanada nasaba da Mutuwar Yusuf ne?!!!!  Miƙewa tayi da sauri  a lokacin data tuna murfin Allurar data gani a hannunsa lokacin dayake kan gargaran mutuwa

da sauri take tafiya har tana bige gefan kanta ta isa ga wata ƙaramar drower ta buɗe, birkita drower ɗin tayi gabaɗaya amma kuma sam bata samu zarafin ganin murfin Allurar ba, watsi ta dingayi da kayan gurin har seda ta yanke hannu da abin drower sannan ta zube ƙasa tana maida numfashi hannunta kuma yana ɗigarda jini

Haushin kanta ne ya kamata a lokacin data tuna yau tsahon shekara daya kenan da mutuwar Yaron amma sam bata taɓa bawa yawan mafarkin datake dashi mahimmanci ba,  da ace ta bawa abin mahimmanci wata qila da yanzu ta gano Ɗaurin dake ɓoye!!   Kuka ta fashe dashi tanajin wani irim abu ya tokare mata maƙoshi,  seda tai mai isarta sannan ta miƙe da nufin ta shiga toilet idanunta ne suka sauka akan  murfin Allurar datake nema ruwa a jallo , ƙirjinta ne ya fara bugawa da ƙarfi a lokacin data ɗauki murfin Allurar dake ɗauke da tambarin inda allurar ta fito.

kuka ta farayi cikeda rashin sanin madafa a haka har aka fara kiran sallar farko na Asuba ammabata samu mtsaya aki ba amma ta ƙudurtawa kanta cewar tabbas seta bin ciko masu hannu a cikin wannan badaƙalar koda ace mahaifinta baze mara mata baya akai ba,  toilet ta shiga tai wanka sannan tayi brush tareda ɗaura Alwala ta fito pray mat ta nufa tai salla sannan ta miƙe ta nufi drower ɗinta ta zaro wata haɗaɗɗiyar Abaya baqa  wuluk da ita ta sanya a jikinta sannan tayi rolling, karona farko a Rayuwar Noor tayi shiga irinta kamala da mutunci a yayinda zata fita. a gaggauce ta ɗauki mukullin motarta da wayanta ta fita daga ɗakin da hanzari tareda ƙudurtama kanta cewar yau seta bin ciko sirrin dake ɓoye koda kuwa hakan na nufin ajalinta ne kuwa.

comment
Nd
Share

Chubaɗo✍️

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now