MURADIN RAI chapter 5

139 8 0
                                    


   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*

*_WRITING BY: ZM~CHUBAƊO✍️_*



Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page:5

____✍️Ƴar ƙara ta saki sabida azabar da taji a ƙwaƙwalwarta sabida yanda hannunsa ke riƙe gam da gashin kanta kamar ze tsige mata shi, cikeda tsiwa gamida Masifa tace "dilla malam sakarmin gashi bakasan akwai zafi bane?"

Wani irin haushinta ne ya ƙara cika masa rai don haka  ya juyoda ita a fusace ta yanda ze samu zarafin ƙare mata kallo, kafeta yayi da ido kamar yanda itama ta kafeshi da nata idanun, ƙara damƙe Gashin kanta yayi Cikin hannunsa tayanda zataji a jikinta sitill yana kallonta da manyan idanunsa, cikin yanayi na tsare gida tareda  kakkausar murya yace "Suwaye ku and what your intentions to bring me here?" 

Ƙara ta kuma saki a karona biyu Sabida  yanda ya matse mata kai har wani azaban raɗaɗi  yake mata tace "nifa bansan Ko kai waye ba malam kawai tsintanka nayi a bakin ruwa a lokacin da muka fita outing  nida friends ɗina, bansan komai ba akanka Ba bayan  wannan  pls don Allah ka sake min gashina wllh akwai zafi."

Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske tareda Busar da wata zazzafar iska  daga bakinsa sannan ya sake kallonta a karo na biyu a rayuwarsa cikeda rashin yarda da maganganunta yace "ina Asalin kayan dake jikina suke? sannan kuma taya za'ai na yarda da abinda kika faɗa na cewar tsinta na kikayi?"

buɗa manyan idanunta tayi lokaci guda kuma ta wani galla masa harara tace "Albashin nawa ka biyani dazan maka ƙarya don kawai ka yarda dani?"    ta faɗi hakan tana wani hura hanci cikeda tsiwa.

ɗage girarsa yay inda wani ɓangare na zuciyarsa ya ƙara hasala da ita  don haka ya ƙara matsa gashin fiyeda yanda ya matse da farko yace "ke mara kunyar Yarinya zaki gayamin inda kayana suke kokuwa sena kafa miki tarihi a Rayuwarki?"

Da sauri ta nuna masa wata ƙaramar drower dake ɗan nesa da inda suke tace "yana cikin can." Tayi maganar cikeda nuna yanda takejin zafin riƙon dayayi ma gashin nata

Sakinta yayi tareda turata gefe ya nufi inda ta nuna masa tareda buɗe drower ɗin zuciyarsa na tsananta bugawa, zaro kayan yayi tareda fara lalubar duk aljihun dake jikin wandon dana rigar  amma Sam be samu nasarar gano abinda yake neman ba,  zubewa yayi a gurin tareda dafe duka kansa da hannayensa biyu sabida tsabar tashin hankalin dayake ciki

Kafeshi Noor tayi da lumsassun idanunta waƴanda suke ɗauke da sirrin kyau gamida tsari dukda irin zafin da gashin kanta keyi mata, so take ta gano wani abu a taredashi amma sam ta kasayin hakan haka kuma abu guda ɗayane keyi mata yawo a tsakiyar kanta shine"me wannan kyakkyawan  matashin yake nema haka?" tabbas tasan akwai wutar muradin dake Addabar wannan  saurayin ma'abocin kyau da kuma kwarjini.

A iya Rayuwarta zata iya cewa bata taɓa cin karoda mutumin dataji a ranta cewar daga kallon farko ta yabada kyansa da kuma tsarinsa ba se wannan!   Shin waneneshi? Kuma me yake nema da har ya gigita kansa irin haka akan sa?"     Bata gama dawowa daga duniyar tunanin data afka ba ya tattara kayansa da hannunsa wanda ciwon ke jiki ya nufi ƙofar fita da hanzari dukda cewar besan inda ze dosa ba.

Wani ƙaramin kati ne ya faɗo daga jikin wandon ba tareda ya lura ba, da sauri Noor ta isa ga katin cikin ɗaga murya tace "mr. arrogant ka yarda katinka."  Ta faɗi hakan tana kallon Abou Hateem dake ƙoƙarin fita daga ɗakin

Tsayawa yay cak Sabida jin irin  Sunan data kirashi dashi  kamar baze juyo ba sabida yanda ta mugun bashi haushi,  Juyowa yayi ba tareda ya kalli fuskarta ba ya isa gareta cikin hanzari ya karɓi kati tareda maida kallonsa ga wayar Dake hannunta, ba tareda ya kalleta ba ya fuxgi wayar ya koma kan gadon Asbitin ya zauna kamar wani zararre ya fara ƙoƙarin kunna data ɗin wayar,  duk abinda yake cikin sauri yake gudanar dashi  don haka nan da nan ya fara ƙoƙarin bin diddigin inda Hateem ɗinsa yake.  gabansa ne yay wani irin faɗuwa a lokacin dayay arba da inda bi diddigin wayar ya nuna, dube-dube ya farayi yana neman inda zega takadda da kuma biro donya samu ya zana  taswirar Gurin Da bi diddingin yake.

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now