CHAPTER 22

98 10 0
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO ✍️_*

Banyi Editing ba 🙅‍♀️

Page: 22

_____Faka motar Saleym yay daga gefan titi cikin hanzari tareda zaro  Tracker ɗin dake Aljihun wandon sa yay disconnecting ɗinta,  kallon da ya mayar ga  Abou Hateem yace "ina ganin kai ya kamata ka tuƙa motar nan  ni kuma senaji dasu."

Exchanging sit sukaiyi Saleym ya koma dit ɗin Abou Hateem shi kuma ya koma nasa, system ɗinsa ya buɗe tareda ɗorata bisa kan laps ɗinshi ya fara latsa ta cikim ƙwarewa in less then a Minutes ya sake kafa wani tsaron bididdigin Dayaci ƙanaiyar na farko, sannan ya dubi Abou Hateem cikin yanayi na zallar farin ciki yace "we did it Abou Hateem. "

Gabakɗayan su babu wanda beyi farin ciki dajin wannan daddaɗan labarin ba Musamman Abou Hateem, cikin yanayi na zallar Farin ciki mara misali suka iso gida Horn Abou Hateem ya Matsa Malam Musa ya buɗe musu ƙofar Get ɗin ya danna Hancin motar zuwa cikin gidan, seda ya   isa inda aka tanada don faka motocin  ya juya yana kallon Saleym fuskarsa ɗauke da Alhini yace

Amma Saleym kana ganin babu wata matsala idan mom ɗinka ko Dad ɗinka suka san Abinda muke aikatawa?  Nikam inajin tsoron kada ƴan bikin da suka fara taruwa wani ya shigo part ɗinka yaga Hateem a kwance a samu matsala...!"

Gabaki ɗayansu tsareshi sukai da idanu suna jiran suji me ze ce.

Ɗaga kafaɗunsa Saleym yay cikin yanayi na rashin nuna Damuwa yace "ina ganin wannan ba abinda zaku ɗaga hankalin ku akai bane Sam, part ɗina yana da girman da babu wanda ze san akwai Hateem a ciki indai har ba gaya masa akayi ba, so ku kwantar da hankalin ku insha Allah baza'a samu wata matsala ba.

Na'am sukai da maganar Saleym ɗin sannan Abou Hateem ya buɗe murfin motar na back sit ya fito da Hateem ɗin wanda ke sanye cikik Uniform ɗin Ma'aikatar Babban Zaure, Kai tsaye part ɗin Saleym suka Nufa dashi Dr. Arfat na biye da Abou Hateem da jakar kayan aikin se kuma cikon na ukun su Wato Saleym.

Suna shig awani ɗaki na musman Salym ya buɗe musu wanda ke ɗauke da ƙaramin gado me ɗan banzan laushi aka kwantar dashi akai,, ƙura masa idanu Abou Hateem yayi zuciyar sa na bugawa da ƙarfi sosai yakejin kewar yaron na Ratsa duk wata gaɓa ta jini dake jiKn sa besan lokacin da wasu zafafan hawaye masu ɗumi suka fara zubo masa ba, nan da nan zuciyar sa ta fara gaya masa cewa "all abinda ya Faru da Hateem is all his fault. Da ace be barshi a wannan dajin ba da yanzu bai faɗa cikin wannan iftila'in ba.

Dafa kafaɗar sa Dr. Arfat yayi cikin siga ta rarrashi yace "ka kwantar da hankalinka Dr. M.Y be kamata kayi blaming kanka akan zanan da ƙaddara tazo maka dashi ba, Nasan DA CIWO A RAYUWAR KA amma idan kayi haquri ka danne zuciyar ka insha Allah everything is going to be alright OK?"

Share hawayen dake zubo masa yay da bayan hannun sa sannan ya ɗaga masa kai alamar gamsuwa da baya nan ƙarfin gwiwar da Dr.Arfat ɗin ya gama yi masa.

Jakar hannunsa Arfat ya buɗe cikin nutsuwa ya fara fito da kayan dake cikin babbar jakar yana ajiyewa a gefe harya gama tsaf amma bega abinda zasuyi amfani dashi ba wajen gwada mizanin yanayin cutar kansar dake jiki Hateem ɗin ba.

Cikeda tashin hankali Arfat yace "Akwai matsala Dr. M.Y !"

Cikin nutsuwa Abou Hateem ya sunkuya yana kallon kayan gabaɗaya da manyan idanunsa yace "matsalar me kuma Dr. Arfat?"

A taƙaice Arfat yace "mun rasa ma'aunin daya kamata musan irin nau'in cutar  kansar dake jikinsa, shin taya zamu iya yin abinda ya dace akan case ɗin?"

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now