MURADIN RAI CHAPTER 9 TO 10

106 11 2
                                    

🧊🧊🧊 🧊🧊🧊
🧊🧊🧊
*MURADIN RAI*
*(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITTEN BY: CHUBAƊO (the chosen one)_*
✍️

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page: 9 -10

____✍️Yaƙe ta farayi don harga Allah yawan securitys ɗin Dake gurin ya mugun bata tsoro Ba kaɗan ba, bugu da ƙari yanda taka suna gabatar da aikinsu babu wasa balle Ka kawo musu wargu a lamarinsu.

daƙyar ta iya gaiyato jarumtar datai mata saura ta kalleshi tareda miƙa masa katin shedarta na Asbitin datake aiki, ya jima yana kallon katin sannan ya miƙa mata yace, "maraba da zuwa." Ya faɗa tareda yiwa waƴanda ke jikin get ɗin alamar su buɗe mata ta shiga, danna hancin motar tayi zuwa cikin ma'akatar nan ma seda tai tafiya me nisan gaske Kamar zata bar gari sannan ta iso inda ake hada-hadar jama'a, inda aka tanada don Ajiye motoci ta nufa tai parking sannan ta fito ta nufi wata babbar ƙofa inda take da tabbacin nan ne inda manyan delers na gidauniyar suke, Nanma seda tayi tafiya sosai sannan ta fara gani mutane tsilla-tsilla sanye da uniform fari ƙal dashi, Babban abinda yaɓƙara ɗaure mata kai guda ɗaya ne tak tunda ta fara tafiya take cin karo da ababan zargi iri-iri, Ajiyar zuciya ta sauke tareda tsayawa cak ta ɗora hannunta na hagu a saitin zuciyarta don kawai ta samarwa da kanta nutsuwa

A hankali ta sauke hannunta daga ƙirjinta ta fara ƙoƙarin yin gaba Cikin yanayi na ƙarawa kai ƙwarin gwiwa, tafiya kawai takeyi har taci karoda wani Matashi shima sanyeda farin uniform same with na sauran Jama'ar data bari a baya Me ɗauke da Hatimin ma'aikatar daga saitin ƙirjinsa cikin hanzari tace Dashi " Excuse me pls" tsayawa yayi cak yana kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa batareda yayi magana ba Noor tayi saurin cewa, " pls I'm looking for Dr. Bashir bala's office And i......" Dakatar da ita yayi ba tareda yayi magana ba yay mata alamar tabiyo bayansa. Wani irin farin ciki taji yana ratsata musamman yanda taga muradinta na haɗuwa da wanda take nema yana gabda cika.

wasa-waa seda sukai tafiya me nisan gaske kafin suka iso office ɗin nasa wanda ya kasance ɗauke da wata arniyar ƙofar glass, shiru Noor tayi a lokacin da matashin daya rakota ya fara ƙwanƙwasa ƙofan tareda komawa gefe ya tsaya ƙam yana jiran a bashi umarni. Ita kuwa gogar taku tun a hanya takebin ko ina da kallo har sanda suka iso bakin ƙofar ofishin Dr. Bashir Ɗin, babban abinda yafi ɗaukar hankalinta shine wata hanya Data gani daga ɓangaren hagunta kafin a iso ofishin haka kawai setaji a ranta tanason tabi wannan hanyar wadda taga an zuba mata matakan tsaron da suka zarta na get ɗin farko kafin ka shigo ma'aikatar,

daga can gefan inda mutanen dake sanye da baƙaƙen kayan suke tsaye wata katafariyar ƙofar glass ce kana daga waje amma kana iya hango haɗaɗɗun gadajen dake cikin ɗakin masu Kamada zubin na yara ƙanana. Daga can ƙasan zuciyar noor tace "tabbas sena shiga naga abinda Waƴan nan ƙartin mutanan suke zaman gadi Ba dare Ba rana a nan." Ƙofar glass ɗin aka buɗe Dr. Bashir Bala ya fito cikin shigar fararen kaya sol dasu kansa kuma cikin wata hula wadda tafi kamada hulan kwano duk ta rufe ilahirin fuskarsa tayanda bazata iya shaida yanayin kamanninsa ba ya kalleta Da fara'a yace " kiyi haƙuri dear amma yanzu kam bazan samu isashshen lokacin dazan gana dake ba. "amma yallaɓoi abunefa na ujila Ya kamata ace ka zauna dani tayanda zaka samu zarafin jin abinda ya kawoni pl........ "kinga inada aikin dazanyi a gaba amma koma menene zaki iya zuwa office ɗin Dr. Arfat Feruz Ki tattauna dashi im sure ze miki duk abinda niɗin zan miki" ya Katseta ta hanyar faɗar hakan, kallon matashin daya rakota Yay yace " Ka kaita gurin Dr.Feruz" cikeda girmamawa matashin yace "ok sir. Bin bayansa tayi suka koma Zuciyarta a cunkushe sabida rashin bata damar dayayi Wani siririn Tsaki taja A lokacin da suka zagayawa can wani ɓangaren na daban Ita da matashin, itadai Noor suna tafiya tana bin ko inada kallo wni guri ne tun shigowarsu yaja hankalinta sosai.

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now