FINAL CHAPTER

171 18 1
                                    

🧊🧊🧊 🧊🧊🧊
🧊🧊🧊
*MURADIN RAI*
*(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Banyi Editing ba 🙅‍♀️

Page: 23

_____Gabaɗayan su Zuba mata ido sukayi shiko Dr. Jardawa miƙewa tsaye yayi sabida ganin baƙuwar Fuskar dayay a wannan lokacin buɗe baki yay da nufin yaji ba'asi matar tayi saurin datakar dashi tace "ka adana tambayoyin ka idan munje inda ya dace sekayi."

Matar tai maganar tareda maida kallonta Ga Zainab tace "kiyi haƙuri tazarar dake tsakanin ki da mahaifiyar ki me matiƙar tsaho ce indai har akace a gaggauce za'ai komai."

Ta ƙare maganar tana ɗauke idanunta daga barin kallon Zainab ɗin sannan ta kuma Duban Dr. Jardawa a karo na biyu tace " ya yanayin Condition ɗinta yake ? Ina nufin shin zamu iya tafiya da ita ba tareda an samu Wata matsala ba?"

Ɗaga mata kai yayi donya tabbatar mata da maganar sa sannan yace"Ae to zamu Iya tafiya da ita ammafa semun kulla sosai sabida aikin da akai mata yanada Haɗari wanda idan har akayi Sake zata iya Rasa Rayuwar ta na gabaɗaya."

Da sauri mata tace "A'a gaskiya muddin zata iya samun Matsala a haƙura kawai zuwa wanin lokacin sa jaɗum idan Ubangiji ya ƙaddara hakan a tsakanin su, sam be kamata muyi wasa da Rayuwar ta ba."

Gabaɗaya ɗakin na'am sukai da shawarar ta Except Zainab wadda tunda suka Fara maganar take kuka tace

"ban damu da irin hatsarin dake zagaye dani ba muddin zan samu damar Ganin Mahaifiya ta koda So ɗaya ne kafin Raina Yabar jiki na! Ina so Rugumeta a ƙirjina sakamako kewar ta danai na tsahon shekaru 27, Na Rayu ba tareda kewar iyaye ba sabida duk wani gurbi ubangiji ya cikemin shi ta hanyar Bani waƴannan bayin Allan masu Zuciya irin ta Salihan bayi wadda babu mugunta a cikinta balle ƙyashi, sun kula dani kuma sun bani Tarbiya gwargwadon iyawarsu dukda cewar basu suka Haifeni ba. Seda dukda hakan ina neman alfarma a gareku don Alfarmar manzon Allah ku barni inga Mahaifiya ta koda So ɗaya ne pl......!!"

Kasa ƙarasawa tayi sabida yanda kukan daya taso mata ya hanat ƙarasa maganar

Gabaɗaƴa Jikinsu Mutuwa yay sabida tausayin ta amma kaf aka rasa wanda zece ƙala, Miƙewa Dr. Jardawa yayi Ya isa gare ta tareda zare mata za ran ƙarin ruwan dake jikinta, gabaki ɗaya ilahirin kanta a nannaɗe yake da farin bandeji sakamakon Aikin da akai mata na cire Harshashin bindigar dake ƙwaƙwalwar ta, sannan ya kama hannunta ya taimaka mata ta miƙe tsaye, fita Sukai daga ɗakin gabaɗayan su ba tareda sun bari wani ya gansu ba, har bakin motar sa suka isa hannunta na cikin nasa ya buɗe mata bayan motar ta shiga ta zauna.

Sannan su Malam da Baba Mairoji da wannan matar datazo ɗazu suka shiga baya suka zauna, sannan yaja motar suka fita daga Asobitin seda sukai tafiya me nisan gaske sannan ya faka a wani haɗaɗɗen Boutique dake kan titin Amadu Bello A cikin garin na Kaduna, kallonsu yayi yace "Baba duk ku sakko mu shiga."

Ba musu duk suka Sauka ciki kuwa harda Zainab ɗin.

Wata haɗaɗɗiyar Sinegalist shadda Ash colour wadda taji uban Stones ya siyawa Zainab sannan ya saiwa Baba Mairoji itama haɗaɗɗiyar Doguwar rigar Atampa irin ɗinkin da akeyi a Dubai ɗinan sannan ya saiwa shima Baba Maroon ɗin shadda ɗinkin babbar riga, iya su kaɗai seda ya kashe musu kusan 200k banda kuɗin takalma dana mayafai

Ɗakin da aka ware don canja kaya aka nuna musu kow aya shiga ya canza kayan jikinsa zuwa Sababbin, sosai kayan sukai masifar Musu kyau especially Zainab sosai kayan suka amshi jikinta tareda fito da ainihin kyan datake dashi, cikin dabaru ta murza ɗaurin ɗankwalin akanta tayanda bandejin baze fito ba

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 19, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now