CHAPTER 13

99 9 0
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

*MASU MIN SHARING ƊIN WANNAN LITTAFIN  WAƳANDA NA SANI DA WAƳANDA MA BAN SANI BA UBANGIJI YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNA DON ALFARMAR MUHAMMADURRASULILLAHI🤲*

Banyi Editing ba

Page: 13

___Jan ƙafarta yay da wani irin mugun sauri itama ta faɗi cikin rashin sa'a santsi ya kwashesu suka gangara cikin wani tsohon Rami wanda ke cike da busassun ganyayyaki, wata wahalalliyar ƙara ya saki a lokacin da hannunsa ya daki wani babban dutse dake cikin Ramin

Hannunta ta ɗora a  saman soft pink lips ɗinsa alamar yay shiru  hakan yasa ya kafata da manyan idanunsa waƴanda ke fitar da wani irin maiƙo. Har bakin ramin sukazo suna dube-dube amma basuga kowa ba  don haka suka juya  da hanzari. Hasken farin watan dake maƙale a sararin samaniya ne ya bata damar ƙarewa fuskarsa kallo daƙyar ta iya buɗar bakinta tace " Mun rayu a mabanbantar gurare amma se gashi ƙaddara ta haɗani dakai, bazance nasan wani abou a game dakai ba amma inajinka a kusa da zuciyata  haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da sukace ɗan halak shi kaɗai ne kan saka khairan da khairan, A yau kam na gama gamsuwa dakai a matsayin gaskuwa a gareni.!"

Lumshe gajiyayyun idanunsa yay tareda kyauda kansa gefe yace " karki ɗauki abinda nai miki a matsayin wani gagarumin Abou balle har hakan ya wani ɗaɗaki da ƙasa, ko wani mutum abinda nai shizeyi don haka ki dena kallo na a matsayin wani mutum na musamman zanso ki kalleni kamar kowa."

Sauke idanunta ƙasa tai tana murza yatsun  hannunta ƙwallar dake maƙyale a tsakiyar ƙwayar idanunta ce ta zubo ba tareda ta damu da ta gogesu  ba ta ɗago tareda sauke rinannun idanunt a kansa dukda ba ita yake kallo ba tace "koda ace zan tilastawa kaina wajen yi maka kallo a mtsayin  mutum kamar kowa wllh yaudarar kaina kawai zanyi, sabida nasan kai ɗin ba kamar kowan kake ba dukda cewar ban ɗauki dogon zango a tareda kai ba."

Cizon lips ɗinsa na ƙasa yay sabida tsabar azabar da hannunsa ke mishi yace "Kada ki yaudari kanki Nooryen wajan ɗora kanki cewar niba mutum bane kamar kowa, zanso ki dingai min irin kalon da sauran mutane kemin na miskilin mutum ko kuma akasin hakan ke kanki kinsan i'm not friendly at all  inada matiƙar wahalar sha'ani."

Yay maganar yana yatsina fuska tareda Lumshe gajiyayyun idanunsa.

Jan hanci tayi wanda hakan yasa ƙwallar idanunta tsagaita zuba tace "shiyasa ai na kiraka da mutum na musamman, amma zanso kamin alfarma guda ɗaya idan har ban takura maka ba."

Batareda ya buɗe idanunsa ba yace "ina jinki."  yay maganar yana jin gina bayansa da dutsen dake bayansa

"shin zan iya sanin sunan ka da ainihin ko kai wanene?"

A  gajarce yace "sunana kike son sani kokuma tarihin Asali na?"

Abou Hateem ya faɗi hakan cikin yanayi na ƙosawa da Surutunta.

Ƙara sinkuyar da kanta tayi kamar bazatayi magana ba sannan ta ɗago da fararen  idanunta waƴanda suka sirka da launin ja tace "Sunanka kaɗai ma idan ka sanar dani ya wadatar base ka sanar dani abinda ke ƙunshe a cikin Rayuwarka ba."

Taɓe baki yay tareda kauda kansa gefe yace " You can call me with Abou Hateem."

Cikin hasken farin watan daya gauraye gurin tayi saurin ɗago idanunta a razane tace "Abou Hateem!" cikin yanayi na zallar kaɗuwa sam batai tsammani yanada mata ba balle ɗa.

Murmushi ya sakar mata a karo na biyu yace " yeah thats my Name."

Bata ƙara magana ba tai tsit sabida wani irin abu daya mugun tsaya mata a rai a gameda abinda kunnuwanta suka jiye mata, zama tai a dandiryan ƙasan kogon dukda zuciyata a cike take da zallar tsoron  bata san akan abinda zata zauna ba ɗin ba.

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now