CHAPTER 18

97 14 0
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY :ZAINAB MUHMD CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

Page: 18

____"Me kake nufi da zaman mu a nan ya ƙare Alhaji?"  dattijon yay maganar yana kafeshi da idanun cikin yanayi irin na wanda ke buƙatar ƙarin haske akan maganar.

Wani dogon Fasali Jardawa yaja sannan yace "hakan dana faɗa shi kaɗai ne mafita  a gareku Malam musamman idan akai duba da ƙurar daka iya tasowa akowani lokaci, shiyasa na zaɓi na sanar daku sabida bazan taɓa jurar wani mara daɗi ya sameku ba jikina yana bani cewar wani abu mummuna yana shirin faruwa muddin baku bar wannan jejin ba!."

kauda kai Dattijon yayi tareda janye idanunsa daga  barin kallonsa yace

"duk na fahimceka Alhaji sedai  har zuwa  wani lokaci zamu ɗauka muna aikin gujewa mutum guda ɗaya tak don kawai yanada ɗaurin gindi a dikance da gurin manyan ƴan siyasa?"

Murmushi dattijuwa Mairoji tayi wanda yafi kamada na zallar takaici da baƙin ciki tace "abinda na lura dashi a wannan rayuwar Malam talaka bashida wani Mutunci balle darajar da idan aka zalunceshi za'a ɗauki wani ƙwaƙwaran mataki akai musamman ma a Nigeria, shiyasa duk wani ta'addanci da rashin imani ake saukeshi akan masu ƙaramin ƙarfi babu wanda yake damuwa da Rayuwar talaka balle har Aji kokensu akan abinda suke fukanta, kullum lamaruran Rayuwar talaka ƙara tsanani yakeyi babu abinda ya damesu  har se zaɓe yazo tukunna a sannan ne talaka yake da amfani a gurinsu, sabida zasu amfana da ƙuri'un su don tabbatuwar MURADAN SU."

hawayen daya zubo mata tasa hannu ta share sannan taci gaba da cewa

"duk wani tsanani da tsadar Rayuwa Talaka ne kawai yake fuskantar su balle uwa uba harkar ilimi da kullum ƙara tsadanta ta  akeyi,  dayawa ƴaƴan Talakawa suna buƙatar su zurfafa Iliminsu amma dayawansu iya Sakandire suke tsayawa sabida rashin abinda zasuyi riƙo dashi wanda ze cicciɓasu zuwaga tabbatuwar muradansu dana iyayensu,  shiyasa kullum ƙara abubuwan rayuwa suke ƙara taɓarɓare mana."

Murmushi Dattijon yayi tareda kai hannunsa ya share ƙwallar dake ƙoƙarin zubo masa yace "Mairoji duk wata al'umar da kikaga suna cikin matsin Rayuwa wllh Rashin kiyaye dokokin Allah ne ya janyo musu hakan, idan kikai duba da Halin da al'umar mu take ciki a yanzu Rayuwa ce akeyinta tamkar ta dabbobi babu maganar tsari a cikinta balle a samu daidaito, duk abinda Ubangiji yay mana haramci akai dayawa mutanan mu shi suke Aikatawa a wannan lokacin da muke ciki Ran ɗan Adam ba abakin komai yake ba,  wannan kaɗai ya isa yasa Ubangiji ya jarabce mu da ƙuncin Rayuwa."

Tsagaitawa yayi da jawabinsa tareda gyara zamansa ya ɗauki murfin kwanon ya Rufe damammiyar furar da Mairoji ta ajiye masa a gabansa tun dawowarsa  sannan yaci gaba da cewa,

" A kwai tarin abubuwa wanda idan har al'umar mu basu sauya daga yanda suke ba wllh yanzu Suka fara kuka,  har yanzu ban yanke ƙauna ba na sani Ubangiji yana tareda duk wasu bayinsa masu kyakkyawar zuciya, banida ƙarfin dazan kare kaina daga dukkan abinda ƙaddarata data iyalaina tazo mana dashi  don haka na barwa Allah komai."


Sosai  maganganun Malam  sukai tasiri a jikin Alhaji Abubakar jardawa  sabida kaf abinda ya  faɗa gaskiya ne  da ace shugabannin mu zasu dinga duba ga rayuwar talakawa tabbas da ba'a samu taɓarɓarewar wasu Abubuwan ba  a cikin ƙasar mu.  Tsugunawa yayi dabda inda diga-digan Malam ɗin suke sannan yace

" Haƙiƙa kai mutum ne na musamman wanda ban taɓa cin karo da kamar ka ba, sedai dukda hakan ina matiƙar jin tsoron kar wani Abu mummuna ya Faru dakai a Sanadina wllh ina matiƙar jin tsor......."      

Kukan dayake dannewa ne yay nasarar kufce masa irin wanda ya daɗe beyi kamar sa ba.

Dafa kafaɗunsa malam yayi tareda sakin murmushi yace

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now